Sashe 119
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da ta idar da sallan Asuba bacci ya cika ma ta ido, harta fara ma baccin akan sallaya subconcious mind ɗin ta ya tasheta "Zaytoonah kuna da baƙi yau fa"
Ya tunatar da ita.
Sai da ta yi wanka da ruwa mai zafi sannan ta shirya ta fito. Tsabar kiÉ—imewa ko É—akin Justice ba ta shiga ta gyara ba kawai ta wuce kitchen ta shiga haÉ—a mu su breakfast a gurguje.
Bayan ta gama ta haura sama. Tana shiga falon ta ga Ghazala na zaune kusa da Justice suna magana.
Yau dai ranan girkinta ne ba dai a wajen sa ta kwana ba. Abinda zuciyarta ya fara riya ma ta kenan. Kaman ta juya ta tafi sai kuma ta ga idan ta yi hakan ma ya nuna ta damu da su ne.
Ko gaishe shi ba ta yi ba ta wuce É—akin sa. Abu da zuciya, tana kallon gadon sa ya É—an yamutse kaÉ—an ta ji wani zafi a ranta.
Har ta fito Ghazala na wajen wannan karon kam abu ta ke nuna ma sa a waya. Zaytoonah ta yi wucewarta tareda banko mu su ƙofa da ƙarfi.
Maganar wani fili da Ghazalar ta siya da ya ke son jawo rikici ne ya kawota wajen Justice da sassafiya haka bayan ya dawo daga masallaci, domin ya ba ta shawara a matsayin sa na wanda ya san harkan shari'ar ƙasar. Sun riga sun gama maganar amma dan ta ƙula Zaytoonah sai ba ta fita ba ta cigaba da ƙaƙalo taɗi har sai da Zaytoonah ta gama abinda za ta yi ta zo ta fita.
Cikin ranta tana faÉ—in wawuyar Yarinya...
Yana karyawa aka kirashi akan Sakataren sa yayi hatsari. Wannan ya sa ya katse cin abincin ya je ya chanja kaya ya fita dubiya duk da ma ance ma sa bai ji ciwo sosai ba.
Ta yi miyar egusi, ta yi farfesun kayan ciki, stew ma tun jiya ta yi shi. Ta tuƙa semo ta saka a leda ta jefasu a food warmer.
Ya saura farar shinkafa da coselaw da kuma samosa da za ta soya.
Tana cikin saka fillings tana wrapping Samosa wayarta ya shiga ringing. Ta duba sai ta ga Muhsinah. Ta amsa kiran tareda saka wayar a speaker.
"Zaytoonah dan Allah ki zo" Muhsinah ta faÉ—a da raunatacciyar murya.
"Wannan nishin kamar mai labour. Ni dai na san ko wata shida bai cika ba balle ki ce bakwaini za ki haifa"
"Ki zo ki kaini Asibiti zan mutu, i'm bleeding"
"Ina Azma?"
"Ta tafi makaranta, ba kowa kusa ki zo dan Allah" ta faÉ—a tareda fashewa da kuka.
"Ganinan zuwa, amma kafin nan ki kira ko Baba maigadi ne"
Tana kashe kiran ta bar kitchen ɗin da sauri. Ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba. Banɗaki ta shiga ta wanke hannunta ta fito ta ɗau hijab ɗin da ta yi sallah da shi tareda handbag ɗin ta.
Ghazala ta gani a falo tana magana da Atika da ke durkushe a gaban ta kamar wata Baiwa. Da alama aikanta za ta yi dan ta ga kuÉ—i a hannun Ghazalar.
"Atika zan fita dan Allah idan ban dawo da wuri ba ki soyamin Samosa da na fara haɗawa, sannan ki dafa white rice kamar ciman mutane takwas haka. Akwai baƙin da za su zo."
"To" ta faÉ—a tana tsume fiska.
Zaytoonah ta fita da sauri. Dreba ta samu ta ce ya zo ya kaita wani waje...
Da gudu ta faɗa gidan lokacin da Dreba ya sauketa. A ɗaki ta samu Muhsina zaune daram a ƙasa ta jingina jikinta ya malale da jini. Tsabar ta yi weak ko iya tashi ta kasa yi.
"Innalillahi Mi ya faru?"
"Namiji! Namiji!" Abinda ta iya faÉ—a kenan sai hawaye.
Da taimakon Baba Maigadi ta taimakawa Muhsina ta shigar da ita mota bayan ta É—aura ma ta wani zani tareda tallafa ma ta da saka towel dan kar jinin ya cigaba da tsiyaya.
Da motar Muhsinan su ka je Asibiti dan Dreban da ya kawota ya riga ya koma.
Lokacin da aka shiga da ita numbar Uncle Aliyu ta fara nema dan har yanzu yana chan America bai dawo ba.
Tana gaya ma sa abinda ya faru shima hankalin sa ya tashi tareda cewa zai kira wani cousin É—in sa da ke Abuja ya zo kafin a zo daga Zaria. Ya ce da zaran Doctor ya fito ta kira shi ta haÉ—ata da shi.
Text ta turawa Justice dan ta kira numbarsa bai shiga ba.
Lokacin da Likitan ya fito ya ce an tsaida jinin sannan anyi scanning abin cikinta ba ya da rai dole sai an cire an mata wankin ciki.
Gaba É—aya Zaytoonah ta rikice sai kuka...
***
Daga Asibiti Justice na shirin komawa gida Baƙin sa su ka kirashi akan sun shigo Abuja dan haka ya ce Dreban sa ya wuce su taro su dan ba su san gidan sa ba.
With full confidence Ya shigo gidan dan mutanen da yai aiki da su lokacin yana Sokoto kuma anyi zaman mutunci. Cikin su mutum biyu ne su ka samu zuwa bikin sa da Zaytoonah to gashi bikin sa da Ghazala ma da ba ayi hidima ba basu samu sun zo ba shine su ka kawo ma sa wannan Ziyara bayan sun halarci auren 'yar Abokin su a Kano.
Bayan an zauna aka shiga hira. Atika ce ta kawo mu su ruwa da lemu ta ajiye mu su. Ganin ba a ƙara kawowa komai ba ya sa shi miƙewa yana faɗin bari ya kirawo matan na sa.
ÆŠakin Zaytoonah ya fara shiga amma ba ta nan dan haka ya wuce É—akin Ghazala wacce ke hakimce akan gado tana latsa waya tana jiran dramar da za ayi yau.
"Akwai baƙi da na ce za su zo sun iso ki fito a gaisa. A kuma taho da abinda za a fara taɓawa kafin idan mun dawo daga sallah sai a ci abinci"
"Abin taɓawa?, anya Zaytoonah ta tanadi wani abu kuwa" ta faɗa in a concern tune.
"Mi hakan ke nufi"
"Abu Razz ni dai ban ga alama Zaytoonah ta yi wani abu ba. Kamar dai ta yi jar miya jiya dan na gani a fridge amma ban ce an ƙara da wani abu ba dan tun da ka fita itama ta fita har yanzu kuma ba ta dawo ba"
Rintse ido yai yana tunanin minene matsalar Zaytoonah.
"Tunda baƙi sun iso kam dole a nemi yadda za ayi dama Atika tana kan haɗa Samosa barin je in sameta mu san mi za a iya yi cikin sauri"
Bai amsa ma ta ba kawai ya fice daga É—akin.
Tai ƙaramar dariya tareda miƙewa da sauri. Ta saka hijabi ta fito.
Bayan sun gaisa da baƙin ta wuce kitchen inda tuni Atika ta fara soya samosar da Zaytoonah ta haɗa.
Bayan minti goma aka kawo mu su lime cake da Samosa da kuma drinks sai soyayyen nama cikin wanda Zaytoonah ta soya jiya.
Justice dai ci kawai yai amma ran sa a jagule ya ke, ya dai dake dan kar su gane akwai matsala. Dole sai ƙarya ya mu su akan Uwargida ta tafi gidan rasuwa.
Lokacin da su ka tafi sallar Azahar sai da su ka tsaya a bakin masallaci yana jan su da hira duk dan ya ja lokaci har a gama abinci. Yana ganin text É—in Ghazala ya É—an ji sanyi a ran sa.
Kusan dukkan su farfesu da kuma tuwon semo da miyar agushi su ka fi ci. Mutum biyu a cikin su ne su ka ƙara da shinkafa. Sun yaba girkin sosai tareda addu'ar Allah ya ba da zaman lafiya.
Ba su suka bar gidan ba sai kusan ƙarfe biyar na yamma. Bayan sun yiwa Amarya da Uwargida kyautan kuɗi ta hanyar bawa Ghazala envelope guda biyu akan ita da Uwargidan ta.
Justice ya so su kwana a Abuja akan gobe sai su wuce amma sun ce ba Sokoto za su wuce ba a Katsina za su kwana.
***
Lokacin da Muhsina ta farfaɗo bayan aiki da aka mata ba abinda ta ke sai hawaye. Zaytoonah, Azma da matar Uncle ɗin su da ta zo ma ta sun yi tambayar duniyar nan ta ƙi gaya mu su mi ke damunta. Su Azma sun fi tunanin saboda mutuwar abin cikinta ne amma Zaytoonah ta san its beyond that.
Bayan Maghrib Azma ta je É—ebo kaya dan ita za ta kwana a Asibitin tareda Hajiya Firdausi.
"Muhsina kina tsoratar da ni minene dan Allah?, mi Abban Habib ya miki"
"AbdulHamid ya zalunceni Zaytoonah. Ya ci amana ta"
"Miya faru?" Zaytoonah ta faÉ—a cike da damuwa.
"Akwai yarinyar da na ga AbdulHamid ya saka hoton su a status na sa da daɗewa ya ce min wai 'yar ajin su ce tare su ke Phd da ita kuma wai itama 'yar Nigeria ce. Yarinyar Tiv ce amma a Lagos su ke da zama. Ni dai tun lokacin hankalina bai kwanta ba. Wancan zuwan da yai ma dai na ga suna waya and i sense that something is fishy. Na dai ɗauki numbarta a fakaice bai sani ba. Har zan kirata sai na share na ce ba kyau bincike da bin ƙwaƙwaƙwafi"
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
"Last week sai na kirata and sai ta tabbatar min wai son AbudlHamid ta ke kuma za ta aure shi. Mun yi musayar magana da ita har ta ke ce min wai ni lusara ce, kuma irin ni'imar da ya ke kwasa a wajen ta baya samu a wajena. Zaytoonah it hurts.
"Na dai bar maganar a zuciyata dan na san sharrin Mata. Yau da safe ta turomin video clip ɗin ta da AbdulHamid suna suna..." ta kasa ƙarisawa sai kuka
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun"
"Shock ɗin ne ya sa na ji cikina ya murɗa and the next thing sai jini ya fara zubowa. Na gama da AbdulHamid har abada Zaytoonah, ko shine Autan Maza na haƙura da shi"
Zaytoonah kuka kawai ta fara dan ba ta san ma mi za ta cewa Muhsinar ba.
Shigowar Hajiya Firdausi É—akin ya sa dukkan su su ka haÉ—iye kukan na su...