← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 161

Sashe 159

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranan taron suna tun da safe aka fara shagali. Anyi wani a gidan Galadima da safe ƙarfe goma zuwa shabiyu sannan aka sake yin wani a Fada da yamma wannan karan ma har hawa aka yi dan taya Galadima haihuwar 'yan biyun sa. Washegari kuma du Hajia Abu ta haɗa wuni a gidanta.
Duk wannan shagali da akayi babu wanda Ghazala ba ta halarta ba. Da ta ji labarin haihuwar Zaytoonah. Kiran Galadima ta yi amma bai É—auka ba dan haka ta tura ma sa text na taya murna daga ba ya ya dawo ma ta da reply É—in 'Amin na gode'

Duk wani shige da fice da ta ke yi a wajen taron sunan ƙoƙarin ta na son samun Alfarmar Hajia Abu ne. Ta sani indai Hajia Abu ta yafe ma ta to tanada 80% chance na komawa gidan Galadima, sai dai abinda ba ta sani ba shine Hajia Abu kaifi ɗaya ce, idan har ta riga ta yi magana to da wuya ta chanja.

Bayan shagalin suna Galadima ya koma Abuja ya bar Zaytoonah a Zaria tana samun kulawa. Sai da Ghazala ta dai-dai ci Galadima ya kusa dawowa ta kai ma sa ziyara gida wai ta je gaishe da yaran sa. Raziya kam ko kallo ba ta isheta ba ta wuce É—akin su ta barta a falon tareda sauran. Suma É—in de ba su wani sake jiki da ita ba tunda sun É—anÉ—ani muguntar ta.

Sanda Galadima ya dawo ya ganta a gidan sa mamaki ne ya bayyana a fiskar sa ya dai yi saurin saita kan sa suka gaisa a mutunce. Zai wuce sama ta ce da shi wai wajen sa ta zo.
Bai amsa ma ta ba ya haura sama ya barta da dake baki.

Kusan awa É—aya kafin ya sauko bayan yayi wanka ya chanja kaya. Ya sha mamaki da ya sauko ya tarar da Ghazala ba ta tafi ba.
Zama yai a kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

"Ina jin ki"

A tunanin ta zai cewa su Suhailah su ba su waje amma bai yi magana ba.

Duk da ta san hankalin su na kan kallon da su ke amma yaran zamani sai a hankali.

Ganin shirun ba zai ƙwace ta ba ya sa ta kallon Falaq ta ce a hankali "Falaq ke da ƙannen ki ku ɗan bamu waje za mu yi magana"

Falaq ta kalli Ghazala sannan ta kalli Galadima wanda ke faman latsa waya.

"Hashir, Hadid, Suhailah let's go upstairs"

Yaran su ka miƙe suna ƙunƙuni.

Bayan yaran sun bar wajen ne Ghazala ta fara magana
"Ranka shi daɗe na sake dawowa ne da ƙoƙon bara ta. Wallahi na ma ka alƙawarin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ka rufa min asiri ka maida ni dan Allah"

Bai san da wani yare zai wa Ghazala bayani ta gane zaman su ya ƙare ba.
"Indai akan wannan maganar ne kar ki sake nema na. Ki ƙaddara wa kan ki cewa iya zaman da Allah ya rubuta tsakanin mu kenan"

Miƙewa yai ya fice daga gidan dan ya wuce masallaci, tsayawa dogon magana da ita ɓata lokaci ne kawai.

Auren ta da Galadima ya kawo ma ta wani daraja na daban a wajen mutane. Da sunan Matar sa ta samu shiga wajaje dayawa cikin 'yan shekaru biyu da burbuÉ—i da su ka yi tare.

Dama ne Allah ya ba ta a sama amma ta yi wasa da shi. May be ta rasa Galadima kenan har abada.

Zuwa Zaria da su ka yi Zaytoonah ta ji labarin zuwan Ghazala gidan su a bakin yara.
Da dare da Galadima ya dawo zai ci abinci ya lura da wani kumbura fiska da Zaytoonah ke yi ya tambayi ko lafiya.

"Ashe dai manyan baƙi aka yi a gidan"

Bai É—auka gidan sa na Abuja ta ke nufi ba shiyasa ya ce "suwaye su ka zo?"

"Ko da ya ke ma ai 'yan gida ne ma, tunda ai da ba a basu lasisin shiga ba ba za su shiga ba"

Galadima ya tsaya yana kallon ikon Rabbi a wajen chubby wife É—in sa.

Ganin bai tanka ma ta ba ya sa ta cigaba "ba ni da hurumin hanaka dawo da ita amma ka sani ba za mu zauna gida É—aya ba. Infact ka barta a chan Abuja zan zauna a nan kusa da Iyaye na"

Sai a lokacin ya gane maganar zuwan Ghazala ne ya jawo wannan haÉ—a ran.

"DaÉ—ina da ke saurin karaya, yanzu har kin sallama ma ta mijin ki kenan?"

"To ai kai É—in ne, kuma sai ka bari ta zo gidan ka, kuma ma..."

"Zaytoon aure na da Ghazala ya ƙare Insha Allah"
Ya katse ta

"Ba dan komai ba sai dan bana son zaman zargi. Idan na maida ta ba zan taɓa yarda da ita kaman yadda ya dace ba, wannan kuma ba zama ne da ya dace da ma'aurata ba"

"Ni dama fa kawai..."

"Ki na son mijin ki ke É—aya ko?"

"Ni ban ce ba"

"Kenan kin yarda na ƙaro mi ki ƙanwa?"

Zaytoonah ta haɗa rai ta fara mita " ai dama ku ma su sarautan nan ba kwa taɓa zama da Mace ɗaya. Daɗin ta ma bani da lokacin kowacce shegiya, hidimar gaba na ya ishe ni..."

Manna ma ta light kiss yai abaki sannan ya ce " ba ni da ra'ayin ajiye mace sama da ɗaya. Ƙaddara ce ta sa na auri Ghazala bayan ke. Ki yi addu'ar Allah ya bar mu tare har ƙarshen rayuwar mu. Amma idan wani ƙaddaran ta ratsa sai dai..."

Ta rufe ma sa baki da na ta.
Lokacin da ta janye bakin ta hannun ta duka biyu ta tallafo fiskar Galadima ta ce "Insha Allah babu ƙaddaran da zai sa ka ƙaro wata mace gidan nan. Ni kaɗai zan tanadi Tsoho na" ta ƙarisa maganar ta manna mi shi peck a goshi.

Wannan karan hannunta ta sa ta fara bashi abincin a baki...

Da maganar zargi Muhsina ta wuni ta kwana a gidan ta.
AbdulHameed tunda ya fita office bai dawo ba, ta yi ta kiran numbar sa amma switched off. Ba abinda ya fara yawo a ranta irin yana chan yana tareda wata karuwar ce.
Da safe cewa ta yi indai bai dawo ba zuwa ƙarfe goma shabiyu na rana tattara kayanta za ta yi ta tafi domin ba za ta iya ba. Dama dai zaman na su har yanzu babu wani armashi. Ranan da yai ƙoƙarin kusantar ta shi kaɗai yai kiɗan sa ya kuma taka rawan sa, wannan ya sa ya haƙura bai sake neman ta ba.

Da safen zuwa ƙarfe shaɗaya wani abokin sa ya kirata akan ta zo ta same shi a Asibiti. Tsoro ne ya kamata, ta tambayeshi mi ya ke faruwa amma ya ce ba komai.

Lokacin da ta isa Asibitin ne ta haÉ—u da Saminu wanda ya sanar da ita abinda ya ke faruwa.
Daga office ɗin su AbdulHameed ne aka kira su akan Ogan sa ya rasu a Mangu, Jos. Da ke dama tunda ya fara jinya ya koma wajen 'yan uwan sa da zama. Kusan mutum huɗu su ka tafi ta'aziyar ciki kuwa harda AbdulHameed sai dai shi da dare ya mu su a chan Jos ɗin cewa yai ba zai kwana ba, ƙarfe tara na dare ya biyo motar haya zuwa Abuja. A hanyar su ta dawowa kuwa motar su ta yi hatsari cikin motar kuwa su biyu ne ba su mutu ba da shi da wani Tsoho.
ID card na shi da aka samu ne aka tuntuɓi wajen aikin su shine yau da safe aka je aka ɗauko shi a Asibitin da ke Akwanga saboda bai wani ji rauni sosai ba.
Muhsinah na jin bayanin Saminu ta fara hawaye.
"Yana ina?"
"Yana barci kuma Likita ya ce kada a dameshi. Amma mu je ki gan shi"
Muhsinah ta bi bayan Saminu da sauri.
Ciwo ne ya ji a kafaÉ—a da kuma goshi sai glass da ya yanka ma sa gefen kumatu shima an É—inka an rufe da bandage.
Muhsinah ta zuba ma sa ido tana ƙara godewa Allah da ya kuɓutar ma ta da Miji. Take ta ɗau alƙawarin kula da shi even if it pains idan ta tuna da abinda ya ma ta a baya.

***

Ahil da Amir na sati biyar Zaytoonah ta koma Abuja da zama. Abin mamaki Hajia Abu ne ta kawo ma ta wata tsohuwa irin hadiman Fadan nan wacce za ta dinga yiwa yara wanka da kula da yaran idan sun je chan.
Zaytoonah ta ji daÉ—in zaman matar dan gaskiya ba laifi matar na da tsafta kuma tsohuwa ce mai mutunci ba irin yarjalallun tsofi ma su haÉ—a guri ba da fitina ba.

Duk da Daddy ba a faculty É—in ya ke ba amma matsayin sa na lecturer a ABU kuma mijin Maryam Nkiru Uzodinma ya sa ya tsaya tsayin daka a wajen da Mommy ke defending thesis É—in ta. Duk abubuwan da yai ta faruwa da iyalin ta ya sa ba ta gama thesis É—in da wuri ba.
Amma finally ta gama komai and she successfully defended her Phd.

T J ne ya je ya riƙo hannun ta ya ma ta jagora su ka fito daga hall ɗin. Ta yi ƙoƙari, ta burge mutane da dama a wajen.
Finally she's now Dr Maryam Nkiru Uzodinma (Mrs Dr Tijjani Abubakar).

Ranan Jummu'a kuwa T J ya shiryawa Maryam da Salman ƙaramar walima a gida saboda murnan kammala karatun su. Mommy Phd shi kuma Salman Bsc.
Humairah ta zo, tana nan da ƙaramin cikin ta da ya ɗan fara fitowa.
Zaytoonah ma ta zo weekend dan haka da ita aka yi komai, harda cewa wai itama dole a mata na ta dan sanda ta gama karatu ai Mommy ba ta ma ta walima ba.
Daddy ya ce kar ta damu idan Humairah ta gama na ta karatun zai haÉ—a yai mu su na su.

***

*Bayan shekaru biyu*
Chapter 159 · 0% Book details