Sashe 4
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar Tijjani da Gidaɗo kan su ɗaya sai ya zamana kullum suna maƙale tare kaman 'yan biyu abinci ma tare su ke ci, ko Aishatu ta zubawa Tijjani nashi haka zai ɗauka ya je ɗakin Maryama ya zauna su ci tareda Gidaɗo. Watarana suna cin abinci tare sai Aishatu ta zo ta raba su ta ja kunnen Tijjani ta ce kul ba ta yarda ya sake cin abinci da Gidaɗo ba har da cewa ta sake kama shi sai ta ma sa shegen duka. Ashe kaf abin ya faru a idon Yadikko ne, ba ta ma ta magana ba sai da Abubakar ya dawo ta ce ya je ya kwaso kayan Tijjani ya kawo wajen Maryama bai tambayi dalili ba yai kamar yadda mahaifiyar sa ta umurta.
Aikuwa Aishatu ta yi faufau ba za a bawa Maryama É—an ta ba, ta biyo Abubakar har tsakar gida tana ta masifa.
Yadikko ta daka ma ta tsawa ta ce idan hukuncin da ta yanke bai ma ta ba ta wuce gidan su, ba za ta zo ta haÉ—a gaba tsakanin jikokin ta ba.
Aishatu ta yi shiru tana huci. Daga lokacin da Tijjani ya koma wajen Maryama Aishatu ta ƙi shi, ko ya zo kusa da ita sai ta dinga hantarar sa kamar ba ɗan cikinta ba. A da duk cikin 'ya'yan ta tafi son shi saboda tsananin kamannin sa da Mahaifinsa, Abubakar da Tijjani yadda ka san an tsaga kara, amma yanzu gaba ɗaya ta ƙi shi. Shi ma bai damu ba saboda yarinta ya koma ɗakin Maryama hankali kwance. Har wa yau Goggo Maryama ya ke gani a matsayin Uwa ita Iya haihuwar sa kawai ta yi amma duk wani tarbiya da ya samu daga wajen Goggo ne.
Gidaɗo Allah bai yi shi lafiyayye ba ashe ciwon sugar ya ke da shi ba a sani ba. Idan ciwo ya tashi ayita ɗura ma sa maganin gargajiya wani lokaci abin yai sauƙi wani lokaci kuma kamar ba zai yi rai ba. Yana shekara goma shahuɗu aka ma sa aure bisa shawaran manya akan ƙila aure zai sa ya samu lafiya. Wata cikin 'yar uwarsa aka aura ma sa 'yar shekara shauku. Shekaran farko kam da Gidaɗo da Hannatu an tafka kwaɓa da shirme kafin a hankali su ka samu kan zaren. Gidaɗo na shekara shashida ya rasu nan ma ciwon sa ne ya tashi ana ta bashi maganin gida sai kumburi ya ke yi ƙarshe aka kai shi Asibiti a Kano a nan likitoci su ka gano ainihin mi ke damun shi amma its too late dan ko sati bai yi ba da aka fara treating na shi ya cika.
Da rabon Asma'u za ta zo duniya ya sa aka ma sa aure da wuri dan bayan rasuwar sa aka gano Hannatu na da cikin wata biyu.
Tundaga primary school Tijjani ke da ƙwazo hakan ya sa lokacin da ya ci makarantar kwana Yadikko ke ƙorafin zai yi nisa da gida kuma Bokon ma yawanci daga primary 'yan gidan su ke tsayawa, akwai wani ɗan Kawun su Tijjanin da ya fara Sakandare ya watsar ya dawo ya cigaba da noma ya ce a ma sa aure. Ta ce ita ba ta so Tijjani yai nisa da gida.
Modibbo ya ce Tijjani É—an Baiwa ne idan aka bashi dama zai yi ilimi sosai.
Dole dai haka ta haƙura Tijjani ya tafi boarding school. A cikin jikokin na ta ba ƙaramin son Tijjani ta ke ba har ba ta iya ɓoyewa.
Daga gama secondary school ya samu sakamako mai kyau ya kuma samu gurbin karatu a ABU Zaria inda ya ke karantar Maths and Statistics. A shekarar sa ta biyu ne Allah yai wa Modibbo rasuwa. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har ta kawo yanzu da Tijjani ya gama makaranta har ya kusa kammala bautar ƙasa.
Wannan kenan...
***
Cincirindo aka yi a ƙofar ɗakin Goggo ana son kallon Arniyar da Tijjani ya kawo gida. Daga balbali-balbali matan yayye, ƙanne da ma 'ya'yan gida haka ake ta shiga ana dubata. Babu wanda Goggo ta tankawa cikin su dan ta san neman magana su ke yi. Wa su da sun shigo sai su cewa Goggo ɗakinta ya zama najasa tunda akwai Arniya a ciki, wasu su ce indai ta yi sallah a ɗakin sallarta ba zai karɓu ba. Wasu kuma su ce mala'iku sun tsine ma ta tunda ta ba wa Arniya mafaka. Jahilci dai kala-kala.
Nkiru kam tunda aka fara shigowa ana kallon ta ana yare ta duƙunƙuna kanta jikin bango tana hawaye. Yadda su ke ma ta kaman wata alien ce a ɗakin, ko da ba ta jin Fulatanci ta san zaginta su ke yi.
Yadikko ta yi masifar amma ba wanda ya kulata sai shigowa ake yi ana turereniya...
T J kam da sassafe da ya shigo ya gaishe da Iya ta sashi a gaba da faÉ—a wai taji ya kawo mu su karuwa gida to maza maza ya fitar da ita. Yanada masaniya akan Baffa ya sanar da ita komai amma kuma ta rufe ido tana kiran Nkiru da karuwa. Har da cewa dan ya yi Boko ne ya tafi kudu bariki.
"Hamma idan aure ka ke so, ga mata nan birjik a garin ku sai ka je wata duniya ka É—auko Arniya. Tarbiyan da Maryama ta É—aura ka kenan? Allah ya kyauta amma sakayyar da ta min Allah ya isa"
Duk yadda T J ya so ya ma ta bayani ta ƙi fahimta ƙarshe ta ce idan har Nkiru ba ta bar gidan ba kar ya ƙara shigowa ɗakin ta. T J ya fita jiki a sanyaye.
Duk da gajiyar da ke tattare da shi haka ya fita daga gidan.
Zuwan Alhaji Isa gidan ne ya sa kowa ya fara ƙoƙarin guduwa. Faɗa ya farayi yana zagin su kan aikin jahilcin da su ke yi kaman ba Ahalin Modibbo ba. Idan ba su manta ba mutane nawa su ka musulunta a dalilin kyawawan halayen Modibbo. Mutane nawa ne ba musulmai ba ba kuma Fulani ba Modibbo ya bawa mafaka a gidan sa sai a kan wannan za a ringa yayaɗa magana kamar wani sabon abu ne a gidan.
"Wallahi duk wacce ta muzgunawa yarinyar nan sai na bata kashinta a hannu" daga haka ya juya ya fice, ana bashi haƙuri amma bai saurari kowa ba.
Alhaji Isa ƙanin Modibbo ne. Duk cikin su kuwa shine Allah ya bawa arziƙi, yafi kowa yawan shanu da gonakai. Yayinda Modibbo ya ke babban malami shi babban ɗan kasuwa ya zama. Shima dai gidan sa kusa ya ke da gidan Modibbo dan gaba ɗaya inda kakannin su suka zauna a nan suma suka yi ginin su. Sai dai ko ba a faɗa maka ba kana zuwa anguwar za ka san Alhaji Isa wani ne domin gidan sa ya fi na kowa girma da tsaruwa a anguwar...
Tafiyar Alhaji Isa ya sa kowa ya watse ana ta ƙananun maganganu. Sai lokacin Nkiru ta samu nitsuwa.
Kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe sai ga T J ya dawo ɗauke da ledoji guda uku. Ɗaya kayan tea ne a ciki ɗayan kuma kayan sawa ne. Doguwar riga ne irin ta turawa guda biyu sai riga da skirt guda biyu, sai takalmi guda biyu. Ɗaya ledan kuma zannuwa ne guda uku ya bawa Goggo akan ta sa Asma'u ta raka Nkiru wajen Tela a ɗinka ma ta.
Cewa yai ta gwada kayan dan hasashen jikinta yai ya siyi kayan. Tsayawa ta yi tana kallon shi, shima sai ya ƙura mata ido.
"Barkindo da alama dai a gabanka za ta sa kayan" Goggo ta faÉ—a. Ya fara sosa kai ya fice daga É—akin.
Ƙuryar gado Nkiru ta shiga ta fara gwada kayan. Duka sun mata sai doguwar riga guda ɗaya da bai shigeta ba. Takalman ma sun yi daidai.
Kusan minti Ishirin sai ga T J ya dawo ya tsaya a bakin ƙofa yana tambayar Goggo ko ya shigo ta ce Bismillah.
Nkiru ta ma sa bayanin kayan tareda godiya, ya karɓi wanda bai shigeta ba ya ce zai mayar a chanja ma ta. Ya ce akwai bread ta haɗa shayi tunda ba lallai ta iya cin ɗumame ba. Ta yi dariya lokacin da ta ji kalmar 'ɗumame'...
Haka dai kwana biyu su ka shige gida ya fara cika ana ta shirye-shiryen biki. Nkiru kam banda T J da wata Pendo wacce ke ɗan jin turanci kaɗan-kaɗan saboda ta ƙare primary ba ta magana da kowa. Pendo cousin ɗin T J ne shekaranta shauku. Tsakanin ta da Goggo da Asma'u kuwa sai maganan kurame. Asma'un ma ta fara makaranta tana primary one amma ba ta jin turanci.
A hankali ta ke karantar 'yan gida da yanayin su, abinci kam da safe, rana da dare T J ke kawo ma ta. Idan ba za ta je banÉ—aki ba ba ta fita tana zaune a É—aki. Ranan da Pendo ta ce su fito ta ga yadda ake nakiya da Alkhakin biki haka matan ke ta tsura ma ta ido suna nunata da hannu. Itakan abun da su ke ya burgeta dan haka ba ta damu da yadda su ke kallon ta ba ta zuba mu su idanu tana kallon abun da su ke yi.
"Ni tausayi BoÉ—É—iyon Tijjani ke bani. Ashe ga mace har mace amma ba addini ba miji"
Wata daga cikin matan ta faɗi. Boɗɗiyon Tijjani ko Boɗɗiyon Hamma sunan da su ka laƙawa Nkiru kenan.
Pendo ta ce " sunan ta fa Mary"
"Ungo na ki Pendo" matar ta ma ta daƙuwa.
Pendo ta ja baki ta yi shiru...
Da yammacin ranan Muntari ya dawo daga Kano ya zo biki ƙannen sa. Ankaishi makaranta yana aji biyu ya gudo ya ce ba zai iya ba Kwanyar sa da ta Tijjani ba ɗaya ba ne. Buga-buga ya ke yi a Kanon ba wai ya zauna waje ɗaya ba ne ko yana da takamaimai abu ɗaya da ya ke yi. Ya ƙi ma ya zauna a Ringim yai noma, kaman yawancin 'yan uwansa. Ɗan Bokon da yai da kuma shiga Birnin Kano da ya ke yi ya jawo Muntari ya koma wani shaƙiyi. Shekarun sa shatara amma abinda ya ke yi da burukan da ya ɗaurawa ransa ko ɗan shekara talatin iya kaci.