← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 161

Sashe 138

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarisawa ta yi wajen Suhailah ta ce ta zo su je a ma ta wanka.

Zuwa awa É—aya da su ka biyo baya dukkan su sun yi wanka sun yi sallah. Yayinda aka gabatar mu su abinci a wajen dinning area.
Za ta zauna a wajen Mommy ta ce ta je ta kaiwa Galadima abinci É—aki. Haka dai ta É—auki tray da aka jera ma sa abincin sa ta wuce da shi É—aki.
Zaune ta sameshi riƙe da tasbaha yana azkar. Ta ajiye abinci a gefen sa ta miƙe za ta tafi amma sai ya riƙe hannun ta.

"Ina za ki je kuma?"

"Wajen su Mommy"

Hannunta ya kai bakin sa ya kissing sannan ya ce "zauna mu gaisa"

Dawowa ta yi ta zauna yayinda shi kuma ya jawota jikinsa sosai sannan ya cigaba da azkar da ya ke. Bayan kusan minti goma kafin ya gama ya ajiye carbin ya kalle ta ya ce "har yanzu dai ba a yafe min ba kenan"

"Ni ban ce ba" ta faÉ—a tana tura baki.

Hannunta ya haɗa da na sa ya riƙe gam kafin ya ce " ba ki san farin cikin da na ji ba da na ɗauki Alinah a hannuna. Ji na yi tamkar ranan da na karɓi Raziya a hannuna. Thank you Qurratul ayn"

Shiru ta yi tana jin daÉ—in kalaman sa.

"Sai gashi na zo ko gaisuwa ban samu daga gareki ba. Allah ka taimaki wannan Bawa na ka a wajen Gimbiya Zaytoon"

Murmushi ta yi kafin ta ce "ina wuni, fatan ka iso lafiya"

"Idan irin wannan gaisuwan ne ai tun ina Nigeria na ke jin ta. Gaisuwan Mata ga Mijin ta na ke so"

"Ba gashi na yi ba..."

Tallafo fiskanta yai ya haɗe bakin su. A hankali ya dinga sarrafa harshen ta cikin ƙwarewa. Kusan minti ɗaya kafin ya cire bakin sa ya ce "wannan gaisuwan na ke so Umm Alinah"

Ya riga ya kashe ma ta jiki dan haka ba ta iya cewa komai ba hakan ya bashi daman sake haɗe bakin su ya cigaba da kissing ɗin ta, itama kawai ta sa hannu a wuyan sa ta ƙara jawo kan sa a lokaci guda kuma tana yiwa ƙeyar sa zuwa wuyan sa tafiyar tsutsa.

"Anty Alinah tana kuka" maganar Suhailah ya katse mu su gaisuwar masoya.

Muryar ta da ya shaƙe ta ce "ina zuwa yanzu"
Bayan fitar Suhailah daga ɗakin Galadima ya fara ƙoƙarin cigaba da abinda su ke ta yi saurin saka hannu ta tare bakin sa ta ce "barin je na dubata"

"Ki kawota nan" ya faɗa tareda kissing hannun ta sannan ya sake ta, ta miƙe ta fita daga ɗakin. Har ta je ta karɓota kuwa yarinyar ba ta bar kuka ba, tana zuwa Galadima ya karɓeta yana ɗan jijjigata ko minti ɗaya bai cika ba ta yi shiru. Zaytoonah ta ce " ji min 'ya da gulma"
"Ba ruwan ki da ita ba ta gaji da jin É—umin Uban ta ba ne"
"Oh haka ko"...

***
Tun kafin su gama cin abinci ya roƙeta akan ta rakashi wani waje. Tsokalar sa ta yi akan bai san gari ba ina zai je da yammacin nan. Ya ce ma ta zai je ganin wani abokin sa ne da su ka yi karatu tare shima yanzu Alƙalina a nan Las Vegas ɗin.

"Ka bari mu tafi gobe, ko hutawa ba ka yi ba fa"

"Gara mu je yau É—in gobe kin ga sai na huta sosai"

Ganin yadda ya dage ma ta ya sa ta amince. Ta je ta sake watsa ruwa a gurguje ta shirya sannan ta samu Mommy a É—akin ta tana yiwa Alinah wankan yamma.

"Mommy zan raka Daddyn Raziya wani waje yanzu zamu dawo"

Mommy ta bi ta da kallon tuhuma.

"Mommy ba zamu jima ba, ya ce za mu je gaida abokin sa ne"

Da toh kawai Mommy ta bita. Dan ba ta da hurumin shiga tsakanin miji da mata. Sanin cewa Zaytoonah ta yi tsarki ya ƙara tabbatar da zargin da ta ke yi, fatan ta dai kar Zaytoonah ta yi kwunika dan ba ƙaramin wahala za ta sha ba. Wannan haihuwar ma dai kariyar Allah ne kawai dan ta wahala watanni biyu kafin haihuwar. Mommy ba ta ma ɗauka Zaytoonan za ta iya haihuwa da kan ta ba, sai ga shi haihuwar ta zo ma ta cikin sauƙi.

Dreban gidan ne ya fita da su sai dai maimakon Galadima ya bashi address É—in gidan da za su je sai ya bashi address É—in wani hotel a fakaice ba tareda Zaytoonah ta ji ba.

Suna tafiya suna É—an taÉ—i wanda yawanci kan harkan shari'ar da ya ke yi ne har su ka isa hotel É—in. Sai da motar ta tsaya Zaytoonah ta kalli inda su ke da kyau kafin ta maida kallon ta ga Galadima wanda ya kashe ma ta ido É—aya.

" Allah dai ya hana ƙarya Justice"

"Akwai ƙaryar sunna ai Yallaɓiya" ya faɗa yana murmushi.

"Hmmm"

Suna shiga katafaren hotel ɗin ya booking mu su ɗaki ya karɓi key sannan su ka wuce. Ita dai Zaytoonah na ta ido, abu ɗaya ta sani ko yafi ruwa gudu yadda ya ganta haka zai barta.

Suna shiga É—akin ya rungumeta sosai kamar zai maidata jikin sa.

"Ranka shi daɗe ban da ƙarfi fa yanzu za ka ɓallani"

"Na yi kewar ki sosai Zaytoon ki tausaya min"

"Ni dai ka sake ni, kana chan da matar ka za ka ce ka yi kewana. Ni ban yarda ba"
Cireta yai daga jikinsa ya ƙura ma ta ido. Zaytoonah ta haɗe rai tana tura baki.

"Yanzu Princess ..."

" yanzu daka zo ba, da ai ni mahaukaciya ce a wajen ka ba Princess ba"

"Ya Allah!" Ya faɗa yana dafa kai. Mace dai sunan ta Mace. Tun a waya su ke fama da maganan nan kuma ta nuna ta haƙura yanzu kuma za ta chaza ma sa kai.
Ko da ya ke Mace dama sai da lallashi balle kuma ita da ya ba wa tazaran shekaru sosai haka.

Riƙe hannunta ɗaya yai ya marairaice murya ya ce " haba Qurratul ayn na ce ki yafe min fa kuma kin ce kin yafe"

"Ya wuce ai, nima yadda aka shareni aka jefa ni a kwandon shara yanzu sai a barni na huta ai. Dan ni da Nigeria sai na yaye Alinah. Ka je chan ka zauna da Aaamaryar ka" ta ja sunan Amaryar da gayya.

"Da gaske" ya faɗa bayan ya sa hannunsa a ƙugunta ya jawota daf da shi.

"Da gaske mana. Kai ma..." bai bari ta ƙarisa ba ya haɗe bakin su. Irin yadda ya ke sarrafata da zafi-zafi ya sa ta ajiye makaman yaƙi ta fara biye ma sa. As if ya ma ta magani dan daga kiss kawai ta ji notinan kan ta ya kunce dan gaba ɗaya ta manta niyyar ta, ta manta iƙirari da cika baki da ta yi- ta yi lokacin da su ka shigo hotel ɗin.

Lokacin da ya kwantar da ita kan gado half naked yana ƙoƙarin janye pant ɗinta ta ce " Sayyidi ban yi tsarki ba"

"Allah ya tona asirin ki ai, kin san addu'an wanda aka zalinta ba ya faɗuwa ƙasa banza. Iya waɗannan watanni kuma ace na zo na samu shamaki tsakani kinga ai zalunci ne"

Wannan mutumi kaman maye, ko ya akayi ya san inada tsarki oho. Ta faÉ—a a zuciyarta a fili kuwa ta ce "Ba wanda ya zalince ka sai.. ahhhh"...

Bayan dukkan su sun samu nitsuwa ne ta tambayeshi ya aka yi ya san tanada tsarki. Shine ya ce kwanaki uku da su ka wuce da ya kira Mommy ya ce a bawa Zaytoonah wayan su gaisa sai ta ce Zaytoonan na sallah.
Kwanaki shatara kawai ta yi jinin ya tsaya gashi yau kwanan ta talatin da É—aya da haihuwa bai sake dawowa ba.

Zaytoonah ta fara miƙewa ta shiga banɗaki dan fitsari ta ke ji bayan ta gama kuwa ta duba wajen shower ɗin ta ga yanada option ɗin ruwan ɗumi dan haka kawai ta fara shirin wankan tsarki. Tana cikin wanka aka buɗe ƙofan banɗakin. Ba shigowar sa ba ne ya ba ta mamaki sai dai kawai gani ta yi ya cire boxers ɗin da ke jikin sa ya tako har wajen da ta ke tsaye ruwa na zubo ma ta a kai.
Saurin rufe ido ta yi da tafukan hannunta duka biyu tana murmushi. This is the first time da ta gan shi haka, completely naked.
Mutum ne mai tsananin kiyaye magana a banÉ—aki shiyasa suka koma maganan kurame.
Cire hannun ta yai a fiskar ta ya É—aga ma ta gira, ta yi saurin sunkuyar da kan ta tana cigaba da murmushi tana tunanin anya Galadiman da ta sani ne kuwa yau É—in nan.
Ya ɗago haɓarta tareda manna ma ta kiss a baki yana cigaba da shafa ilahirin jikin ta...

Yau dai na farko a tarihi Galadima ya cire kunya ya bari sun yi wanka tare infact ita ne ma ta cuccuÉ—a shi sai da ta gama yai wankan tsarkin da kan sa.
Da su ka gama kuma suka fito manne da juna dan kusan towel É—aya suka yi amfani da shi.

"Yau da a India mu ke da sai na ce ko sai da ka biya gidan Sharukh Khan kafin ka zo nan" ta faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin saka ma sa kaya.

"Wani banza kuma Sharukh Khan bayan muna da karatun soyayya daga wajen fiyayyen halitta"

"Allahu Akbar! Sheikh yau Limanci ne ya zo kenan" Zaytoonah ta faÉ—a tana dariya.

"Let's just say ina son na tanadi 'yan mata na da kyau ne"

"Allah ya ƙara maka lafiya nawan"

Tafiya ta ɗauka za su yi amma koda su ka yi sallar Isha gogan ya waske wai bai shirya tafiya ba ƙarshe ma dai sake gabatar da wani sabon kalar soyayyar su ka yi.

Gaba É—aya sun manta da mutanen da su ka bari a gida balle kuma 'yar jinjira baiwar Allah.
Chapter 138 · 0% Book details