Sashe 33
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
- idan har kina son rage ƙiba ne bisa karan kan ki. Misali, kwana biyun nan na fara yin nauyi fa gara na ɗan zama fit kaɗan (may be nauyin na ɗan sa ki kasala ko ma dai wani issue ɗin daban. Ko kinga kamar ƙiban ki ya fara zama unhealthy) to wannan dalili daga karan kan ki ne kuma ke hangen ki ba wai ki zama siririya ba ce kamar ƙawar ki Zeenatu ko kamar 'yar film Rahama Sadau ko Nargis Fakhri. Abun da ki ke so shine kina son rage nauyi ko kina son ki ɗan sake kaɗan. Then my Sister my brother you just need to change your life style kaɗan ko na ce ka adjusting wasu abubuwa a lamuran ka na yau da kullum. Weight loss is 70% diet and 30% workout or excercise. Ba wai ki ce daga yau na dena cin abinci da yawa ba. Ba haka abin ya ke ba. Za ki saka wasu abubuwa ne cikin abincin da ki ke ci wasu kuma ki rage cin su, a hankali kina inganta lafiyar jikin ki ta hanyar yawan cin vegetables da fruits fiye da carbohydrate. Sannan kina motsa jikin ki daily walau yoga ne kike yi a gida ko kuma dai kina da Gym a gidan ki ne ko kuma kina fita trekking ne ko gudu ko tsalle etc (idan namiji ne buga ball yana da advantage sosai. Idan macece ke kamar ni musamman ma matar aure akwai yoga da za ki iya yi a gidan ki,a ɗakin ki ko falon ki ko ma tsakar gida. Minti 15,20 ko 30 ya isheki a rana depending on your tight schedule. Dancing (rawa) shima yana da fa'ida sosai domin shima motsa jiki ne, ki girgije ƙugu ki girgije jiki za ki ji jikin ki ya yi saƙayau. ( ba wai ki yi sau ɗaya sau biyu ba ki ce ke ba ki ji chanji a jikin ki ba. My Sister ba kwana ɗaya biyu na ke magana ba, ba kuma kiyi sau uku a sati ki share sai bayan sati biyu ki sake yi ba. Ina nufin ki ware minti 15 zuwa 30 a rana ki dinga motsa jiki walau rawa ne ko yoga kiyi haka na sati huɗu ki ji ko za ki ji chanji a jikin ki, ki cigaba ki yi ya kai wata uku ki ga how your body will feel. Ban ce ƙiba za ki rage ba miraculously. Aim ɗin ki ba rage ƙiba ba ne, aim ɗin ki rage nauyi ne da kuma jikin ki ya samu benefits na excercise wanda za ki ji ko malaman lafiya suna emphasizing akan a dinga motsa jiki. Ko mutum siriri ne ma ba a bar ka a baya ba ana so ma riƙa excercise. Yana rage kasala, yana rage stress yana yana yana)...
Chaaiii na gaji da bayani😀
Domin ƙarin bayani kya iya browsing more akan anorexia don samun haske sosai.
Ina ga ma ya kamata na buɗe fitness group Lol😂
Dear 'yar uwa ko ɗan uwa ma su ƙiba kamar ni. Za'a kiramu da sunaye na izgilanci, za a zolaye mu, za'a aibata mu kar ka taɓa bari wannan ya dameka. So what dan muna da ƙiba, so what idan sun zolaye mu da suna ma su muni. We get better things to do than responding to stupid people.
Kar mu koma gefe mu yi kuka ko mu ɓata rai dan ance mana ƙato ko ƙatuwa, Lukuti ko Lukuta etc wanda ya gaya mana mu zare ma sa ido mu yanka ma sa magana har sai ya ji dama bai buɗe shaddar bakin sa ya kiramu da sunan nan ba.
***
" Azumi ki ke yi ne?" Mommy ta faɗa lokacin da ta ga Zaytoonah ta mai da hankalin ta ga kallo ta ƙi cin abinci.
"Zan ci anjima Mommy, yanzun ba na jin yunwa ne"
Salman ya fashe da dariya Mommy ta ma sa dundu a baya
"Mommy wai Zaytoonah ne ba ta jin yunwa caɓɗi"
"Ba na son shirme Salman ka fita a hancin Zaytoonah dan idan ta waiwayeka ba ruwana"
Ya cigaba da cin abinci yana dariya ƙasa-ƙasa.
Lokaci zuwa lokaci tana leƙa su. Yawunta sai tsinkewa ya ke yi yadda ƙanshin jollof rice ɗin ke bugan ta.
Bayan abin da ya faru a wajen reheasal ɗin nan Zaytoonah ta ci kuka sosai. Ƙarshe ma cewa ta yi ta haƙura da karatun gaba ɗaya amma da ta isa gida sai ta rasa bakin yin magana dan tana fara furta maganar rashin zuwa makaranta ƙila Mommy sai ta zaneta. Haka dai ta dinga daddafawa tana zuwa makarantar har su ka fara exams na su, batun debate kam ya sha ruwa dan sai wata aka ɗauka.
Sati biyu kenan da ƙarisa Junior Waec ɗin su. Abinda ya faru ranan ya sa ta tsani makarantar ta su, ranan suna tareda Daddy ta ma sa maganar ba za ta koma wannan makarantan ba a chanja ma ta wata. As usual bai tambayi dalili ba ya ce ta zaɓi wace makaranta ta ke so. Maryam da ke jin su ta ce "tunda ba ta son makarantan inaga boarding school za a kaita ta ƙarisa karatun a chan"
T J ya ce "ba inda za ta je tana nan kusa da mu"
"Ka dai cigaba da sakaltata ni ba ruwana. Yarinya ba abinda ta sani sai ci"
"Ba ruwan ki da 'ya ta. Adaeze ki ci abinci ki ƙoshi sosai kin ji?" Zaytoonah ta gyaɗa ma sa kai...
Zuwa dare ta galabaita, abincin da aka ajiye ma ta flushing É—in sa ta yi a banÉ—aki amma sai da ta É—auke naman ciki ta cinye. Ta yi challenging É—in kan ta cewa za ta rage cin abinci za ta dinga ci sau É—aya a rana saboda tana so kafin ta fara SS class ta koma kamar Humairah. Ga sabon makaranta ga sabuwar Zaytoonah. Zaytoonah siririya wacce ba za a dinga tsokala ba.
Da dare ba yadda ta iya dodging dole sai da su ka haÉ—u su ka ci abincin dare kamar yadda aka saba.
Wasa-Wasa ta cigaba da skipping abinci da safe sai ta ƙi karyawa da wuri idan Mommy ta wuce office shi Salman ya fita ball sai ta flushing abincin ko idan ta ji Almajiri yayi bara ta fita ta zuba mai. Tunda Iya da Humairah su ka koma gidan Muntari T J ya ce Auwal ya koma gidan Hajjo dan gidan zai mata faɗi daga ita sai Sadiq musamman idan T J na gidan Maryam.
Daga gidan Maryam ake tura ma sa abinci ko kuma ya zo ya ci ya tafi. Yanzu ya gama jarrabawar WAEC ɗin sa saura NECO hakanan yana ɗan taɓa ɗinki a shagon Ogan sa. Tun yana JSS3 ya fara fita yana koyon ɗinki gashi shekaru uku ya iya sosai ba laifi.
Da rana ma haka za ta nemi ƙaryar cin abinci tareda su ta ce sai daga baya za ta ci alhali ba ta ci. Ita ba Azumi ba balle ta samu lada sai rashin cin abinci.
A hankali jikinta ya fara weak har Mommy ke tambayarta ko lafiya ta ke ta ce lafiya ƙalau. Sai ta koma dan tana wajen Mommy sai ta daure ta nuna kaman tana nan da ƙarfinta idan ta koma ɗakin ta ta dinga murƙususun yunwa. Daurewa kawai ta ke yi dan it has not being easy musamman saboda yadda Mommy ke chanja salo salon girki ma su daɗi. Wani lokaci har kuka ta ke idan za ta zubar da abincin sai ta lallashi kan ta da cewa nan da lokaci kaɗan za ta dawo siririya kamar Humairah sai hankalin ta ya kwanta. A kwana na biyar ne kuwa ta fara period ɗin ta. Ciwon ciki ne ke ɗan fizgarta kaɗan kaɗan sai ta ɗauka na yunwa ne ta cigaba da dannewa abun ya zo yai yawa. Ta tashi ta wuce banɗaki ko cikinta ne ya ruɗe, ta fita a ɗakinta za ta shiga banɗaki kenan ta ji Mommy ta kirata "Adaeze come here"
Da ta zo gaban ta Mommy ta juyata dan ta tabbatar da abinda ta gani. Jini ne a bayan doguwar rigar da ta sa, jinin ba da yawa ba ne amma kasancewa rigan fara ce sai ya nuna.
Nan Maryam ta mai da ta É—aki ta ma ta bayanin abinda ya faru da ita. Ta É—an ji wani iri musamman yadda Mommy ke karanto ma ta dokoki ma su yawa duk da kuwa an mu su karatun a Islamiyya a Babun Fil Haidhi a littafin Akhdari amma saboda ba ta fara ba ya sa duk ba ta wani sa karatun a ranta sosai ba.
Da T J ya dawo da dare ta ma sa albishir da cewa Adaeze ta zama cikakkiyar budurwa.
"You know what? Nima @14yrs na fara fa"
T J ya ce "ai ba ta cikata 14yrs ba"
"Mi ya saura kuwa tunda saura 21days ne"
T J ya rungumota jikinsa ya ce "barin karɓi tukwuici tunda na zama Baban budurwa"
Kafin Maryam ta yi magana ya fara birkitata da zafafan salon shi ma su rikitata.
Bayan kwana shida.
Tana zaune a falo tana kallo ta ji mai tallen magani yana kirarin maganin sa. Irin. Ma su yawo a cikin motan nan ne suna aza loud speaker a saman mota suna kunna tallen magungunan su.
Yadda ake ta kururuta maganin ƙiba ya sa Zaytoonah ta fara tunanin fita ta siya. Ba kowa a gidan sai ita ɗaya, Mommy da Daddy duk sun fita aiki shi kuma Salman dama indai ana hutun makaranta to ƙafar sa ba ta zama a gida, daga ya je ƙwallo ko ya je shagon su Auwal koma ya je neman tsokala tareda abokanan sa ma su ƙiriniya irin sa.
Maganganun mai tallen na ratsata sosai har ta fara hango kan ta ranan birthday É—in ta wanda ta ke ganin sai ta bawa su Humairah mamaki harda su Nuratu ma da 'yan islamiyyan su musamman Na'ima mai cin tosono lokacin suna yara.
ÆŠakin Mommy ta shiga ta É—au kuÉ—i ta fita da sauri. Hamsin-hamsin ne maganin amma sun ce za su bar ma ta uku É—ari dan haka ta sayi guda shida a naira 200.