← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 161

Sashe 145

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ghazala ta saka dariya kafin ta ce "kin sani sarai Hajia Abu idan ta ji maganan nan ba abinda zai sa ta cigaba da maganan auren Mubaraka da Galadima"

"Na fi ƙarfin ki Ghazala. Idan ƙona kan ki za ki yi sai dai kiyi amma mun riga mun tsaida magana. Nan da wata uku za a kawo miki ƙanwa"

"Ahaf, sai mu zuba ido mu gani, ni da ke wa zai yi nasara"

Daga haka ta katse wayar.

A ɓangaren Hajia Ajwa ta sake tsinewa Yusuf a karo na ba adadi. Wani yaron Igala ne da su ka haɗu da Mubaraka lokacin tana first year ɗin ta a ABU shi kuma yana aji uku. Soyayya ne ya shiga tsakanin su lokaci guda. Shi Yusuf yana baya-baya da Mubaraka saboda ita 'yar babban gida ne amma Mubaraka ba ruwanta. Kafin ka ce me Mubaraka ta fara sake ma sa kuɗi har motar da ta ke hawa ta bashi ta sa Baban ta ya siya ma ta wani. Ana cikin haka 'yan gulma su ka kai wa Hajia Ajwa maganar.
Jin cewa wani yaron talaka ɗan ƙabilar Igala Mubaraka ke soyayya da shi ya sa ta tuhumi 'yar ta da maganar. Mubaraka ta tabbatar ma ta da cewa Yusuf ɗin ta ke so.

Takurawan da aka yiwa Mubaraka akan Yusuf da kuma kashedi da akai wa Yusuf É—in ya sa Mubaraka ta kawo mu su mafita.
A zahiri Mubaraka ta nunawa Hajia Ajwa ta rabu da Yusuf amma a gefe suna nan manne da juna. Wata biyu da haka kuwa Mubaraka ta samu ciki. Dama abinda ta ke nema kenan. Ba kunya ba tsoron Allah ta faɗawa Hajiyar akan tanada ciki kuma so ta ke a barta ta auri Yusuf. Tuni Hajiya Ajwa ta yi maganin zancen dan ko kaɗan ba ta so a ɓata ma ta suna a gari.
Sawa ta yi aka sace Yusuf aka tura shi prison a chan kudu. Mubaraka kuwa ta kaita South Africa aka cire cikin, daga nan kuma ta rufe bakin 'yar ta. Nan da nan Mubaraka ta manta da wani Yusuf ta cigaba da karatu a chan.

Hajia Ajwa mantawa ma ta yi da wani kashin Yusuf. Yana chan kurkuku shekaru huÉ—u kenan ba tareda laifin komai ba...

Ghazala ta kira Hajia Abu ta sanar ma ta komai gameda cikin da Mubaraka ta yi a baya. Hankalin Hajiya Abu ya tashi ta ce ai ba zai yiwu Galadima ya auri macen da ta gama gantali a titi ba. Suna gama wayan ta dannawa Hajia Ajwa kira ta nemi tabbacin abinda ta ji daga wajen Ghazala. Hajia Ajwa ta ce ba ta san komai ba, amma ina Hajia Abu ta janye maganar aure.

Suna gama waya da Hajia Abu ta dannawa Bokan ta kira. Shekarun baya da ta kai maganar Mubaraka ce ma ta yai ƙaddaran Mubaraka haɗe ya ke da ta Yusuf hakan ya ƙara tunzurata. The last thing she wish shine 'yarta ta auri talaka, talakan ma ƙabila.

"So na ke ma ka fara fitar min da Ghazala a gidan tun kafin ma Mubaraka ta shiga gidan. Auren Galadima da Mubaraka na ke so nan ba da jimawa ba. Kai nan da wata É—aya ma ayi shi"

Ko mi Bokan ya gaya ma ta oho sai kawai ta ma sa godiya ta ajiye wayar.

Mubaraka da ta zo shiga ɗakin mahaifiyarta ta juya da baya da sauri. Tuntuni maganin da aka ma ta akan manta Yusuf ya ɓace. Da ta dawo Nigeria ma a ɓoye ta ke ƙoƙarin binciko inda ya ke duk da iyayen sa sun yi amanna da cewa ya riga ya mut, ita kam tana ji a ranta bai mutu ba mahaifiyarta dai ta ɓoye shi.

Tana shiga ɗaki ta ɗau wayarta ta kira ƙawarta Gimbiya Safiyya ƙanwar Galadima. Ce ma ta tayi ta turo ma ta numbar wayar Galadima. Ita kuwa Safiyyar ta fara tsokalar ta akan soyayya ta kankama kenan. Dan tuni maganar Mubaraka da Galadima ta fara yawo a Fada.
Bayan ta turo ma ta numbar ne ta tura ma sa saƙo. Kusan minti biyar sai ga shi ya yi ma ta reply.

Zuwa yamma ta samu Hajia Ajwa akan za ta je Abuja gobe akwai wani aikin NGO da ta cika kuma za a mu su interview gobe. Hajia Ajwa ba ta kawo komai ba a ranta ta ce ta je. Har da cewa idan ma ba za ta dawo a ranan ba ta wuce gidan Galadima ta kwana a chan. Da gayya ta faÉ—i hakan tunda ta san ba Galadima ne kaÉ—ai É—an uwan su da ke zaune a Abujan ba. Tsokalar Ghazala ta ke son yi.

Washegari ƙarfe shabiyu ta wuce kaɗan Mubaraka ta sauka a office ɗin Galadima.
Ba dan zuciyarta ya jima da son Yusuf ba da ba abinda zai sa ta ƙi haɗin da ake son ma ta da shi. Ba kyaun sa kaɗai ke jan mace gareshi ba sai dai kwarjini da Allah ya bashi. Har yau idan ana hawan sallah idan har ba ka tsaya ka ga tawagar Galadima ba to kaman ba ka ga hawan sallah ba. Kwarjinin sa ya jawo ma sa mutane.
Lokacin da yake zawarci kafin ya auri Zaytoonah Mata dayawa suna kawo ma sa wargi, idan ka ga saƙonnin da Mata ke tura ma sa a rana sai ka sha mamaki. Lokacin da ya auri Zaytoonah ne ma abin ya zo ya ragu sosai.

"Ina jin ki Mubaraka"

Mubaraka ta sunkuyar da kan ta ƙasa ta fara magana dan idon sa ya ma ta nauyi.
Sai da ya gama sauraron bayanan ta kafin ya É—aura da na shi. Lokacin da ta fita a office É—in ne ya sauke ajiyar zuciya yana faÉ—in "Ya Allahu!"

Miyasa wasu Matan ba su da hankali ne? Akan namiji sai mace ta jefar da mutuncinta ta take dokokin Allah.

Yanzu kam lokaci yayi da zai fito da komai waje. A da ya bari sai ranan da za su je supposed honeymoon trip ɗin da Ghazala ta shirya ne sai ya fito da komai waje, amma yanzu dole ayita ta ƙare dan delaying it further will ruin things...

Bayan ya tashi daga office kai tsaye gida ya wuce inda ya samu Ghazala a É—aki tana lissafin kasuwancinta. Ce ma ta yai gobe ta shirya za su je Zaria Sallama tunda tafiyar ta su nan da kwana huÉ—u ne.

***

"Aje ayi sallah sai aci abinci" Mommy ta faɗa bayan ta fito daga kitchen. Tuntuni aka kira sallan la'asar amma surutun da su ke yi ya hana su tashi gashi har ƙarfe biyar saura kwata.

Yaran kamar kar su bar jikin Uban su musamman Junior da Zaytoonah. An ji na Junior shi sai yau ya fara ganin uban sa a zahiri ita kuma Zaytoonah sakalci ne na ta na iyashege daya haÉ—u da jin daÉ—i.

Mommy ta kama hannun T J ta yi ɗaki da shi, suna shiga ta nemi sakata ta saka. Sake rungume shi ta yi sosai tana ƙara jin wani sabon son sa na shiga jikin ta.

"Sadiq ya rasu ko?" Ya tambaya a hankali.

Ta É—ago kan ta ta ce "ya rasu ranan da na haifi Junior"

"Allah ya ma sa Rahama" ta amsa da Amin.
Suna tsaye rungume da juna kusan minti biyu kafin Mommy ta ce su ƙarisa banɗakin. Ruwa mai ɗumi ta haɗa ma sa kafin nan ta shiga cire ma sa kaya. She missed those days da su ke komai tare.

A hankali ya furta "kin tuna wani rana mun yi faÉ—a kika zo cire min kaya kika rufe idon ki, kika yi haka da fuska"
Ya faÉ—a yana juya fiskarsa gefe kaman yadda ta yi ranan.
Tabbas ta tuna ranan. Da ke idon ta a rufe ya ke ba ta san sanda ya rankwafo kai ya haÉ—a bakin su ba and that's how the fight ends ranan.
Yanzun ma haɓarta ya ɗago sannan ya ɗaura bakin sa saman na ta...

Ba su fito daga wanka da wuri ba dan suna fitowa daga banɗakin 'yan biyu suka fara ƙwanƙwasa ƙofa suna faɗin wai kowa yayi sallah su ake jira.
"GrandPa GrandMa ku fito mana"

T J yai murmushi.

"Ai indai 'yan biyu ne za ka yi dariya ka gaji"

"Miyasa Aka yiwa Zaytoonah auren wuri?
Dan dai idan ba auren wuri aka ma ta ba, ba yadda za ayi ta haifi yara kaman 'yan biyu."

"A hankali za ka ji labarin komai. For now, bari mu yi sallah"

Cikin tsofin kayan sa da Mommy ke sawa ta bashi wani riga da wando ya saka. Shine ya ja su sallar, bayan sun idar su ka gabatar da godiyan su ga Ubangiji.

Bayan sun fito a tsakiyar falo su ka zauna aka matsar da kujeru aka ajiye ƙaton silver tray. Zaytoonah da Humairah su ka taya Mommy serving abincin. Tuwon shinkafa aka yi da miyar egushi wanda ya ji nama, Stockfish da Pomo. Miyar egushi is one of his best miya shiyasa ta mi shi.
Zaytoonah ce a gefen Daddy na hagu yayinda Mommy ke É—aya gefen.
Lokacin da aka fara cin abincin Salman ya tsaya ya ƙi sa hannu.

"Salman ya ba ka ci?"

"Daddy ni kai na ke son ka bani a baki"

"CabÉ—i, wallahi Daddy ka bashi sai ka bani. Ai ni ce Princess É—in ka" Zaytoonah ta faÉ—a tana tura baki.

T J yai murmushi ya ce za'a ba ta itama. Zaytoonan ya fara bawa loma ɗaya a baki kafin ya koma kan Humairah sai kuma Salman da Junior. 'Yan biyu su ka matso kusa wai suma a basu. Ganin anyi sau biyu za'ayi na uku Mommy ta riƙe hannunsa ta ce " ya isa haka ko bari ya ci abinci a nitse"

"Lah! GrandMa ta yi fushi dan ba'a bata a baki ba" Hadid ya faÉ—a hakan ya sa gaba É—ayan su suka sa dariya.
T J ya ce " bari itama a bata na ta" ya miƙa ma ta lomar abinci a baki. Suna cikin cin abincin Auwal ya fara ƙwanƙwasa ƙofa dan sun riga sun kulle ƙofan Falon. Humairah ta miƙe da sauri ta je ta buɗe ma sa.

"Mi ya faru aka rufe ƙofan? Na ɗauka ma ba kwa nan..."

"Hamma, Daddy, Daddy ya dawo"
Chapter 145 · 0% Book details