← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 161

Sashe 147

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Safara'u ta kurɓi juice ɗin da aka kawo ma ta ta ce "ni dai ƙarshen maganan mu da ke cewa ki ka yi Galadima ya saketa. Da ta zo ta haihu kika ce idan 'yar ta kwana biyu zai karɓo mi ki ita ki rene ta"

"Ina cikin matsala Safara'u. Ban san ya aka yi komai ya dagule min ba, yadda ya ke ji da haihuwan nan ina ga ko haihuwar farko da aka ma sa albarka. Ina da tabbacin saboda cikin da ta ke da shi ne ya sa ya dawo da ita" Ghazala ta yi maganar dan ta kare kan ta.

Hajiya Safara'u ta dai ji ne amma ba ta yarda ba dan Galadima ba irin mutanen nan ba ne da su saki matar su cikin sauƙi. Ko lokacin da Ghazalar ta yi ta yaɗawa akan ya saki Zaytoonah ta yi shiru ne amma ba ta gama yarda da zancen ba.

"Ke idan aka ce za'a taimakeki sai ki fara maganar ke ba ka son harka da Boka. Ni na gaya miki Malami ke mini aiki ba boka ba. Laya ce kawai za'a ba ki amma wallahi sai kin dawo kina godiya"

"Abin bai kai nan ba Hajiya Safara'u. A hankali zan yi maganin Galadima, musamman idan na samu ciki..."

Hajiya Safara'u ta furzar da juice É—in da ke bakin ta tsabar dariya.

"Lafiya ki ke dariya?"

"Stop deceiving yourself Hajiya Ghazala. Ba abinda za ki yi ki raba Galadima da Zaytoonah musamman yanzu da rabo ya shiga tsakanin su. And ciki? Kina tsammanin za ki samu ciki?" Ta ƙarisa maganar tana dariya

"Ba na son walaƙanci Safara'u. Mi ki ke nufi da ni ne, ai ban wuce shekarun haihuwa ba"

Sai da Hajiya Safara'u ta sha dariyarta kafin ta ce "kin ga Ghazala gara ki nemi mafita na dahir wa kan ki. Samun kan Galadima haka kawai ba zai taɓa yiwuwa ba."

" tashi ki bar min gida" Ghazala ta faÉ—a a fusace.

Bayan tafiyar Hajiya Safara'u ta juya maganar da su ka yi sosai amma ba ta samu matsaya ba.
To lokacin da Zaytoonah ta dawo gidan kuma kishi ya hanata sukuni ga uwa uba yadda yaran Galadima su ka juya ma ta baya su ka tare a gindin Zaytoonah.

Cikin ƙanƙanin lokaci Shaiɗan ya hure ma ta kunne sai gashi ta kira Hajiya Safara'u akan maganar da su ka yi.

Ita dai abu ɗaya ta ke so wato shine ta samu kan Galadima ta san idan ta samu kan shi cikin sauƙi za ta sa shi ya saki Zaytoonah.

Kuɗi kawai ta turawa Hajiya Safara'u ta account dan a cewarta ba ta da lokacin zuwa ƙauye, besides ba sai ta je ba koma minene ta karɓo ma ta kawai...

Kubra Sadiq ɗaya daga cikin sales girl ne na shagon Hajia Ghazala. A Nyanya ta ke amma da ƙarfi da yaji ta samu aiki a cikin Abuja, kafin shagon Hajia Ghazala ta yi aiki a wani restaurant daga baya aka koreta. Tana zaune a wajen Kawun ta ne amma kusan kaman zaman kan ta ta ke dan shima Kawun akwai son abin duniya baya tsawatar wa Kubra ko kaɗan, kusan ma za ka iya cewa tafi ƙarfin sa ne. Son kuɗi da abun duniya ne da ita har na jaraba.

On this faithful day ta shiga office ɗin Ghazala ta kai ma ta report na abubuwan da su ka ƙare da wanda su ka kusa ƙarewa saboda ta kusa tafiya sari.
Lokacin da ta shigo Ghazalar na waya shiyasa ta tsaya tana jiran ta. Tana tsaye sai ta hango wani awarwaron gold na Ghazala guda ɗaya a ƙasa.
Sanda Ghazala za ta shiga banɗaki ne ta cire su guda uku ta sa a kan table, to da ta dawo ba ta bi ta kan su ba sai ta cigaba da harkokin ta. Sanda ta zo ɗauka kuma ashe ɗaya ya faɗi ƙasa, sai ta saka biyun akan daga baya za ta duba ɗayan.

Bayan ta gama wayar ne ta karɓi report ɗin a hannun Kubra sannan ta ce ta tafi. Kubra ta fita tana Allah-Allah kar Ghazala ta ga ɗaya awarwaron.

Kusan awa É—aya bayan haka Ghazala ta fita daga office akan za ta je ta dawo.
Kubra da ta ga fitan Ghazala ko minti biyar bai cika ba ta sulale akan za ta je banÉ—aki nan kuwa office É—in Ghazala ta je.

Ba yau ne ta taɓa yiwa Ghazalar sata ba dan a fakaice tana sace kuɗi da wasu ƙananun abubuwan da su ke da wuyan ganewa da wuri.
Sa'arta ɗaya kuwa sai ga awarwaron na nan a ƙasa inda ta gan shi. Ta ɗauka tana murmushi. Dai dai ta zo fita daga office ɗin ta jiyo muryan Ghazala tana dariya.

Kubra ta doka salati ta yi baya da sauri banɗaki ta ke shirin shiga ta ji ana shirin buɗe ƙofa dan haka ta yi saurin ɓoyewa ta bayan wani wardrobe babba inda kusan Duk wasu valuable abubuwa da su ka danganci takardu ko ƙananan abu suna nan a wajen an kulle da key da kuma password wanda Ghazalar ce kawai ta sani.

Ghazala ce ta shigo tareda Hajiya Safara'u.

"Kin san da kin ƙara minti biyu da ba ki sameni ba"

"Ai na ci sa'a kuwa dan nima so na ke na kawo miki saƙon ki sai na wuce gida ina da baƙi"

"Ya aka yi an dace kuwa?"

"Sosai ma. Ai sai kin ƙara kuɗi ma Allah"

"Duk uban kuɗin da ki ka karɓa Hajia Safara'u. Ai idan kika ga na ƙara miki sisi to na ga biyan buƙata ne"

"Sha kurumin ki ƙawata. Wannan mutumin aikin sa 100% original ne ba algus. Yanzu dai"

"Ina zuwa?" Ghazala ta faɗa ta miƙe ta je ta sawa office ɗin na ta key.

"Kin san za a iya shigowa anytime musamman wannan Kubran nan da sam ba ta da tarbiyya"

"Yawwa. Na yiwa Malam bayanin komai kuma ya bani taimako. Kin gan ta nan"

Hajiya Safara'u ta fito da wata laya a cikin jakarta. Layan yana cikin farin leda.

Ghazala ta karɓa tana jujjuya ledan. Wai dan ɗan wannan abun ne sai da ta ba da kuɗi dubu ɗari bakwai da hamsin.

"Yadda za ki yi amfani da shi shine, za ki samu gashin shi tsilli uku sai ki ɗaura a jikin layar. Sai ki sa a ƙarƙashin pillow ko gado ki tabbatar ya kwanta dai akai. Idan har ya kwanta akai shikenan sai ki cire ki je ki bisine. Galadima ba zai ƙara yi mi ki mu su ba"

"Dole gashin sai tsilli uku?"

"Ghazala kenan. To ko duka gashin aka ce ki ba za ki iya ba ne"

"Wannan ma mai sauƙi ne ai. Batun binnewan zan iya bisine shi a ko'ina?"

"Iyi"

"Hajiya Safara'u indai wannan abun yai aiki za ki samu tukuici"

"Ranki shi daÉ—e Sarauniyar Galadima"

Su ka tafa tareda fashewa da dariya. Ba su ƙara minti biyar ba Su ka fita dan kowa yana da inda zai je...

Lokacin da Kubra ta fito daga office ɗin Ghazala gaba ɗaya ta haɗa zufa saboda tsorata da ta yi. Duk iskancinta bai kai ta yi shige-shigen neman magani ba. Tana iya ƙoƙarin ta sai dai rashin samun tarbiyya mai kyau da kuma kwaɗayi ya sa ta ke ɗan sata da kuma bin maza wasu lokutan. Amma Asiri? Tsubbu?.

Ba ta taɓa ganin Galadima face to face ba amma hoton sa da ke office ɗin Ghazala ya sa ko a ina ta ganshi za ta iya ganeshi.
Ba wanda bai san mijin Ghazala shine Justice Yunus Muhammad Abbas ba a Shagon na ta saboda yadda ta yaÉ—a abin lokacin auren su.

Da farko tunanin blackmailing É—in Ghazala ta yi da audio É—in da ta naÉ—a na hiran su. Daga baya ta ce idan ta yi haka lallai kuwa itama ba ta tsira a wajen Ghazala ba. Nan da nan ta yanke hukuncin samun Galadima.

Excuse ta nema na awa ɗaya ta fita daga katafaren shagon ta nufi office ɗin Galadima bayan ta kira wani stingy saurayinta da ke Law School na Abuja. Sunan Justice Yunus ba ɓoyayye ba ne shiyasa ta samu address ɗin office ɗin sa a wajen sa.
Ko da ta je ba ta samu ganin sa ba dan ba ta da appointment kuma ma yadda ta ke ɗin ba ta yi kama da wacce za a gabatar da ita wajen Justice kai tsaye ba ne. Sai dai lokacin da ta ce Dan Allah a gaya ma sa saƙo ne mai mahimmanci gameda matarsa ta ke son bashi, ta kuma nuna ID card ɗinta na aiki. Sunan shagon Ghazala ce a jiki kuma shi Secretary ɗin ya san Ghazala matar Galadima ce. Yo tunma kafin auren su ya san alaƙar da ke tsakanin su.
Kiran Galadima yai ya sanar da shi zuwan Kubra. Galadima ya ce idan ya gama magana da baƙon sa ya turota office ɗin sa.

Bayan minti shauku sannan ta shiga office ɗin. Ƙirjinta ya dinga dukan tara-tara ganin Galadima cikin gown ɗin Alƙalai, yau yayi zaman kotu shiyasa ya saka gown ɗin. Ta ma ci sa'a ne dan bai fi minti Arba'in da shigowa office ɗin ba.

Sai da Galadima ya ce ta zauna kafin ta É—an É—osanu a kujeran tana tunanin ta inda za ta fara ma sa bayani.

Kwarjinin sa da yadda ta tsinci kan ta da fargaban ganin ta gaban Alƙali ya sa gaba ɗaya ta kasa yi ma sa ƙarya. Ta gaya mishi sata ta je yi office ɗin Ghazala ta saurari hiran su da Hajiya Saratu har ta kunna wayarta ta yi recording. Kunna ma sa audio ɗin ta yi wanda ya fara daga inda Hajiya Safara'u ke yiwa Ghazala bayanin yadda za ta yi amfani da layar da ta karɓo ma ta.

Galadima a nitse ya saurari audio É—in wanda hakan ya sa Kubra ta tsorata dan ko kaÉ—an ba ta ga alamar damuwa a fiskar sa ba.

Bayan ya gama saurara sunan ta ya tambaya ta gaya ma sa baki na rawa.
Chapter 147 · 0% Book details