← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 161

Sashe 49

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakin ka ne mu fahimci junan ai. Look, kar ka ƙara aikowa a kirani dan zan watsa ma ka ruwan zafi" Ta shige gida ta barshi a tsaye.
Wonders shall never end. Wai Uncle Muntari ne zai turo ma ta saurayi.

Haka dai ta yi sati biyu ta dawo gida har lokacin kuma Bello kamar yadda ta gane sunan shi daga baya bai sake zuwa ba. Matan gidan su kuwa duk wacce ta ma ta maganar aure tsayawa ta ke ta silleta son ran ta.

Da ta koma gida ne cikin taɗi ta yiwa Mommy maganar abinda ya faru. Nan da nan Maryam ta ankara da abinda Muntari ke shirin yi. Wato nufinsa auren dole zai yiwa Zaytoonah. To kuwa tana dai-dai da shi dan abinda ba za ta taɓa bari ya faru ba ne. Amma dai bari ya zo ya sameta da maganar za ta nuna ma sa cewa ita ta haifi Zaytoonah ba shi ba.

Kyautar sabuwar waya andriod Maryam ta siyawa Zaytoonah lokacin da result É—in ta na WAEC ya fito mai kyau. Tana da A biyu da B guda biyar sai C uku.
Tuni ta saka numbar ƙawayenta wanda su ke da waya aka hau network...

Ranan ta dawo daga Islamiyya ta samu Muntari da Mommynta a falo suna masifa. Ta jima da sanin rashin jituwar da ke tsakanin Uncle Muntari da Mommyn na ta, duk da ma ba ta san takamaimai miya jawo hakan ba.

Ko gaishe su ba ta yi ba ta wuce ciki amma ta kasa kunne daga jikin ƙofa tana jin mi ake faɗi.

"Ka san Allah, ko sama da ƙasa za su haɗu ba ka isa ka aurar min da 'ya ba. 'Ya ta karatu za ta yi, ban roƙe ka kuɗi ba balle ka ce za ka takura da hidimar ta. Idan hauka ka ke yi ka je ka nemi magani amma ba ka isa ba Muntari, ka yi kaɗan"

"Maryam kenan, Zaytoonah dai sunan Tijjani Abubakar ta ke amsawa ba na Maryam ba. Dan haka a matsayina na shaƙiƙin Tijjani na yiwa 'yar sa miji. Ki gama borin ki nan da wata biyu za ayi biki"

"Idan mafarki ka ke yi ka farka Muntari domin indai nina haifi Zaytoonah ba ka isa ka ma ta auren dole ba ina dai-dai da kai"

Yai Murmushin mugunta ya ce "to mu zuba mu gani"

Bayan tafiyar Muntari Zaytoonah ta fito da gudu ta faÉ—a jikin Mommy tana kuka. "Mommy do something dan wallahi idan aka min auren dole kashe mijin zan yi ko kuma na kashe kai na"

Maryam ta ce " ba zai kai ga haka ba ma Insha Allah"

Bayan kwana biyu Maryam ta kira Goggo ta sanar da ita abinda Muntari ya ce. Goggo ta ce idan ta samu lokaci ta taho Ringim ayi maganar.

Abunda Maryam ba ta sani ba shine. Tun zuwan Zaytoonah hutu Muntari ya fara mission É—in sa ta hanyar hura wutar fitina cikin familyn su. Dalilan da ya gabatar na son aurar da Zaytoonah mafiya yawa cikin family sun gamsu da shi. Goggo da ta ji batun da ake a cikin gida sai ta samu Iya da maganar lokacin ba ta koma Zaria ba. Iya ta ce Muntari Uba ya ke ga Zaytoonah ba zai cutar da ita ba. Da ta ga abin yana son zama gori sai ta yi shiru ta bar zancen.

Muntari cewa yai Zaytoonah ta yi girma dayawa sannan tana da rashin kunya da reni. Ga uwa uba shiriritar 'yan fari da ke damunta.
Kusan kaf matan cikin gida sun yi gulmar Zaytoonah lokacin da ta koma Zaria hakan ya sa mazajen su da su ka ji dalilin aurar da Zaytoonah da Muntari ke yi ya sa su ka fara yaba ma sa acewar sa yana ƙoƙarin tseratar da mutuncin Zaytoonah ne kafin ta lalace ace saboda Ubanta baya nan ne aka kasa yi ma ta tarbiyya mai kyau.
Ba kaɗai dalilin ba ne ya sa su ka amince, Muntari ya jima yana yiwa 'yan uwansa Alkhairi na kuɗi da kayan abinci. Wanda ya ke ganin za su kawo ma sa cikas akan manufar sa tuni ya yi mu su abinda ba za su taɓa yi ma sa gargadama ba. Ya biya mu su kujeran Makkah.
Abu dai ya koma ba don Allah su ka amince da Muntari ba sai dan 'yan chanji da ya É—auki watanni yana ba su...

Da Maryam ta je Ringim ta samu Goggo su ka tattauna abinda ke faruwa. Maryam ta yi mamakin goyon baya da 'yan uwan T J su ka ba wa Muntari a wannan hukunci na son zuciya da ya ke shirin yi. Dan kaf sun yadda da auren Zaytoonah da Bello wanda yaron shekaransa ashirin da ɗaya, sakandare kaɗai yai ya kama aikin makanike, a ƙarƙashin wani ya ke ba wai yana da garejin sa ba ne.

Har wajen Baffah Umar ta je akan ta ganar da shi kuskuren wannan haÉ—in da Muntari ke yi. Amma sai ya ce ma ta indai saboda karatun Zaytoonah ta ke tsoro shi Muntarin yayi alkawarin zai biyawa Zaytoonah ta cigaba da makaranta bayan aure. Hadda cewa ai karatun 'ya mace a gidan mijinta ya fi kwanciyar hankali.
Ba ta samu abinda ta yi niyya ba dan haka ta chanja maganar ta hanyar roƙon a bari Zaytoonah ta auri Auwal instead of Bello. Shi Auwal ya ma fi kusanci da Zaytoonan kuma tare su ka taso sun saba da juna. Baffa Umar ya ce to magana ce mai kyau amma bari yai shawara da sauran 'yan uwa tukunna.

Kamar wanda Muntari ya mu su magani haka su ka haɗu su ka ƙi karɓan wannan shawara. Su ka ce anriga anyi nisa da zancen Bello kuma ba daɗi azo a ce an fasa hakan zai jawo matsala tunda da Bellon da Auwal ɗin 'yan uwan juna ne.

Maryam na komawa Zaria ta tattara kayan Zaytoonah ta É—auketa su ka fita, ita kan ta Zaytoonah ba ta san inda za su je ba kawai binta ta ke yi. Yadda ta dawo babu walwala a fiskarta ya sa Zaytoonah ta sha jinin jikinta.

Bauchi su ka je inda Maryam ta damƙawa Pendo amanar Zaytoonah zuwa lokacin da za ta buƙace ta. Ta kuma ja ma ta kunne akan kar ta yarda ta faɗawa kowa kan cewa Zaytoonah na wajen ta. Mijin Pendo lecturer ne a Jami'ar ATBU shiyasa tuntuni su ka bar Dutse da zama su ka dawo Bauchi. Itama Pendo ɗin ta cigaba da karatu dan ta kusa kammala degree ɗin ta a jami'ar. Ga sana'ar gyaran jiki da ƙunshi da ta ke yi ya karɓeta sosai, yanzu Pendo wacce 'ya'yanta ke kira da Ummi Hajiya ce.

A ranan da ta dawo Muntari ya kira Maryam a waya, tana É—auka sai ya kwashe da dariya ya ce "kin É—auka ban san shige da fice É—in ki ba ne? To ki ce Pendo ta yiwa Amarya Zaytoonah gyaran jiki da kyau dan aure ba fashi"

"Muntari stalking É—ina ka ke yi?. For Allah's sake ka fita a harkata dan wallahi akan maganar Zaytoonah har kotu za mu shiga da kai kuma ba zan daddara ba sai na ci galaba a kan ka"

*"idan kina so ki cececi 'yar ki daga auren nan, abu biyu za ki yi. Ki je a raba auren ki da Tijjani sannan ki aureni, ni kuma na miki alkawarin ko professor Zaytoonah ke son zama kafin ta yi aure to sai ta zama, babu mai ma ta auren dole. Kuma duk ƙasar da ta ke son zuwa karatu sai na kai ta"*

Tana jin abinda ya faÉ—a ta kashe wayan tana huci. Ba za ta yarda ba, ba zai ma yiwu ba.

Wasa-wasa sai ga shi a date É—in da aka sa har ya saura wata É—aya. Muntari har da turo ma ta text wai ya siyawa Zaytoonah kayan É—aki ta zo ta gani idan akwai abinda babu ta faÉ—a. Ta yi tsaki ta tura ma sa "keep on dreaming"

Tunda su ka yi zancen auren Zaytoonah da Auwal ya shiga cikin tashin hankali. Abu ne da ta jima da karanta cewa Auwal na son Zaytoonah, itama ta yi kwaÉ—ayin zumuncin amma ba ta nuna ta san komai ba ne saboda tana so dukkan su su maida hankali a karatu. To gashi kuma Muntari ya zo da wata sabuwa.

ÆŠakin su ta buga ta ce ya zo tana son ganin shi. Kamar marar lafiya haka ya tashi daga kan gado ya sa jallabiya ya fito falo.

"First son ya jikin?"

"Da sauƙi Mommy"

"Dan Allah kanada wani numbar Baffan ku Suleman ne? Wanda na ke da shi ba ya shiga"

"Ya dena amfani da tsohuwar wayar sa an sace wayar. Ina da sabuwar numbar sa barin kawo miki" ya shiga ɗaki ya ɗauko wayar sa ya ba ta numbar ta saka a nata wayar. A take a wajen ma ta kira kuma aka ci sa'a ya ɗauka. Tana fara magana ya shiga ba ta haƙuri na rashin jin sa da su ka yi. Ta ce ma sa ba komai sha'ani na rayuwa. A tsanake ta ma sa bayanin abinda ke faruwa ya ce ta ba shi kwana biyar zai zo Zaria sai su yi maganar da kyau.

Suleman ya bar Ringim da daÉ—ewa ya koma Taraba da zama.
Yadda ya ce É—in hakan kuwa aka yi bayan kwana biyar da maganar su sai ga shi ya zo. Ya je ya samu Muntari ya ma sa faÉ—a ya nuna rashin jin daÉ—in sa akan abinda ya ke shirin yi. Amma sai Muntari ya ce ba ruwan Suleman cikin maganar 'ya dai tashi ce, ya fi shi iko da ita tunda yanzu T J baya nan.

Suleman ya samu Maryam akan wannan magana fa inda ya hango shine tarihine ya ke son maimaita kan sa. Shawaran da zai ba ta shine ta kai ƙara Fada a sasanta su kawai. Tunda da shi da sauran Baffanun na su ba wanda zai ƙi bin maganan Sarki.
Ya ce ta samu Dattawa ma su daraja su je su jagoranceta a Fada a yi maganar, ya tabbata Sarki zai sa a fasa auren nan domin adali ne.
Chapter 49 · 0% Book details