← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 161

Sashe 115

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa su ke yi da Suhailah shine ta shiga banɗakin su ta yi fitsari da ta fito kuma ta ce wandonta ya jiƙe sai ta cireshi ta ajiye a ƙasa. Da ke Hadid ya fara bacci sai suma su ka kwanta akan gadon Hadid ɗin. Da ke gadon ya mu su kaɗan su uku shine cikin bacci Hadid ya ɗaura ƙafar sa ɗaya akan Suhailah.
Wannan Ghazala ta shigo ta gani, dama abin nema ne ya samu kawai ta ɗauko belt ɗin yaran da ta gani a ƙasa ta fara dukan su , kukan yaran ya sa Falaq da Raziya su ka shigo ɗakin da gudu kafin da Falaq ta ga dukan yayi yawa ta je ta kirawo Zaytoonah...

***

Fitowar da yai daga É—aki dan ya fita sallar magariba saboda yaran sun yi bacci yai ido huÉ—u da Zaytoonah.

"Ka fito min da yara na, tafiya za mu yi"

"Ba inda za ki kaimun yara da daren nan"

"Oh really! Ta nan kuma ka ɓullo. To ba zai yiwuba, Yara dai ni na haifesu kuma ina da ikon tafiya da su duk inda na ga dama sai dai idan muguntar ce ta tashi sai na sani"

"Zaytoon ki matsa zan je sallah"

"Ni ban ce kar ka je sallah ba amma ka fitomin da 'ya'ya na. Na gaji da zaman gidan da ba a É—auke su a bakin komai ba"

Cikin kuka ta cigaba da magana " da ni ce na daki yaran ka da yau ko'ina sai an jimu amma nawa yaran gashi nan ai ba abinda ka yi ma ta. Nan nan saboda na saka Raziya aiki ba tareda ka bi bahasin mi ya faru ba ka ɗau fushi da ni ƙarshe ma Aure ka ƙara. To na gaji, na gaji da take hakkin da ake min a gidan nan. Komai idan aka ce ni ce ba za ka taɓa bincike ba sai dai ka hau maganar da aka gaya ma ka ka yanke hukunci. Ba zan iya ba Daddyn Raziya ba zan iya ba"

Sosai maganganun sa su ka taɓa shi amma ya daure ya ce " idan na dawo daga masallaci za mu yi magana"

"Ba wani magana da za mu yi, ka bar ni kawai na tafi da 'ya'yana idan ba haka ba zaman Allah ya isa za mu yi a gidan nan"

Ya É—ago rinannun idanun sa ya kalleta, murya a raunane ya ce " yanzu dare yayi, Dan Allah ki bari gobe sai ku tafi"

Yadda yai maganar ya sa ta ji ba za ta iya ma sa mu su ba. Ga shi itama ta san ba ta iya tuƙi da dare saboda duhu.

Ranan dai yaran a wajen Justice su ka kwana. Shi Justice tun da ya fita sallah bai dawo ba sai kusan ƙarfe shaɗaya na dare. Gaba ɗaya maganganun Zaytoonah sun tsaya ma sa a rai musamman maganar zaman Allah ya isa da ta ce za su yi.

Washegari ƙarfe shida da rabi suka ɗauka hanyar Zaria. jikin Hadid ma ya warware dan dama kukan da yai ne ya sa ma sa zazzaɓi.

***

Junior ne ya buɗe mu su ƙofa su ka shigo. Mommy na zaune a falon tana shan tea. Yaran su ka yi kan ta da gudu suna kiran GrandMa.

"Mommy ina kwana" ta faÉ—a yayinda ta ke dai-dai ta tsayuwar akwatin ta.

"Lafiya" ta amsa ba tareda ta É—ago ido ta kalleta ba.

Zaytoonah ta ƙarisa da akwatin cikin ɗaki ta sake fitowa ta ɗauko sauran kayan har lokacin yaran na manne jikin Kakar su.

Kusan har dare Mommy ba ta yiwa Zaytoonah maganar zuwanta ba. Infact bayan gaisuwan da ya haÉ—asu ba ta sake ce ma ta uffan ba. Jikin Zaytoonah yai sanyi tana ma tunanin ko Justice ne ya kirata ya gaya ma ta wani abin amma kuma ba halin sa ba ne.

"Mommy ki yi haƙuri Dan Allah, na san ba haka kika so ba amma Mommy i'm not happy in that house. Ni bare ce. agidan nan, Daddyn Raziya bai damu da ni ba, ya fi bawa Amaryarsa muhimmanci and 'yan biyu ba su da walwala a gidan nan. Ba ni da farin ciki a gidan..."

"Allah shi kyauta"

"Mommy ki fahimce ni please"

Murfin tukunyan da ke hannun Mommy ta sake ya faɗi ƙasan tile yana bada ƙaran gararanran.

"Na fahimce ki Zaytoonah, na fahimci ke wawuya ce kuma daƙiƙiya. Duk tarin ilimin da ki ke da shi ba shi da wani amfani a gareki. Ba ki da farin ciki a gidan ko? To Allah ya baki farin ciki a nan ɗin"

Kuka Zaytoonah ta fashe da shi dan yadda ta karanci tsantsar ɓacin rai tattare da Mommyn.

"Ki yi duk abinda ki ka ga dama, ba zan sake saka baki cikin lamarin ki ba. Idan ma so ki ke ki kashe auren ki dan ki auri Auwal Bismillah, idan wani daban ma za ki aura Allah ya baki sa'a, idan kuma zama za ki yi haka ba aure duk ba ni da matsala da hakan"

"Mommy you know its not about Auwal. Farin ciki na, farin cikin 'ya'ya na su ne kan gaba akan komai, kuma babu shi a gidan Justice" ta yi maganar cikin kuka.

Mommy ba ta ƙara cewa komai ba dan yadda zuciyarta ke tafasa idan ta cigaba da fitar da abinda ke cikinta za ta iya samun matsala.

Zaytoonah ta fice daga kitchen É—in ta wuce É—aki da gudu.

Lallai yaro ba shi da amana. Tana shiga É—aki ta samu Yaran na waya da Justice.
Tana ji suna faɗin sun missing ɗin sa ta yi saurin ƙwace wayar ta katse kiran.

"Wa ya ce ku kirashi?"

"Shine ya kira" Hadid ya ba ta amsa.

"Maza ku je wa je ku yi wasa"

Sake kiran wayan aka yi a karo na biyu. Kamar ba za ta É—auka ba sai kuma ta É—auka kiran lokacin yana gab da yankewa.

Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

"Gobe zan shigo, ina so ki bani dama mu yi magana"

Kashe wayar ta yi ta kifa kan ta tana sauke ajiyar zuciya.

Daren ranan ita da Mommy haka su ka koma tamkar kurame ba wanda yai wa wani magana.

"Mommy i'm sorry about yersterday"

Zaytoonah ta faɗa lokacin da Mommy ke shirin miƙewa daga sallayar da ta yi sallar Asuba da shi.

"Ba komai, rayuwar ki ce ai"

"Mommy ban san ya zan yi ba, i tried my best amma komai baya tafiya dai dai"

"Akwai auren da ke tafiya dai-dai ne?"

Sai da ta zauna bakin gado kafin ta cigaba "babu auren da ya ke tafiya dai-dai. A yadda ya zo da targaÉ—e É—in ke ce za ki yi ta seta shi har a samu ya tafi miki dai-dai yadda za ki samu farinciki a cikin sa.

" watan ki nawa da aure Zaytoonah har kina complain ɗin kin gaji. Ki gaya min tsakanin ki da Allah a cikin watanni takwas da ki ke zaune da Galadima kin yi ƙoƙarin sauke duka haƙƙoƙin sa da ke kan ki? Kin yi iya ƙoƙarin ki wajen ganin an samu zaman lafiya a zamantakewar ku da matar sa da kuma 'ya'yan sa?.

"Indai kin yi dukkan wannan kuma kina ganin ba ki samu farin ciki ba. Bismillah ki yi yadda ran ki ya ke so, ni dai nawa ido. Amma har wa yau ni a wajena Galadima mutum ne mai gaskiya"

Shiru Zaytoonah ta yi tana tunani. Tabbas ko da akwai laifin Justice to itama mai babban laifi ce. She can't believe that har ta yi wata takwas a gidan Justice. Bawan Allah yana nan yana zaman jira ta gama hutu.

"Ki ji tsoron Allah Zaytoonah. Wannan Bawan Allah ya mana ƙoƙarin da ba mu isa mu biya shi ba sai dai kawai mu ma sa addu'a amma still kina tuhumar sa da zalunci. Ni na haifeki kuma na san halin ki sarai. Ko kaffara ba zan yi ba idan na rantse cewa ba ki bawa auren ki muhimmanci ba. Auren da ba ki ɗauke shi a bakin komai ba ta ina za ki samu farinciki a cikin sa?"

"Idan farincikin 'ya'yan ki kike nema, to yana tareda Galadima, idan kuma wasa da hankali za ki mu su to ga ki ga su"

Haka Mommy ta cigaba da yi ma ta nasiha. Gaba É—aya sai nadama ya sauka ma ta.

Da rana ta fito daga wanka kenan, sai ga kiran Justice a wayarta. Ta yi sauri ta ƙariso ta ɗauka. Ce ma ta yai ya shigo Zaria yana son ƙarisowa gidan su ta ce ma sa to.

Minti hamsin da maganar su sai ga kiran sa lokacin Mommy ta dawo daga school.
Tana É—aukan kiran ya ce ta fito yana waje.

Hijab kawai ta saka ta fito ta sami Mommy na yiwa Junior faÉ—a.

A kunyace ta ce "Mommy xan fita, Daddyn Raziya ne ya zo"

"Shine za ki bar shi a waje"

Zaytoonah ta yi shiru tana É—an sosa kai.
"Ki je kar ki sa shi jira"

Tana buɗe gate ta hango Motar sa, ta ƙarisa wajen. Tun kafin ta ƙariso ya buɗe ma ta ƙofa dan haka kawai ta shiga gidan gaba tunda shi da kan sa ya tuƙo Motar.

"Barka da rana"

"Barka"

"Ya yaran?" Ta yi tambayar ne ganin shirun na su yayi yawa.

"Sun yi missing É—in ki"

"Anya kuwa?"

"Sun yi missing É—in ki sosai fa"

"Hmmm" kawai ta ce ta yi shiru.

"Ikon Allah" ta furta lokacin da ta hango yaranta akan Keke suna nufo su.

"Motar Daddy ne wannan" Hashir ya faÉ—a lokacin da su ka zo dai-dai bakin Motar.

Justice yana shirin buÉ—e window ya mu su magana Zaytoonah ta dakatar da shi. "ka bar su kawai, yanzu sai su ce sai sun shigo"

"Na ga alama dai da ƙarfi so kike ki raba Uba da 'ya'yan sa"

Ta wajen glass Hadid ke leƙawa saboda Motar tinted ce.

"Hadid ba kowa a ciki ka zo mu shiga gida, yana cikin gida".

"Hashir ina ga Daddy ya zo É—aukan mu ne fa. Idan Mom ta ce ba za mu bi shi ba ka san me za mu yi?"

Hashir ya ce "a'a"

"Da Baba Tsoho za mu haÉ—ata"
Chapter 115 · 0% Book details