Sashe 120
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe tara da minti Arba'in da ɗaya Zaytoonah ta yi sallama a falon gidan ta. Justice na zaune yana karanta jarida wanda maganar gaskiya bai ma san mi ya ke karantawa ba.
Ghazala na zaune kusa da shi tana kallo. Tunda ta ga ya dake a falon ƙasan itama ta zauna dan ganin ya lamarin zai kaya.
Sallama ta yi mu su za ta wuce ta ji ya ce " ina ki ka je?"
"Inda na gaya ma ka zan je mana where else?" ta faÉ—a tareda haurawa stairs É—in.
Tausayin Muhsina, haushin Maza, gajiya, duka ya haÉ—u ya dagula ma ta lissafi.
Ga shi wannan ma zai dameta da ina ta je ?, bayan ta tura ma sa text akan ta kawo Muhsina Asibiti ba lafiya. Ko ya mai jiki bai ce ma ta ba sai tambayar ina ta je.
Tana shiga É—aki shima ya shigo.
"Idan ina magana ki ka sake barin wajen ba tareda na baki izini ba za ki sha mamaki a gidan nan"
Yadda yai maganar da ƙarfi ya sa ta sha jinin jikin ta.
"A wani dalilin kika fita a gidan nan ba tareda kin yi abinda na sa ki ba?"
"Dan Allah ka bar ni, ba fa ni ɗaya ba ce a gidan nan. Na ce Atika ta ƙarisa girki zan fita, miye a ciki?. Ko so ka ke na tsaya girki har Muhsinah ta mutu saboda ni na kawo girki duniya. Ku maza kullum kan ku kuka sani. It always about you you you and you" ta yi maganar da tsawa.
"Zaytoon!"
2/11/21, 10:04 PM - ****: 59
Bismillahir Rahmanir Rahim
*pay back*
Hajiya Ghazala dai ta amshi girki ne da hannun hagu. Tayi shiri da zuwan Galadima baƙon wata kuma ya zo ya ma ta sallama. Abu ya zo ya haɗu ma ta goma da ishirin.
Kwana biyun da Justice yai a wajen ta kamar ta haɗiyi ran ta dan baƙin ciki. Daga yin yaji shikenan sai Zaytoonah ta dawo da sabon salon bariki.
Ranan da Zaytoonah ta amshi girki tana kula da ita dan ta tabbatar da hasashenta na shiryawan ta da Justice. Tun daga irin kwalliyar da ta sha ma ta san an riga an wuce waren kawai.
Ba ta taɓa ɗauka Zaytoonah za ta Farga da shiririntanta nan kusa ba.
Ba ma a dining table ta serving Justice abinci ba. Chan falon sa ta ajiye ma sa abinci, da ya dawo daga sallar Isha su ka zauna cin abincin, ana ci ana hira.
Ghazala na falon ƙasa Zaytoonah ta sauko da kwandon da ta tattare sauran abincin da su ka ci ta kaishi kitchen. Dogon hijab ta saka ajikin ta dan haka ba ta ga kayan da ta saka ba amma yadda hijabin ya lafe ma ta tunanin Ghazala biyu ne, ko dai Zaytoonah ba ta sa komai a ciki ba ko kuma abinda ta saka ɗin bai kai ma cinya ba.
Zaytoonah da ta fito yaran ta da ke kallo ta tattare ta tisa ƙeyar su zuwa ɗaki. Bayan sun yi brush ta sa mu su kayan bacci, ta bita mu su addu'ar bacci sannan ta fito daga ɗakin ta wuce turakar Mai gida, tana shiga ta saka key ta kulle ƙofar falon dan da za ta shigo ta ga Ghazala ta fito daga ɗakin ta tana bin ƙofar falon da kallo.
Kusan har ƙarfe shabiyu Ghazala na jiran ta ga Zaytoonah ta fito daga sashen Galadima kaman yadda ta saba amma shiru ka ke ji kaman Shaho ya ci Shirwa.
"Shegiyar Yarinya, wanda ya ba ta shawaran ta gyara halinta bai yi ba wallahi"
Ghazala ta faÉ—a tana jan tsaki. Tana mugun kishin Zaytoonah amma tunda ta gano zaman doya da manja ne tsakanin su da Justice ta É—an sassauta kishinta, to yanzu kuma Zaytoonah ta farka daga baccin da ta ke yi.
Baccin kirki ba ta iya yi ba ranan...
Sati uku kenan da dawowar Zaytoonah gidan, yanayin zaman gidan ya chanja salo. Shi kan sa Justice yanzu ne ya san yana auren mata biyu. Ta ko wani fanni shi É—an gata ne.
"Abu Razz inada magana"
"Ina jin ki" ya faÉ—a yana cigaba da cin abinci.
"Ni tun da ka min magana akan 'yan biyu ina tsoron saka baki akan harkan Zaytoonah. Kamar ba ka so a faÉ—i aibunta.
"Idan na yi shiru ni zan cutu shiyasa na ce dai gara na maka maganar dan ko za ka iya yi ma ta bayani dan ta É—au mataki saboda lafiyar mu gaba É—aya"
Yanzu kam ajiye cokalin hannun sa yai ya maida hankalinsa kan ta yana sauraren ta.
"Dama kwana biyun nan idan muna tare na kan É—an ji zafi-zafi haka. To sai na kira Likita na ma ta bayani sai ta ce na zo a min gwaji. To daga Shago jiya sai na wuce Asibitin aka min gwaji aka kuma tabbatar min da infection ne, irin infection da ake samu wajen saduwa. An rubuta min magani kuma na siya.
"Na ce Dear mi zai hana itama Zaytoonan ta nemi magani sannan ko za ka ɗan yi haƙuri da ita na ɗan wani lokaci zuwa dukkan mu mu samu lafiya. Ka san ance idan ku biyu ne a wajen Miji idan ɗaya tana shan magani ɗaya ba ta sha kaman a banza ta ke yi dan za ta ƙara samun sa"
"Idan mun gama cin abinci sai ki kawo min maganin na gani" ya faÉ—a bayan ya sauke numfashi.
Bai wani ƙara abincin ba ya tura plate ɗin gefe ya ce ya ƙoshi. Bayan Ghazala ta tattara wajen ta je ta ɗauko magungunan da ta siyo. Da gasken dai maganin infection ne amma dalilin siyo su ne dai wannan kam ita ta barwa kan ta sani.
Justice ya duba maganin ya karanta su ya ga tabbas dai maganin infection ne. Still dai sai ya ji gara ya ƙara bincike a kai. Wani ƙanin sa da su ke Uba ɗaya ya kira wanda shi Likita ne ya tambayeshi gameda infection. Bayanin da ya ma sa ya sa shi yarda da maganan Ghazala.
Washegari ya kira Zaytoonah falon sa inda a fakaice ya ma ta tambayoyi gameda infection ta amsa ma sa dai-dai abinda ta sani. Daga nan ya faÉ—a ma ta maganar Ghazala tareda nuna ma ta cewa ita É—in ma gara ta je Asibiti a duba ta. Bai yi gigin faÉ—a ma ta shawaran Ghazala ba dan shi kan sa ya ji batun Ghazalar ne ba iya aiwatarwa zai yi ba. Yaushe ma ya fara biyan bashin da Zaytoonah ta É—auka.
Ƙaramar dariya Zaytoonah ta yi bayan ta gama jin bayanan sa sannan ta ce "My Prince inaga dai..."
Shigowar Ghazala falon ya sa ta yi shiru tana bin matar da kallo. Yau dai kwanar Ghazala ne shiyasa da ta ji Suhailah na faÉ—awa Maman Tope cewa Anty Zaytoonah na falon Daddy ba shiri ta hauro saman dan ba za ta lamunci wannan shishshigin ba.
"Yawwa 'yar halak. Hajiya Ghazala yanzu na ke jin abinda ya faru a wajen My Prince"
Wani ƙululu Ghazala ta ji a cikinta jin sunan da Zaytoonah ta kira Galadima da shi. Ta tsani shegen sunan da ta kakaɓa ma sa tun dawowar sun nan. Mutum kamar Galadima ta wani zaƙe tana kiran sa My Prince kamar wani saurayi.
"Sannu ya jiki ɗin?. Ai wallahi infection mugun ciwo ne, ba ƙaramin kassara Mace ya ke ba. Allah ya yaye miki"
Ghazala ta zauna gefen Galadima tana kallon yadda Zaytoonah ke ma ta magana da shaƙiyanci.
"Kema ya kamata ki fara karɓan magani dan ance zai iya shekaru a jikin mutum ba tareda ya gane ba. Kinga idan kika magance na ki dukkan mu mun tsira"
"Ashe! Well, sorry ehn. Na gode da kulawar ki sai dai ni ba ni da wata matsala infact the last check-up da na yi na bawa My prince report É—in"
Ta kalli Justice ta ce "Love, ba na baka result ɗin da na karɓo ba?"
Galadima ya ɗan yi gyaran murya dan yanzu ya ke gano cewa akwai wata a ƙasa gameda maganar.
"To kin gani. Ba ni da komai, garau na ke, ko My prince zai shaida hakan. Tunda dai ke ce ke da symptons na infection sai a cigaba da shan magani zuwa lokacin da Allah zai kawo sauƙi"
Ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce "idan za ki ci girma ma zuwa lokacin da za ki warke sai na amshi duka girkin kin san lafiya ya fi komai..."
"Girman Uwar ki" Ta faɗa da ƙarfi.
"Ghazala" Galadima ya kira sunan ta
"Ka yi haƙuri ranka shi daɗe. Rainin hankalin yarinyar nan ne yai yawa"
"Ni fa shawara na kawo, kuma dan sati biyu zuwa uku da za ki yi ta shan maganin ai ba komai ba ne dan na rage miki aiki. Infact maganin ma zai fi yin aiki sosai"
"Riƙe shawaran ki. Da magani ko ba magani zan iya kula da My Dear"
Justice yai murmushi dan sai yanzu ya fahimci komai. Kishi kumallon Mata.
Zaytoonah ta miƙe tsaye ta ce "Allah ya ƙara lafiya Hajiya amma a dinga kula da amfani da banɗakin shago ɗin nan dan na san daga chan kika ɗebo. Allah dai ya yaye miki"
Ba dan Justice na wajen ba da Ashar za ta yiwa Zaytoonah.
Har ita za ta yiwa maganar banza, ko an gaya ma ta ƙaramin shago gareta...
***
Justice na zaune yana duba report card É—in Raziya Zaytoonah ta shigo falon da sallama.
"Raziya you barely got 40marks in Mathematics. Miye matsalar ne?"
"Daddy i tried my best amma Allah ba na ganewa"
"Extra lesson da ki ke É—auka duk a banza kenan"
"No Daddy..."
"Ke ki ka zaɓi science class and Mathematics is a core subject, but with this performance gaskiya ki ƙara ƙoƙari"
Zaytoonah ta ce "Na ga result É—in"
Justice ya miƙa ma ta ta amsa tana dubawa yayinda Raziya ta haɗe rai.
" physics 54% and Maths 40%. Kin yi ƙoƙari sosai Raziya. Ban yi Physics ba a school but Maths, i can help you with that"
"Dont bother, ina zuwa extra lesson"
"Raziya!" Ya daka ma ta tsawa
"Yi haƙuri Yallaɓai" ta faɗa tana kamo hannun sa.