← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 161

Sashe 53

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan haihuwan Lucile da shekara biyu ta fara ciwo. Bayan ciwo da ta ke yi har da rashin kwanciyar hankali saboda chanjawar da Muhammad ya fara yi ma ta. Da ta fara zuwa asibiti ne aka fara gwaje-gwaje har aka tabbatar tana da Leukemia wato cancer ta jini. A wannan jinyan da ta yi ne iyayenta su ka zo kuma su ka yafe ma ta bisa guduwa da ta yi daga gida ta auri Muhammad. Ta ɗau watanni kafin aka ce ta warke. Abubuwa dai bai yi dai-dai ba bayan jinyar da ta yi inda daga baya bayan ta kama Muhammad da wata co-worker ɗin sa a office ta nemi ya sake ta. Bai so haka ba ya dinga neman yadda zai yi ta yi haƙuri amma ta ƙi. Ta riga ta sawa ranta rabuwa za ta yi da shi dispite the fact tana son sa sosai.

Bayan sun rabu ta É—au É—an ta ta koma gidan iyayen ta inda a nan ta maida hankali wajen kula da gidan gonar su. Da farko Muhammad sai da ya É—au watanni bai nemeta ba sai daga baya ya fara zuwa duk wata sau É—aya yana ganin É—an sa har lokacin kuma yana son maida auren su da Lucile dan sai da su ka rabu ya gane ya fara son ta tsakani da Allah amma Lucile ba ta ba shi fiska ba.

Wannan ya sa yai ƙoƙarin dawowa kusa da su ya zauna a Las Vegas inda ya samu aiki da wata kamfani. Ya cigaba da ɗebe-ɗeben Matan shi amma har lokacin ba ya jin zai iya auren wata ba Lucile ba. Lokacin Zuhayr na shekara tara Leukemia ɗin Lucile ya dawo aka fara ziryan Asibiti da ita. Lokacin da jinya ya tsanan ta aka ce ba za ta wuce wata shida ba za ta mutu, wannan ya sa a karo na ƙarshe da Muhammad ya nemi su maida auren su sai ta yarda da hakan saboda har lokacin akwai soyayyar Muhammad a tattare da ita. A gidan gonan Iyayen ta su ka zauna bayan ta buƙaci hakan. Watan ta huɗu ta mutu bayan ta sha fama da cancer dan har gashinta ya fara kakkaryewa.
Mutuwar ta taɓa Muhammad matuƙa, ya yiwa kan sa karatun ta nitsu yana so ya je ya nemi iyayen sa gafara amma ya fi so ya tafi da ɗan sa Zuhayr sai dai iyayen Lucile da dama sun saba da yaron su ka ƙi fir, dan su tunanin su ma Muhammad guduwa ya ke son yi da Zuhayr. Bayan sun ƙi ya tafi da ɗan sa ne sai ya shigar da ƙara dan really yana so ya koma Nigeria ya kuma tafi da ɗan sa dan ya ma sa tarbiyyan musulunci dan yadda yaron ya taso ba abinda ya sani gameda Musulunci.

Sai dai ya shigar da ƙara amma bai yi nasara ba domin kotu iyayen Lucile su ka damƙawa Zuhayr tareda cewa zai zauna da su har shekara shatakwas kafin ya zaɓi inda ya fi ma sa ko ya zauna da su ko ya koma wajen Uban sa. Da haka Muhammad ya koma Nigeria ya bar Zuhayr a wajen kakannin sa. Da ya je Nigeria fa cikin 'yan uwan sa kowa fushi ya ke da shi dan mahaifin sa ma cewa yai ya koma inda ya fito. Abu da ɗa da uba bayan ya nemi manyan mutane sun tayashi roƙon mahaifiyan sa sai ya yafe ma sa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuma ya settling a Zaria har aka fara ƙoƙarin haɗa shi aure da wata'yar uwar sa sai dai ƙarar kwana ya zo ya hana hakan tabbatuwa, domin Muhammad hatsarin mota yai da shi da ɗan uwan sa Aliyu. Shi ya mutu amma Aliyu ya rayu raunuka kawai ya ji.

Dalilin rasuwan Muhammad ya sa daga baya Alhaji Iliyasu ya fara bibiyan jikan na sa wanda har chan wajen Iyayen Lucile ya je ya karɓi Zuhayr a lokacin hutu akan zai zo Nigeria ya ga 'yan uwan mahaifin sa. Ba su so ba amma da ya takura sai su ka je gaban hukuma ya rubuta yarjejeniya akan zai dawo da shi bayan sati huɗu. Hakan kuwa aka yi bayan sati huɗu ya dawo mu su da Zuhayr. Tundaga lokacin ya ke bibiyar jikan na sa dan ya saba da shi, lokacin da girma ya kama Alhaji Iliyasu ne ma ya rage zuwa wajen sa sai dai Ɗan sa Aliyu wanda shima daga baya aiki ya kaisa America yana zuwa wajen ɗan Yayan na sa shima kuma yana zuwa inda su ke lokaci zuwa lokaci.
Raɓuwa da 'yan uwan mahaifin sa ya sa shi fara Sallah da admitting musulunci a matsayin addinin da ya zaɓa sai dai duba da inda ya taso da mutanen da ya ke mu'amala da su addinin ba wai ya shige shi har chan ba ne...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 23

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yau ita da kanta ta ke girka abinda za ta ci. Ta yi missing girkin irin na gida Nigeria dan haka ta shiga kitchen ta fara dafa farar shinkafa da jar miya wanda ya ji nama zuƙu-zuƙu, da ke akwai albasa mai lawashi, bayan ta gama miyar sai ta kashe gas ɗin sai ta zuba albasar da ta yanka ƙanana ciki ta raugaya ta rufe, ta ɗau plate ta cika shi da shinkafa ta sa sokali sai ta ɗau wani bowl ta zuba miyan a ciki. Ta sa a ƙaramin tray ta ɗauka ta nufi ɗaki dan karatu ma take yi yunwa ya fito da ita ba kuma yunwan ba kaɗai kwaɗayin shinkafa da miya ta ji.

Tana haurawa stairs ta ci karo da su suna saukowa dukkan su suna ɗaure da towel a ƙugu.

Rintse idonta ta yi ta takure gefe guda, alamun wucewa da ta ji ne ya sa ta buÉ—e ido sai kuma ta tsinci idonta cikin na Zuhayr.

"Abincin be mi ki yawa ba?"

Ta murguÉ—a ma sa baki ta ce "to sai ka min gori kuma tunda abincin gidan ka ne"

Bai yi magana ba kawai ya cigaba da sauka.

"Kuma a daina yawo tsirara acikin gida" bai juyo ba amma yayi murmushi.
Ben da ya riga ya kai ƙasa kuma idon sa akan Zaytoonah yana aika ma ta wani mugun kallo.

Bayan ta shiga ɗaki a kan gado ta baje kolinta inda ta buɗe laptop tana kallon wani tutorial ɗin da aka mu su jiya, tanayi tana cin abinci. Ta ci kusan rabi sai ga kiran Mommy a wayanta, katse kiran ta yi dan ta san yadda MTN za su zuƙe ma ta kuɗinta cikin ƙanƙanin lokaci. Bayan ta kirata su ka fara gaisawa inda Mommy ke tambayarta ya karatu ta ce Alhamdulillah. Karatu akwai daɗi akwai kuma wahala.
"Fatan kina yiwa mijin ki biyayya?"

"Yes Mommy"

"To Allah ya miki Albarka" Zaytoonah ta amsa da amin.
Kafin ta kashe wayar sai da ta tambayeta ko akwai matsala ta ce ma ta babu.
Duk da hoton da Zaytoonah ta tura mu su recently ya nuna tana cikin jin daɗi saboda ƙiba da ta ƙara gashi tayi wani fresh da ita, skin ɗin ta na glowing. Amma kuma hakan bai hana Maryam fargaba ba a koda yaushe gani take kamar ba ta yiwa Zaytoonah adalci ba, aurar da ita da ta yi da wuri haka, ga kuma mutumin da ba ta taɓa haɗuwa da shi face to face ba sai da ta je gidan shi. Addu'arta a kullum Allah ya daidaita tsakanin su.

Ben da Zuhayr wajen swimming pool su ka je da ke ta bayan gidan inda su ka cire towel É—in jikin su ya saura boxers kaÉ—ai su ka faÉ—a cikin ruwa. Sun kai 30mins aciki suna wasa kafin su ka fito suka goge jikin su da towel su ka zauna a rumfar da ke gefen swimming pool inda tuni Chef Green ya jera mu su desert da drinks a wajen.

"Ina tsoro" Ben ya faÉ—a yana kallon Zuhayr da ke kwance yana karatu.

Zuhayr ya saukar da littafin ya kalli Ben ya ce "tsoron me?"

"Ina tsoron kar ka faÉ—a soyayyar yarinyar nan, na ga ka fara damuwa da ita sosai"

Zuhayr ya ce "ba zai faru ba. Na riga na gama soyayya a rayuwata. Kar ka manta yarinya ce"

Ben ya girgiza kai amma cikin zuciyar sa yana wasi-wasi. Tun da su ka dawo daga gidan Kakannin Zuhayr ya ke lura da shi gameda wasu changes da ya ke gani gameda Zuhayr ɗin. Kamar idan baya gari zai kira shi sau ɗaya ko sau biyu ya tambayeshi lafiyar Zaytoonah, idan kuma yana nan idan bai ji motsinta a gidan ba kuma ya san ba ta je class ba zai leƙa ɗakin ta ya tambayeta ko lafiya.

***

Yau ta ke jummu'a kuma saura kwana goma shabiyu su Zaytoonah su fara jarrabawa.
Ta yi wanka ta fito ta shafa mai ta ɗauko wani gown ɗinta na Atamfa wanda daga gida ta zo da shi. Rigan da ya ke ma ta ruwa da sai gashi yau da ƙyar ta saka shi. Wajen zuge zip kuwa yana kaiwa tsakiya ya ƙi motsawa, tayi-tayi ya ƙarisa zugewa ya ƙi. Ta kalli kan ta a madubi tana ɗan jujjuyawa.

"Ya Allah Zaytoonah ba dai ƙiba na ƙara ba?"

Daga jikin ƙofa ya ke tsaye yana kallon ta tun lokacin da ta ke struggling ɗin buɗe zip ya shigo amma ba ta ganshi ba shima kuma bai ƙarisa wajen ta ba.

Ganin dai Zif ɗin ba zai zugu ba sai ta fara ƙoƙarin cire kayan.

"Ehm Ehm" ta ji gyaran murya a bayanta dan haka ta juyo da sauri.

"Indai kika cigaba da cin junk food duk wata sai kin chanja wardrobe"

"Ina ruwan ka"

Ƙarisowa yai wajen gado ya ajiye ma ta wata leda ya ce kayan da za ta sa gobe kenan saboda suna da party a company.
Ya ƙara da cewa "na gwada size ɗin ki ne da ɗaga daga cikin kayan ki. Amma ki je ki gwada kar ya zama kayan zai miki kaɗan"

"To zage ni, ka ce kawai ƙibana ya tsole ma ka ido abinda ko da kuɗi ba za ka iya samu ba" ta ƙarisa maganar tana jujjuya ido.
Chapter 53 · 0% Book details