Sashe 23
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ɓarin Hajjo da wata biyar ta sake samun ciki, a lokacin ne kuma Maryam ta fara tsorata ko dai ita ce ba ta haihuwa tunda gashi Hajjo ta samu ciki har sau biyu. Ta je Asibiti aka ma ta duk wasu gwaje gwajen daya kamata aka ce lafiyarta ƙalau za ta iya samun ciki kowani lokaci.
Hajjo kam banda laulayi har da iskanci, ta dinga tsirface tsirface dan taga T J ya ɗan damu da ita saboda cikin jikinta. Gaba ɗaya sai girki ya koma hannun Maryam da rana girkinta da na Hajjo duk ita ke girki. Hakan bai dameta ba dan girki a wajenta ba abun ɗaga hankali ba ne. Sai da Hajjon ta fara iskancin sai dai a dafa ma ta kaza ko kuma sai Maryam ta gama girki ta ce ba za ta ci ba ita kaza da kaza ta ka so sannan Maryam ta fara yiwa T J ƙorafi. Da farko T J ya fara biye ma ta saboda laluran ma su ciki amma daga baya da ya gane harda iskanci a lamarin na ta sai ya taka ma ta birki.
A hankali dai ciki ya girma Hajjo ta haifi ɗanta namiji. Zo ka ga murna a wajen ta ganin yanzu kam za ta karɓi gida tunda ita ta fara haihuwa ga shi ɗa namiji.
A Zariyan a ka yi suna kuma 'yan uwan sa na Ringim sun zo dayawa. Yaro ya ci sunan Baffah wato Abubakar suna kiran sa Sadiq.
Tun watan farkon Sadiq ya fara rashin lafiya. Yau suna asibiti gobe su na gida. Na da nan Hajjo ta tada Hankali wai Maryam ce Mayya ta kama mata ɗa. Ita da Inna da ta zo mata wanka su ka kama Maryam da zagi da faɗa. Har Inna Saratu ta je ta nemo tafarnuwa su ka fara sakawa a duk gidan. Da Maryam ta shigo kuwa za su fara jifanta da Tafarnuwa. Ba ta taɓa gayawa T J ba dan ba ta son tashin hankali.
Ranan da ciwon Sadiq ya tashi aka kaishi babban Asibiti nan Inna Saratu ta wuce gida wai za ta zo da sarkin mayu.
A asibitin bayan anyi gwaje-gwaje ne aka tabbatar wa T J da cewa Sadiq SS ne wato sickler. Nan aka gwada jinin sa da na Hajjo aka tabbatar dukkan su genotype É—in su AS ne. Wannan ya sa washegari ya taho da Maryam aka gwada ta amma ita AA ce nan hankalinsa ya kwanta.
Da yamma yana Asibiti saboda ana ƙarawa Sadiq jini sai ga maƙocinsa Mr Badmus wato Baban Lucas. Ya ce maza-maza ya zo gida ba lafiya. Da ya tambayeshi miyake faruwa sai ya ce wai wasu tsofi ne su ka taho da Sarkin Mayu gidan sa an ɗaure Maryam ana dukanta wai sai ta sake kuruwan Sadiq. Jiki na rawa haka ya bi Mr Badmus hankali tashe duk da kuwa Mr Badmus ɗin ya ce ma sa an tafi da Maryam Asibitin cikin makaranta shi kuma Sarkin Mayu an kira ma sa security yanzu ma ana maganar za a wuce dashi police station ne.
Asibiti su ka wuce inda su ka samu an sallami Maryam É—in, dama ciwukan da dorinar Sarkin mayu ya ji ma ta ne aka treating.
Gidan Mr Badmus su ka wuce tunda matar sa ce ta kai Maryam É—in Asibiti. Su na shiga Maman Lucas ta nuna ma sa É—akin da Maryam É—in ta ke.
Yana shiga ya ganta zaune a kan gado. Ya ƙariso da sauri ya hau gadon ya kamo hannun ta.
"I'm sorry Dear, i'm very sorry, ya jikin na ki? Are you Ok? " ya shiga kissing É—in hannuta
"Divorce me" ta furta hawaye na bin kumatunta
Girgiza kai ya farayi yana hawaye.
"Mahaifiyar ka ta tsaneni, she'll keep coming between us. Lets just go our separate ways"
"Nooo, Nooo. Dear ba zan iya rabuwa da ke ba. You are my world, you are my happiness"
"Barkindo ba zan iya cigaba da zama da kai ba, ka sake ni kawai, for Peace sake lets go our separate ways b..."
Haɗe bakin su yai ya shiga kissing ɗinta da sauri sauri. Da ƙyar ta samu ta ƙwace bakinta daga zazzafar kiss da ya ke ma ta.
Tana hawaye shima yana yi haka su ka ƙurawa juna ido suna maida numfashi.
Da ƙyar T J ya ce " Maryam Dan Allah kiyi haƙuri, ba zan iya rabuwa da ke ba. Please..."
"Idan saboda maganar Baffah ne kar ka damu ai bai ce idan na nemi saki kar ka bani ba. Ba wai dan Iya ta ce ka sake ni ba, nine na ke so ka sakeni. I want peace Barkindo i want peace" ta ƙarisa maganar da ƙarfi.
Ba abinda ya ke cewa sai Sorry...
***
Kwana shida kenan da faruwan wannan abu, Iya da Inna da su ka taho da Sarkin Mayu kam suma kaɗan ya rage a rufe su sai da T J ya shiga ya fita kafin aka rufe case ɗin. Da kan sa ya je Ringim ya samu Alhaji Isa ya ma sa bayanin duk abinda ya faru da ma abin da ke damun Sadiq ɗin. Alhaji Isa shima ya kaɗu da maganar, bai taɓa tsammanin rashin hankalin Iya ya kai har haka ba.
Goggo kam sai da ta yi hawaye saboda tausayin Maryam. Tana ina ma Baffah na raye.
Meeting mai zafi Alhaji Isa ya kira wanda ya haɗa da Iya, Inna Saratu da ma Hajjo wacce an sallame su saboda Sadiq ya ji sauƙi. Ya kira Maryam ma amma ba ta zo ba saboda exams da su ka fara har lokacin gidan Mr Badmus ta ke kwana ta ƙi komawa gidan T J. Yayi kukan yayi magiyan ta ƙi sauraron sa.
Sosai Alhaji Isa ya jawa Iya da su Hajjo kunne akan Maryam. Yai Allah wadai da halin su da ɓatawa Gidan Modibbo suna ta hanyar zuwa ɗauko wani Boka wai Sarkin Mayu. Ya haɗa da cewa dukkan su suje su bawa Maryam haƙuri.
Shi T J ya so a raba auren sa da Hajjo ne ma musamman saboda yadda dukkan su suka kasance AS that is akwai probability za su yi ta haihuwan SS amma Alhaji Isa ya ce a'a tunda har sun samu rabo ya cigaba da haƙuri kawai. Duk bayanin daya ma sa akan rashin compatibility na su da Hajjo bai gane sosai ba haƙuri kawai ya bashi akan ya cigaba da zama da ita su yi jinyar ɗan su.
A wajen kuwa Alhaji ya ce da Iya da Inna bai yarda ko É—aya ta sake zuwa gidan T J ba idan suna son ganin su su bari sai sun zo Ringim. Idan da matsala za a aika wasu cikin 'yan uwa su je mu su.
Bayan taro ya watse ko ta kan Hajjo bai bi ba ya koma Zaria. Duk wani hanya ya bi akan Maryam tayi haƙuri amma ta ƙi tace abu ɗaya ta ke so shine ya saketa. Ya ma ta bayanin babu wanda zai sake zuwa gidan su cikin Iya da Inna amma ta ƙi sauraren sa. Ya aika abokanan sa da dama amma ta ƙi komawa. Ƙarshe aka bashi shawaran ya barta ta huce tukunna.
Hajjo da ta yi sati a gida ta ga T J bai bi ta kanta ba sai ta tattara ta dawo. Gaba É—aya ba ta gane kan T J ba, idan ba tambaya gameda Sadiq ba baya kulata.
Wasa-wasa har Maryam ta gama exams ba ta koma gidan T J ba. Itama daurewa ta ke yi domin har yau tana tsananin son T J amma dole ta katse alaƙarsu saboda a yadda ta hango auren su za ta cigaba da fuskantar ƙalubale matuƙar Iya ba ta son ta. Its better to quit now tunda ma ba haihuwa tsakanin su. Ba ta ji za ta iya son wani bayan T J ba amma kuma rabuwa shine mafita.
T J ya gama marking scripts na student ya fito daga office zai tafi gida ya yanke jiki ya faÉ—i. BuÉ—e idon da zai yi ya ganshi a Asibiti. Jinin sa ne ya hau abunda aka ce da shi kenan.
Matuƙar Maryam ta cigaba da demanding saki a wajen sa ƙila zuciyar sa ne za ta buga ya mutu kawai. Bai ji zai iya rabuwa da Maryam ba ko da ita Maryam ɗin ne ta nemi rabuwa da shi...
Maman Lucas na sanar da ita an kwantar da T J a Asibiti hankalinta ya tashi, hankalinta a tashe ta shirya su ka wuce asibitin, lokacin da su ka je bai farfaɗo ba. Gaba ɗaya ya rame ma ta dama ina jikin yake balle yanzu da damuwa ya ƙara busar da shi. Ganin yana bacci ne ya sa ta koma gida dan ta haɗa ma sa abinci. Zuwanta gidan na su kenan na farko tun bayan abinda su Iya su ka ma ta kusan sati biyar da su ka wuce. Ta samu gidan kaca-kaca as expected, dama haihuwa ya sake sawa Hajjo ƙazanta.
Ɗakinta ta buɗe shima ya ɗan yi ƙura ta cire kayan jikinta ta sa kayan gida ta fito ta shiga kitchen babu wasu abubuwan da ta ke buƙata dan haka ta fita gidan su Maman Lucas ta aiki Lucas ya siya ma ta kayan miya.
Faran shinkafa ta dafa da miyar ugwu wanda ya ji stock fish da kayan ciki. Ta haÉ—a komai sharp-sharp ta wuce Asibiti wannan karan ta samu T J ya tashi har ma suna taÉ—i da wani abokinshi lecturer daya zo duba shi.
Ganin Maryam ya sa ya ƙara langwaɓewa yana ma ta shagwaɓa musamman dayaga hankalinta a tashe ya ke da ciwon na sa. A baki ta dinga bashi abinci, ya kuwa ci sosai. Rabon da ya ci abincin kirki tun tana gidan sa...
Ƙarfe Shida ta baro Asibiti dan ta taho ma sa da wasu kayan buƙata. Ashe tana tafiya ya ce a sallameshi duk da kuwa likita ya ce ya bari sai bayan kwana biyu tukunna kafin nan ya warware sosai amma ya ƙi. Shi kam maganin sa Maryam ne ba zaman Asibiti ba.