Sashe 113
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gurguje ta shirya bayan ta fito daga wanka dan ta ji sanda ya shigo É—akin. Doguwar riga ta saka kalar brown irin É—inkin jallabiyar maza amma gajeran hannu gareta. Irin su ta ke sawa tayi zaman gida da shi. Auwal ne ya É—inka ma ta irin su har kusan kala shida kwanakin baya tun ma ba ta haÉ—u da Justice ba balle har ayi zancen auren su.
Har za ta fita a haka sai ta fasa ta nemo ƙaramin hijab ta saka akai sannan ta fita.
Ganin ba ya falo ya sa ta fita ta je ta É—auko ma sa kwaÉ—on zogale da kuma juice É—in kankana da abarba da ta haÉ—a. Ta ajiye a center table ta zauna tana zaman jiran sa.
Kusan minti goma sai gashi ya fito.
Hankalin ta na kan TV ma ba ta ga fitowar sa ba sai da ya ce " Ke da gidan ki sai ki tsaya a nan"
Murmushi ta yi ta ce " an dawo lafiya"
"Lafiya Princess"
Ta yi saurin É—ago ido tana kallon sa. Ya É—aga ma ta gira.
"Fatan yaran duk suna lafiya"
"Lafiya lau, suna chan suna jiran sabuwar Maman su"
Ta zuba ma sa juice ɗin a kofi ta miƙa ma sa, ya amsa tareda yi ma ta godiya.
Ta buÉ—e bowl É—in ta É—au spoon ta É—ebo kwaÉ—on zogalen kusan fiye da rabi ta zuba ma sa a plate ta tura gaban sa.
Tana ɗan satan kallon sa lokaci zuwa lokaci tana ganin yadda ya ke cin zogalen a hankali. Ya ma ta tayi amma ta ce ba za ta ci ba. Ita tun da ya tafi ma zazzaɓi ne ya riƙe ta, jiya da yau ne ma ta ji dama-dama.
Bayan ya gama ci ne ya shiga É—akin sa ya É—auro alwala amma kafin ya fito ta riga ta tattare wajen ta maida su kitchen.
Justice bai dawo ba sai bayan sallar Isha. Da ya zo ya samu Zaytoonah tana falo tana kallo.
Ta tambayeshi ko ta kai ma sa abinci falon sa amma ya ce ta bari zai ci a dining É—in. Ya haura sama zuwa minti goma sai gashi ya sauko.
Lokacin da ya zauna ta yi serving É—in sa sannan ta yi serving kan ta. Ta ajiye ma sa sokali ko zai ci tuwon da shi amma sai ta ga ya É—auraya hannu ya fara ci da hannu.
Dukkan su shiru su ka yi sai ƙaran sokalin da Zaytoonah ke amfani da shi wajen cin abinci.
Tun loman farko yai suspecting girkin Amarya ne wannan sai dai bai tabbatar ba sai bayan ya ƙara loma uku. Yau da gobe ya saba da irin girkin Baba Nafy shiyasa ya gano miyar nan ba irin miyar ta ba ne. No offense amma miyar egusin nan ya fi wanda ya saba ci daɗi.
"Ya ba ki É—auko min yara na ba?"
"Erm...Mommy ta ce sai sun ƙare ajin da su ke yanzu sai na ɗauke su"
"Anya zan iya haƙuri zuwa lokacin nan kuwa" yai maganar yana miƙa ma ta bowl ɗin miya.
Ta amsa ta ƙara zuba ma sa wani miyar tareda tambayar sa ko ya isa haka.
Ya gyaÉ—a ma ta kai.
"Zan dai fi so a nema mu su transfer zuwa chan Abuja tun yanzu, zuwa su gama term har biyu yayi yawa"
Shiru ta yi ba ta amsa ma sa ba dan ta san da wuya Mommy ta yarda tunda cewa ta yi gara ta je ta saba da yaran Justice kafin na ta 'ya'yan su zo, idan har ta tafi da 'yan biyu yanzu ba za ta bawa yaran Justice kulawar da ya kamata ba.
"Adaeze" ya faÉ—a da wata sassanyar murya, sunan ya fiÉ—o raÉ—au kamar yadda Daddy ke kiran ta da shi.
"Ki yiwa Mommy magana ta bar mana yaran kin ji"
GyaÉ—a ma sa kai kawai ta yi ta cigaba da cin abinci...
***
Ranan Lahdi da safe su ka wuce Abuja. Da daren Asabat ta je yiwa su Mommy sallama kuma sai a lokacin ne yaran nata su ka tada daru akan za su bi ta, da ƙyar ta lallaɓasu akan da zaran ta kwana biyu za ta zo ta ɗauke su.
Suna daf da shiga garin Abuja wayar Zaytoonah ya fara ringing wanda ya tasheta daga É—an baccin da ta fara a motar.
International number ta gani amma ba ta gane call code ɗin wani ƙasa ba ne. Ta dai ɗauka dan tana tunanin ko wani investor ɗin su ne.
"Happy married life sweetheart" muryan Farha ya doki kunnen ta.
"Farha?" Ta faɗa da mamaki dan maganar su na ƙarshe da ita lokacin da ta kirata tana gaya ma ta aurenta da Justice ya kusa kuma tana tsoro, ita kuma Farhan ta ba ta shawaran akan idan har ba ta so to kar ta takura kan ta.
"Fatan ban katse miki honeymoon É—in ku ba?"
Sai da ta kalli Justice wanda hankalin sa ke kan wani magazine da ya ke karantawa kafin ta ce "Farha ba na son gulma kina ina?"
"Taiwan"
"Mi ki ka je yi?"
"Neman better half É—ina. An gaya min my perfect man É—an Asia ne"
"Allah ya shiryeki Farha, ki zo Africa na sama miki miji dai dai da ke" ta yi maganar tana dariya.
Itama Farhan dariya ta yi kafin daga baya ta ce "Are you happy with him?"
Ta saci kallon Justice kafin ta furta a hankali "i'm happy"...
Abinda ya faru daren ranan da ya dawo ne ya zo ma ta. May be ba ta ma sa adalci ba amma gaskiya tana buƙatan lokaci, har yanzu ba ta gama amincewa da zuciyarta za ta iya mu'amalar aure da Justice ba.
Daren Jummu'ah bayan sun gama cin abinci ta tattare wajen ta koma ɗaki. Da ke akwai saƙon da za ta tura ta email sai ta buɗe laptop ɗin ta tana composing mail ɗin. Sai ga kiran Justice a wayar ta.
"Idan ba matsala ki zo ki tayani hira"
Ita ba yarinya ba ne ta san mi ya ke nufi da hakan. Ta san hakkin sa ne amma gaskiya she's not ready for it.
Bayan ta gama jujjuya zancen a ran ta kafin ta ɗau waya ta tura ma sa saƙo kamar haka.
*Daddyn Raziya ka yi haƙuri ka bani lokaci na ɗan huta har yanzu ban gama warware gajiya ba*
Sai da saƙon ya tafi da kusan minti goma kafin reply ya shigo wayar ta
*kar ki damu Princess, ko hutun shekara za ki É—auka ni ba mai takura miki ba ne. Ina fata dai mu fahimci juna kafin koma minene zai shiga tsakanin mu. Mu kwana lafiya*
Ta karanta saƙon ya kai so goma kowanni lokaci kuma da abinda zuciyarta ke riya ma ta. Sai da ta ji kaman ta tashi ta je ta same shi amma wata zuciyar ta ce tunda ya fahimceta gara kawai ta bari ɗin...
Bayan Azahar su ka isa gidan. Justice ne ya jagoranceta har É—akin da aka ware domin ta É—akin bai kai na gidan sa na Zaria girma ba amma shima ba laifi Babba ne. Wannan gidan siya yai , shi kuma na Zaria shi ya gina, komai na gidan ya tafi bisa tsarin sa ne.
Iya falo Dreba ya shigo ma ta da kayanta yayinda mai aiki ta dinga ɗauka tana ƙarasa ma ta da shi ɗaki. Maimakon Baaba Nafy da ta ke da fara'a wannan ko kaɗan ba ta sake fiska wa Zaytoonah ba. Gaisuwar da ta ma ta ma kaman na dole ne. Ko ajikin Zaytoonah dan ba wannan ne a gaban ta ba.
Da yamma Zaytoonah ta shiga kitchen dan ta yi girki dan tun da ta karɓi girki a wajen Baba Nafy har su ka taho ita ke yiwa Justice girki sai dai kawai Baba Nafyn ta tayata da ƙananun ayyuka.
Kalmar farko da matar ta faÉ—a ya sa Zaytoonah yi ma ta kallon are you mad?.
"Yallaɓai bai ce na ba ki girki ba" abinda matar ta faɗa kenan tana magana tana tsume fiska.
Zaytoonah ta juya maganar a ranta wanda yai ma ta banbaraƙwai.
Ta zo da niyyar bin kowa a hankali ne amma idan hakan bai yiwu ba za ayi zama 'yar zafi-zafi ne.
"Ban gane ba" ta faɗa dan ta tabbatar lafiyar matar ƙalau ko kuma dai iskanci ne.
"Mu biyu mu ke aikin girki a gidan nan, idan na yi na kwana shabiyar sai Maman Tofe (Tope) ta karɓeni. Yallaɓai bai ce mu bari Amarya ta yi girki ba"
Dariya ya tahowa Zaytoonah amma ta dake ta ce " ki je ki cewa Yallaɓan ni Zaytoonah daga yau zan dinga yi ma sa girki"
Yadda ta yi maganar ya sa Matar ta yi gum da bakin ta dan ba ta ga alamar wasa a fiskan Zaytoonan ba.
Komawa gefe ta yi ta tsaya tana kallon Zaytoonah.
Zaytoonah ta je ta buÉ—e fridge dan ta ga abinda akwai a gidan ta san mi za ta shirya. ÆŠan zaman su da Baaba Nafy ta gaya ma ta duk favourites É—in Justice.
"Ina ne store?" Zaytoonah ta tambaya ba tareda ta kalli inda matar ta ke ba.
"Ga ƙofar nan" ta faɗa dan dole...
Da yamma lis sai ga yaran sun shigo gidan sanye da kayan Islamiyya. Falaq da Suhailah ne su ka ruga kitchen da gudu bayan Justice da ke falo ya gaya mu su Antyn su na kitchen.
Sun ga hotunan biki dan haka gani ɗaya su ka yiwa Zaytoonah su ka gane ta. Suhailah ne ta je ta rungumeta yayinda Falaq ta tsaya daga gefe tana ƙare ma ta kallo.
"Anty ina su Hashir da Hadid?"
"Suna Zaria Suhailah"
"Yaushe za su zo"
"Ashe dai 'yan biyun nawa dai suna da babbar ƙawa"
Suhailah ta yi dariya.
"Falaq ko?"
Falaq ta gyaÉ—a kai tareda barin kitchen É—in da gudu saura kaÉ—an ta buge Raziya da ke shirin shigowa.
Lokacin da Raziya ta shiga kitchen É—in ta samu Zaytoonah na yiwa Suhailah bayanin abinda ta girka mu su yayinda yarinyar ke irgo ma ta abinda kowa ya fi so a cikin su.
"Raziya ya karatu?" Zaytoonah ta tambaya fiskarta É—auke da murmushi amma ga mamakin ta sai harara Raziya ta bi ta da shi.