← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 161

Sashe 93

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jima tana kuka kafin daga baya ta tashi ta wanke fiskarta ta fito ta fara haɗa kayanta. Ba za ta iya ba, indai haka ake ruɗar da mutum da tambayoyi ba za ta iya ba. Wai tun daga gwaji fa kenan, gwajin ma da Ahmad wanda shima ko case ɗaya bai taɓa yi ba.

Tana cikin haɗa jaka ta ji wayarta na ringing a cikin handbag ɗin ta, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta chanja ra'ayi ta fiddo da wayar. Justice ta gani a jikin screen ɗin dan da haka ta saving numbar sa. Wayar na yankewa aka sake kira, haka kawai jikin ta yai sanyi maimakon ta ƙi ɗaukan wayar kamar yadda zuciyarta ya riya ma ta sai kuma ta swiping ta ɗauka kiran.

Assalamu Alaikum. Sassanyar muryar sa ya ambata.

Murya a dashe ta amsa sallamar tareda jan hanci saboda majina da ke ƙoƙarin zubowa.

"Ina son ganin ki a office É—ina yanzu" ya faÉ—a da isa da gadara.

"Sir ba zan iya zuwa ba, gida zan tafi"

"Minti talatin na baki" daga haka ya kashe wayar.

"Shi a su wa zai dinga nuna min iko, ba zan je ba, tafiya ta zan yi" ta yi maganar tana murguÉ—a baki kamar a gaban sa ta ke. Dai dai lokacin wayan Auwal ya shigo. Sai da ta nitsu kafin ta É—au kiran, maimakon muryan Auwal sai muryan rabin ranta ya doki kunnen ta.

"Mom we miss you" Hadid ya faɗa da ƙarfi. Hashir ya ce "Mom yaushe za ki dawo?, GrandMa ta ce sai kin iya aiki za ki dawo. Mom ki yi sauri ki iya kin ji"

Hadid ya ƙarɓi wayan yana faɗin "Mom wai irin arise my case kike koya? irin wanda ake yi a TV?"

Kuka ne ya so kuɓuce ma ta tayi saurin toshe bakinta tana jin faɗan 'ya'yan na ta inda Hashir ke cewa ba arise my case ake cewa ba i raise my case ake cewa. Daga baya ta ji Auwal na gyara mu su akan cewa duk ba su ci ba "i rest my case" ake faɗa. Sama-sama su ka gaisa da Auwal ta mishi sallama akan za ta yi wani aiki, ya so gane cewa ta yi kuka amma sai ta ce ma sa mura take yi shiyasa muryar ta ya dashe.

Maganar 'ya'yan ta ya sa ta ji wani ƙwarin gwiwa. Kayan da ta fara haɗawa duk ta mai da su. Ta chanja kayan jikin ta sannan ta fita daga gidan da ɗan guntun confidence ɗin ta.

Office ɗin Justice ta fara zuwa, faɗa ta yi zaton zai ma ta amma kamar kullum taƙaitacciyar magana ya yi ma ta wacce ke kama da ƙarfafa gwiwa.

"Babu wanda baya faɗuwa, sai dai ga mai hankali, da ya faɗi zai yi ƙoƙari ya tashi ya karkaɗe jikin sa ya cigaba da tafiya"

Yai shirun kusan minti É—aya kafin ya ce " ki sake shiri, gobe za a cigaba"

Da wannan ta bar office É—in sa bayan ya É—aga ma ta hannu alamar ta tafi.

Washegari da aka cigaba da case ɗin ta daure ba ta yi wannan katoɓarar ba, although muryar ta na rawa amma ba ta girgiza da jin points ɗin Ahmad ba. Wannan karan Barr. Noah magana ya ma ta akan ta dinga saita nitsuwar ta kuma yi ƙoƙari wajen daidai ta muryar ta.
Har su ka gama ba ta ga Justice ba kuma ba ta san dalili ba amma ta so ya gan ta yau É—in tunda ta samu improvement...

Yau ne ta gama sati biyun da za ta yi a ƙarƙashin Barr. Noah. Dan haka da wuri ta zo ta kuma shiga wajen Justice dan ta bashi report kamar yadda ya ce.
Cewa yai ta ma sa summarizing abinda ta koya a wajen sa a taƙaice. Duk yadda ta so saita nitsuwar ta sai da muryarta yai rawa lokacin da ta ke yiwa Justice bayani.

Bayan ta gama ne ya É—auko wasu files guda biyu ya ba ta ya ce ta je ta studying É—in su na sati É—aya sai ta dawo ya ma ta tambayoyi. Case ne wanda ya ke É—an kamaceceniya da irin case É—in Mommy.

Da ke bai yarda ta tafi da files ɗin gida ba sai ta zauna a office ɗin su ta fara dubawa. A haka Ahmad ya shigo ya sameta tunda su uku ke sharing office ɗin da wani Barrister Yusuf wanda shima sabon ma'aikaci ne amma ya shekara da fara aiki. Ƙarfe huɗu suka tashi ta tattare kayanta sai gida. Tana cikin Mota traffic ya tsaidata ta ji waya na ringing a jakar ta sai dai kuma ba irin ringing ɗin wayar ta ba. Ta sa hannu a jakar ta zaro wayar sai ta ga Hajia Ghazala a jikin screen ɗin wayar.
Ta maimaita sunan a ranta kafin ta É—au kiran tana mamakin ya akayi sunan ya shigo wayar ta.

"Assalamu Alaikum, Ranka shi daÉ—e kamar motar ka na gani ta wuce ni yanzu" matar ta yi maganar da wani nitsuwa da sanyi irin maganar da mace ke yiwa mijin ta idan tana rarrashin sa.

"Wrong number" Zaytoonah ta furta kai tsaye.

"Wrong number!" Hajiya Ghazala ta furta jikin ta na wani tsuma. Ta yi saurin duba screen ɗin wayarta. Abu Razz ta gani ɓaro-ɓaro.

"A ina kika samu wayar nan?, ke waye?, ina Abu Raziyan?"
Ta jero tambayoyin cike da damuwa.

"Oho, na gaya miki wrong number ne" daga haka Zaytoonah ta katse kiran ta maida wayar jaka. Tana ji wayar na cigaba da ringing amma ta shareshi, da aka basu hanya ta cigaba da tuƙinta hankali kwance. Numbar Hajiya Ghazala sai da ya kira ta ya fi sau hamsin lokacin da ta isa gida ta fito da wayar, sai a sannan ta lura ba wayarta bane although duka wayan iphone ne. Tunanin ko wayar Auwal ne ta yi tunda shima irin wayar gare shi.
Tana ƙoƙarin nazarin wayar ta ga numbar ta ya kira wanda aka yi saving da *Barr. Zayt*

"Ahmad yau shiriritan ka har exchange É—in waya ka mana. To maza-maza ka kawo min waya gida dan yanzu haka wata Hajia Ghazla ne ko Ghalza ne sai kiran ka take yi. Wait. Ko dai sugar Mommy É—in ka ce dan..."

"Assalamu Alaikum" muryan da ba ta yi tsammani ba ya daki kunnen ta, sai a lokacin kuma ta tuno cewa ita ta yi mistake É—in É—aukar wayan lokacin da ta mayarda files wajen sa É—azu da rana.

Har ya faɗa ma ta zai aiko Ahmad ya zo ya karɓi wayan ba ta iya furta komai ba...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 47

Bismillahir Rahmanir Rahim

"An fitar da sunan alƙalan da za su duba ƙaran, Justice yana ciki"

Banza ta yi da shi ta cigaba da danna wayar ta, tun jiya ta ga sunayen kuma sunan shi da ta gani ya sa ta yi shiru da maganan dan yanzu ko mai sunan shi ba ta son gani. She still recall yadda ta kirashi ta gaggaya ma sa maganganu, ta sani ba dan a waya ba ne ko kallon sa ba za ta iya yi ba balle har ta iya gaya ma sa irin maganganun nan.

"Justice Bulus Kwaplang, Justice Yunus Muhammad Abbas da kuma Justice Shafa'atu Ladan"
Salman ya jero sunayen alƙalan.

"Har na hango ki a gaban Galadima kina zuba bayani, wuhuhu"

"Ba na son surutu Salman fita min a É—aki"

"A yi haƙuri ba ni na kar zomon ba balle a bani rataya"

Tsaki ta ja sannan ta cigaba da danna wayar. Why on earth za a saka sunan shi cikin alƙalan da za su saurari ƙaran?
Wannan ba coincidence ba ne, shi ne dai ya je ya cusa kan sa ciki tunda ya san zai gan ta a kotun.

Ita yanzu ƙaran ma ya fita ma ta akai. Kallon Munafuki ta ke yiwa Justice tunda behind her back ya ne ya nemi auren ta, shi gashi mai sarauta.
To kuwa sai dai ya mutu dan ba auren sa za ta yi ba. Ita ba dabba ba ce da za a je kasuwa a taya a siya. Tana da 'yancin da za ta zaɓi yadda za ta yi da rayuwar ta including wanda za ta aura. Balle yanzu kam ba ta da agenda na aure a gaban ta...

Duk da Mommy ba ta ji daɗin yadda al'amura su ka kasance ba amma kuma yanzu ta barwa Allah komai saboda shine ya san zaɓin da ya dace da Zaytoonah. Abu ɗaya ta sani shine ko da ba Justice Zaytoonah za ta aura ba to dai ba za ta bari ta auri Auwal ba saboda kada a MAIMAITA TARIHI (a novel by my namesake).
Maganganun Humairah tun da jimawa suna nan daram a ranta ba za ta manta ba. Da hannun ta ba za ta bari a samu ɓaraka tsakanin 'ya'yan Tijjani ba.

A ɓangaren 'yan uwan Justice kuwa ranaku na tafiya suna cigaba da shirye-shiryen yadda biki zai kasance. Su ma a chan Ringim ɗin hakan ta ke tunda dai ɗiyar su ta yi goshi gidan sarauta za ta shiga. Hidimar da ba su ma ta ba kafin ta yi aure da kuma lokacin aurenta da Zuhayr shi su ke ƙoƙarin yi yanzu.

***

Kotun ya ciƙa maƙil saboda sauraron yadda case ɗin zai progressing.

Yana zama akan kujera inda ta ke zaune ya kalla, suna haÉ—a ido ta watsa ma sa harara. Wani haushin sa ta ke ji yanzu. And the old man has the nerves to text her this morning ta faÉ—a a zuciyar ta tana hararan iska.

*Ina addu'ar Allah ya taimaka mi ki, ya kuma ba ki nasara, Amin. Remember i'll be there with you so dont panic".

Mr Edet aka fara gabatarwa wanda yai bayani kan abinda ya sani gameda kamfanin da Patrick ya gina da kuma yadda bayan mutuwar sa kwatsam ƙanin sa Udodiri ya riƙe kamfanin a matsayin na sa bayan ya yi chanje-chanje a kamfanin including chanja sunan kamfani.
Chapter 93 · 0% Book details