← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 161

Sashe 95

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ya shiga É—akin. Sai dai babu kowa sai Zaytoonah da ke kwance tana bacci. Tsayawa yai a gefen gadon yana kallon yadda ta ke bacci so peacefully. Ya É—an zauna gefen gadon ya kai hannu ya shafa goshin ta. Duk da ta nuna rashin amincewarta bisa wannan aure da su ke shirin yi, baya tunanin zai janye. As selfish as it sounds, yana son auren Zaytoonah now more than ever.

Shafa kumatunta daya farayi a hankali ne ya farkar da Zaytoonah inda ta miƙe a zabure tana ihu.

"Ni ne" ya faɗa a ƙoƙarin sa na son kwantar ma ta da hankali amma jikinta kakkarwa ya ke tana furta sunan Zuhayr.

Ba shi da hurumin yin hakan amma zuciyar sa ce ta tunkuÉ—ashi bisa aiwatar da hakan. Jawo Zaytoonah yai jikin sa ya haÉ—e bakin su yana tsotsa a hankali, for a while Zaytoonah ta yi shiru amma duk wani tunanin ta Zuhayr ne a gabanta dan haka ta shiga maidawa Justice martanin kiss É—in sosai.

Mommy da ke Alwala a banÉ—akin da ke cikin É—akin, ihun Zaytoonah ya sa ta fito ba shiri sai dai turus ta tsaya lokacin da idon ta ya ga abinda ya ke faruwa a É—akin. Saurin komawa ta yi banÉ—akin tana faÉ—in "Allah kai ne masanin gaibu ka tabbatar da alkhairi a cikin wannan haÉ—in"

Lokacin da Justice ya janye bakin sa daga na Zaytoonah lumshe ido ta yi ta faɗa jikinsa haɗe da ƙanƙameshi tana faɗin "D dama na san za ka zo, na san ba za ka bari Ben ya kashe ni ba"
2/11/21, 10:04 PM - ****: 45

Bismillahir Rahmanir Rahim

*i'll stand by you*

"Zauna" ya faÉ—a kamar ba da ita ya ke ba.

Zaytoonah ta É—an É—okanu a kujeran tana tsuke fiska.

Sai da ya gama rubuce-rubucen da ya ke kafin ya É—aga kai yana kallon ta.
Ƙaramin Gyalen da ta yane kan ta da shi ya ɗan yi baya har kana ganin farkon gashin ta.

Waya ta ke dannawa dan haka ba ta san ma yana kallon ta ba. Daga baya jikin ta ya ba ta kamar ana kallon ta dan haka ta É—ago kai, nan kuwa ta sauke idon ta cikin na Justice. Maimakon yai magana sai ya sa hannu ya shafa goshin sa zuwa kan sa.
Ganin kamar goshin ta ya ke kallo ya sa tayi saurin jawo gyalenta ya rufe gashin sosai.

Wani file ya miƙa ma ta ya ce " zan baki case ɗin nan ne saboda ina so ki nuna ƙwazon ki a matsayin ki na wacce ta yi karatun Law. A Kaduna za'ayi shari'ar kuma duk abinda kike buƙata yana cikin file ɗin nan. Za ki iya ganawa da mutumin da za ki wakilta. Zan kuma haɗa ki da Barr. Batula, za ta ƙara taimaka miki wajen ganin komai ya tafi dai-dai.

"Ina ga, daga yau sai kin gama wancan case É—in nan kafin ki dawo nan. Kafin ina miki fatan Alkhairi"

Sai da ta sauke numfashi kafin ta É—auki file É—in ta fara dubawa. A É—an dubawa da ta yi na É—an mintuna biyu zuwa uku ta gano case É—in akan rikicin fili ne.

"Na gode Sir, Insha Allahu zan samu nasara a wannan case É—in"

Har ta miƙe ta kai ƙofa bai ce komai ba, sai da ta da hannu ta buɗe ƙofan ta tsinkayi muryan sa yana faɗin " za ki iya kirana a duk lokacin da ki ke da tambaya"...

Sati biyar ta yi ƙarƙashin kulawar Justice, kuma gaskiya zaman ta a chamber ɗin sa ba ƙaramin horuwa ta yi ba. Sati biyu da ta yi bayan dawowan ta daga Ringim ta yi su ne duka a ƙarƙashin Justice, kusan kullum ma a office ɗin sa take sai dai idan yana da baƙo, idan kuwa baya nan haka zai zaunar da ita da litattafai da articles ya ce ta dinga karantawa. Tambayoyi kuwa tana shan su kamar ba gobe, ba shi da takamaimai lokacin da ya ke tambaya duk lokacin da ya ga dama ya ke jehowa.

Kwanan ta biyar a Zaria ta wuce Kaduna. Ta haɗu da Barr. Batula da kuma client ɗin ta kuma tana da yaƙinin case ɗin zai zo ma ta da sauƙi, haka ma Mommy ta ce ma ta.

"Ke wacce irin daƙiƙiya ce? Ba ki yi karatu ba ne ko ba shirya ba ne?. Ko da ace court attachment ki ke bai kamata ace kina wannan irin kuskuren ba, balle ke certified Barrister ce. Anya ma ba da kuɗi ki ka haye jarrabawan Law School ba?"

Maganganun Barr. Batula kenan lokacin da su ka shiga office É—in ta bayan sun dawo daga kotu.
Zaytoonah ta sunkuyar da kan ta ƙasa tana sauraron wannan cin mutuncin. Ba fa cewa aka yi sun loosing ƙarar ba. Kawai dai an ɗaga ƙaran ne zuwa nan da sati biyu.

"This is an open and close case Wallahi. Tuni da an wuce wajen, amma kin je kina ta shirme. Wai tukunna ma wani matsayi gareki da har Galadima zai ce na bar miki case da ke hannuna?"

A harzuƙe Zaytoonah ta ɗago fiska tana faɗin " Ya ishe ki haka Barr Batula. Ba ni na kawo kai na nan ba, idan kin matso ki san mi ke tsakanina da Justice za ki iya ɗaukan waya ki kira ki tambayeshi" daga haka ta fice ma ta daga office. Duk da matar ta girmeta sosai dan aƙalla za ta kai shekaru Arba'in amma ba ta tunanin za ta iya juran wannan cin mutuncin. Dama tun kafin ma a saurari ƙaran take-taken matar ya nuna kamar ba za su jitu ba.

Tana ganin kiran Justice lokacin da ta fito amma ta share shi, ita da shi da Batulan ma haushin su take ji.
Mai kawai ta ƙarawa motar ta ta wuce Zaria.
Da ta ba wa Mommy labarin abinda ya faru a kotu Mommy ƙara ƙarfafa ma ta gwiwa ta yi tareda nuna ma ta cewa dama haka ake shari'a, ba lallai daga zaman farko a yanke hukun ci ba, ƙila sai an yi zama biyu ko uku ma duk yadda dai yanayin shari'ar ta ke da zafi.

Bayan hiran su da Mommy ne ta samu ɗan sanyi a ran ta. Auwal ma da ya zo encouraging ɗin ta ya dinga yi yana nuna ma ta ai ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba ma duba da cewa wannan ne first case na ta.

Sai da za ta kwanta ne ta ga missed calls ɗin Justice har guda biyu, ta tuna cewa ai ya kirata tun da rana ba ta ɗaga ba. Ta duba agogon wayar ta ta ga ƙarfe goma har da rabi da minti shida. Hiran da su ka tsaya yi da su Auwal ne ma ya sa itama bata kwanta da wuri ba.

Kamar ba za ta kira shi ba sai kuma ta kira É—in bayan ta tuna cewa shi É—in tuzuru ne tunda zawarci ya ke yi.

Sai da wayar ta kusa tsinkewa aka É—auka da sallama.
Shiru dukkan su suka yi bayan Zaytoonah ta amsa sallamar ta shi.

Kusan second talatin ta gitta ba wanda yai magana a cikin su ganin dai ba magana zai yi ba ya sa ta sauke fushin data ke yi ta ce "Sir an ɗaga ƙaran"

"Na sani" ya furta a sanyaye.

Sai ya dinga yin shiru, ni ban san mi zan ce ba kuma. Mutum magana ma aiki ne a wajen sa. Ta yi wannan tunanin a zuciyar ta.

"Kin yi ƙoƙari sosai" ya furta biyo bayan shirun da yai.

Ba ta ce komai ba dan ba ta da abin faÉ—a.

"Barin gaya miki wata addu'a da za ki dinga yi da zai rage miki jin tsoro"

Jin yayi maganar addu'a ya sa ta tattaro hankalin ta ta bashi, lokacin da ya fara bayanin ne ya sa ta yi saurin danna call record saboda ko ta manta zuwa gobe za ta sake sauraran sa.

Yana gama gaya ma ta addu'ar ya kashe wayar.
A ɓangaren Zaytoonah ta ce "Justice ba dai manyan ce ba"

A saman ƙirjin sa ya ajiye wayar tareda sauke dogon numfashi. A kullum da ya ke sakata cikin addu'o'in sa sabbin lamura ya ke ji a ran sa gameda ita. Maganganun Ni'ima na ranan su suke ƙara tunzura zuciyar sa wajen kwaɗayin tayin da ta ke ma sa.

"Yaya ba sai na faɗa ma ka falalar da za ka samu ba idan ka riƙe marayun yaran ta. Allah kai kan ka za ka yi alfahari da auren ta nan gaba kaɗan. Ta san ciwon maraici tunda tana da 'ya'ya marayu shiyasa na ke kyautata zaton ba za ta muzgunawa su Raziya ba. Yaya ka bani dama na yiwa Hajja magana"

Bai san dalilin sa na ajiye hoton a wayan ba, ba halin sa ba ne irin haka amma ranan kallo É—aya yai wa hoton ya saving na shi. Profile picture É—in ta ne da ta saka a whatsapp ranan wata Jummu'a. Bai san yaushe aka yi hoton ba amma a office É—in sa aka yi a kuma kan kujerar sa. Ba selfie ba ne hoton dan zama ta yi da kyau aka É—auketa, babu tantama Ahmad ne ya É—auketa. A ranan ta cire hoton daga DP É—in ta É—aura hoton wasu jarirai guda biyu, sai ya ji daÉ—in ma saving É—in hoton da yai da sauri.

Yanzu ma hoton ya kalla yana tunanin anya yarinyar nan za ta iya amincewa da shi?...

***

"Ai da Ni'ima ta kawo yarinya tuni ka amince. Wato dai ni ce ban isa na maka tayin Mata ba"

Hajiya Abu ke wannan magana tana wani cin magani, a matsayin ta na babbar Ya a wajen Galadima.
Chapter 95 · 0% Book details