Sashe 116
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hashir da Hadid su ka wani tafa suna dariya tareda juya keken su suka shige gidan.
Ƙwaƙwƙwaran numfashi mai kyau ta kasa yi. Yau da ace wani ne ya gaya ma ta abinda 'yan biyu su ka ce da ba za ta taɓa yarda ba amma sai gashi da kunnen ta ta ji komai. Wato da ƙarfi da yaji dai Justice ne Daddyn su.
Ya lura da yadda ta kaɗu da jin maganar yaran dan haka ya kauda hankalinta ta hanyar cewa "shekaru bakwai da su ka wuce na haɗu da wata yarinya mai karambani a wajen wani biki. Yarinyar da ƙarfi ta ke son shiga wajen da ake dinner bayan kuma ba ta da card ɗin shiga. Ta maƙalewa wani mutumi da ta kira Uncle Muhammad su ka barta ta shiga.
"Da ikon Allah wannan Uncle Muhammad ɗin ya sake ganinta a cikin jirgi bayan watanni kaɗan. Ba tareda ta ganeshi ba ta ma sa tayin plantain chips da ta ke ci. Da jirgi zai tashi ta fara karanto addu'o'i kala-kala har ta riƙe hannun sa ba tareda ta sani ba..."
"Ya Allah! Daddyn Raziya kai ne dama?"
Murmushi yai ya ce "na ƙara tsufa sosai ko?"
"Oh my goodness, shiyasa ranan da mu ka je gidan ka na ke tunanin kaman na taɓa sanin ka a wani waje, ashe kai ne"
Ta dafa kan ta tana É—an girgizawa cike da tunanin wannan coincidence É—in.
" Kalmar Allah ya isa tana da nauyi Zaytoon. Idan har zaman da za mu yi tana ƙarƙashin wannan kalmar ne, zan iya haƙura da zaman ko da kuwa abu ne da zai min ciwo"
Ya kwantar da kan sa jikin kujera yana kallon sama kaman mai tuno wani abu.
"Immediately da na gama Law School ina da dogon buri a rai na. Kwata-kwata ba ni da niyyar yin aiki ƙarƙashin gwamnati. Case na farko da na karɓa na wani Baffana na ne ƙanin Mai Martaba. Wani babban fili ne ake jayayya a kai. I was young, buri na kawai shine na ci first case ɗina ta ko wani hali. Aka shiga ƙara kotu mu ka fafata da lawyan gwamnati da ke kare Tsoho mai filin da kuma ni da na ke kare Baffana. In the end aka ba wa Baffana gaskiya aka ƙwace fili daga hannun Baba Sama'ila.
"Bayan mun fito daga kotu ina murna na ci case ɗin sai na ji an taɓani ta baya, juyawan da zan yi sai na ga wannan tsohon ne da akayi shari'ar da shi. Akwai tsantsan ɓacin rai da damuwa tattare da fiskar sa, ya ce min ("Na san kun fi ƙarfina, amma zan bar ku da Sarkin da baya zalunci. Allah ya isa fili na").
"Zaytoon ban iya bacci ba ranan ba. Kalmar Allah ya isan nan ya tsaya min a zuciya, ya hanani sukuni. Washegari na tafi Æ™auyen Tsohon nan only to find out ana zaman makokin sa. Ashe bayan ya koma gida da ya shiga ya kwanta bai sake tashi ba. Æacin rai ya zama ajalin sa. Hankalina ya tashi matuÆ™a, i blamed myself for his death. Na koma na waiwayi case É—in nan, na bi proper ways na yi bincike na gane cewa Baba Sama'ila bai sayarda filinsa wa Baffana ba. Yes Baffana ya ma sa tayin sayar da filin amma ya Æ™i, shine aka yi fake documents da kuma sa hannun Æ™arya aciki. Wasu marasa imani cikin Æ™auyen su ka ba da shaidar zur akan cewa lallai Baba Sama'ila ya saida filin sa. Bayan na gama haÉ—a komai i met my uncle akan ya maidawa 'ya'yan Baba filin su ko kuma dai na sake buÉ—e sabon Æ™ara akan sa. Abu dai ta kai mu har gaban Mai Martaba still bai yarda ba. Ni na jagoranci yaran Baba Sama'ila aka É—aukaka Æ™aran nan har ta kai an Æ™wace fili daga hannun Baffana an maidashi wajen Magadan Baba Sama'ila.
"Dalilin wannan har yau ba ma shiri da Baffa na. Saboda wannan shari'ar ya sa na fasa zama lawyer mai zaman kan sa na koma ɓangaren gwamnati na fara aiki har na kawo matsayin da na ke yanzu.
"Zaytoon, har kafin a bawa 'ya'yan Baba filin nan, ban taɓa yin bacci na kwanciyar hankali ba. Duk lokacin da na kwanta kalmar Allah ya isa da Baba yai shi ke hanani bacci..."
Kukan da ya ci ƙarfin sa ne ya hanashi ci gaba da maganar. Itama Zaytoonah hawaye fall ne a idonta.
Justice ya fito da handkerchief ya fara goge hawayen da ke fita a idon sa, sai dai yana gogewa wasu na fitowa.
"Daddyn Raziya ka yi haƙuri" Zaytoonah ta faɗa tana ɗaura hannunta akan cinyar sa.
Kusan minti biyu kafin ya iya tsaida kukan na sa ya juyo yana kallon Zaytoonah ya ce
"Ina son ki Zaytoon, amma ba zan iya zaman Allah ya isa da ke ba. Zan ba ki kwana uku ki yi tunani, in har kin yadda ni mugu ne marar adalci, wanda ba za ki iya zama da shi ba. Zan sawwaƙa mi ki. Da na zauna da ke ina zaluntar ki gara na danne zuciyata na rabu da ke na miki fatan alkhairi a rayuwar ki"
Jikinta ne yai sanyi, ta ma rasa mi za ta faÉ—a ma sa a wannan lokaci.
Ya sa hannu a baya ya jawo wata leda ya É—aura a cinyarta ya ce " ga tsarabar 'ya'yana. Ki gaishe min da su"...
***
Maganganun Justice ta ke ta juyawa a ranta wanda ya hanata bacci. Idan har za ta kira Justice mugu to ita ce babbar muguwar. Bayan matsalar Ghazala mi ya ma ta da har za ta kira shi da mugu. Ghazala ce fa Munafuka.
Ƙarfe tara na dare sai ga kiran Hajia Abu a wayarta. Ta tashi zaune ta ɗauka wayan tareda sallama.
"Ke wacce irin daƙiƙiyar yarinya ce, Iye?. Idan ma kin yi yaji ne dan kina tunanin Galadima zai zo ya yo bikon ki to kin yi kaɗan. Idan za ki tattara ki koma gida ki koma, idan kuma takardar ki kike buƙata sai ki yi magana a kawo miki har gida. Ba dan ma ƙaddara ba mi zai haɗa auren ki da Galadima"
Sarai ta san Ghazala ce da wannan aikin, wato har ta beza cewa ta yi yaji daga kwana uku da ta bar gidan.
"Hajiya waya ce Yaji na yi?. Mommy na ne fa ba ta da lafiya shine na zo duba ta"
Hajiya Abu ta ji gwiwarta ya sace, dama barazana ce kawai. Ko kaɗan ba ta son abinda zai ɓatawa Galadima record domin tanada ɓoyayyen buri akan sa na son ya gaji Mai Martaba idan rai ya halin sa.
"Ghazala ta ce da dukkan akwatunan ki kika tafi, ana zuwa gaisuwa da duka kaya ne?"
"Lah! Kayan da ke Abujan ne naga sun kwana biyu shine na dawo da su nan saboda zan É—auko wasu a nan É—in na tafi da su chan"
"To Allah ya ba ta lafiya"
Ba ta jira Zaytoonah ta ce Amin ba ma ta kashe wayar.
"Mommy ki ji wai har Ghazala ta fara yaÉ—awa wai na yi yaji"
Mommy da ke duba assignment É—in yara ta ce "to ba yajin ki ka yi ba?"
"To shine harta fara bezawa a gari"
"Mi za ta jira kuma tunda gidan mai gaba É—aya za ki bar ma ta"
"Allah ya sawwaƙa na bar ma ta gidan"
Sai da ta yi maganar kuma sai ta riƙe baki tana jin kunya. Mommy ta yi murmushi ta cigaba da abinda ta ke yi.
2/11/21, 10:04 PM - ****: 58
Bismillahir Rahmanir Rahim
*I'm back*
Washe gari Zaytoonah ta je salon aka wanke ma ta kai aka ma ta ƙananun ƙitso, aka ma ta gyaran farce kafin aka ma ta jan Lalle. Ba ta dawo gidan ba ma sai bayan Azahar.
Ta kira Baaba Nafy ta ce ma ta Justice yana nan bai tafi ba sai washegari zai tafi saboda ya je representing Mai Martaba zuwa ta'aziyya wani ƙauye.
Ƙarfe shida saura ta isa gidan Justice. Sai da su ka gaisa da Baaba Nafy kafin ta wuce ɗakin ta bayan ta ƙarfi kwandon abinci da ta zo da shi. Tunda ta cewa Baaba Nafy za ta zo ta sa aka gyara ma ta ɗakin ta dan haka bayan ta ajiye jakarta ɗakin Justice ta wuce, falon sa na nan tsaf-tsaf sai ƙanshi ya ke. Ɗakin ma a tsaftacce ya ke duk da ma Justice baya bari ma su aiki su shiga ma sa ɗaki shi ya ke gyara kayan sa. Ko a chan Abuja ma shi ya ke gyarawa ko ya saka Raziya, yanzu kuma da ya ke da Mata har biyu kowacce ranan kwananta sai shiga ta gyara ma sa.
Da ta gama É—an gyara abinda ba za a rasa ba komawa É—akinta ta yi ta É—auko sabon bedsheet ta zo ta shimfiÉ—a ma sa. Sabon rayuwa sabon bedsheet.
Da ta ga komai ya ma ta yadda ta ke so sai ta koma na ta É—akin. Alwala ta yi ta zo ta zauna a sallaya tana azkar kafin a kira sallar Magariba.
Gaba ɗaya a gajiye ya dawo. Ƙauyen da su ka je hanyar kwata-kwata babu kyau, sun ji jiki a tafiyar da su ka yi.
Da ke sai da ya tsaya yai sallar Isha ma kafin ya shigo gidan saboda da ya ci abinci kwantawa zai yi ya huta gajiya tunda gobe ma sabon hanya zai É—auka.
Bayan yayi wanka ya fito ya saka silk pyjamas ɗin sa baƙaƙe sannan ya fito falon ƙasa inda aka jera ma sa abinci.
Da ke ya ga dare ya yi bai yi niyyar cin abincin sosai ba. Tea da aka haɗa ya fara zubawa kafin ya buɗe warmers ɗin ya fara serving kan sa abinci. Lomar farko da ya ci ya tabbatar ba girkin Baaba Nafy ba ne, kamar dai girkin Zaytoonah amma kuma ta ina Zaytoonah za ta ma sa girki bayan tana chan gidan su. Har ya ɗaga waya zai kira Baaba Nafy ya tambayi wa yai girkin yau sai kuma ya fasa ya cigaba da cin abincin, ya sawa ransa ƙila kewanta da ya ke yi ya sa shi jin abincin kamar irin girkinta.