Sashe 75
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanyar su ta dawowa ne Ben ya kira Zuhayr. Hankali a tashe ya ke ma sa magana saboda abinda ya gano a gidan su.
"Miyasa ba ka gayamin ba?" Ya sake maimaitawa jin Zuhayr yayi shiru.
Ba ya son yai maganan da zai sa Zaytoonah ta gane tunda sun yi magana da Mommy akan za ta gaya ma ta idan sun dawo.
"Ka yi haƙuri" ya furta a hankali yana kallon Zaytoonah da ta baza ido da kunne tana sauraron wayan na su.
"Na kusa dawowa, za mu yi maganar idan na dawo" ya faÉ—a tareda kashe wayar.
"Shi wannan Ben É—in ba zai bar ka ka huta ba ne. Bini bini ya kiraka"
"Laifi ne idan mutum ya nemi jin lafiyar É—anuwan sa?"
"Ba laifi ba ne amma shi wannan na sa nacin yayi yawa kullum sai ya kiraka fa sai ka ce mata da miji"
"Baby yaushe za ki bar kishi da Zubayr ne?" Yai maganar yana riƙe hannunta.
Ta kwantar da kanta a kafaÉ—un sa ta ce "Ranan da ya dena bibiyar rayuwar mu"...
Yau saura kwana biyu su koma America. Tana taya Mommy girki a kitchen suna ɗan taɓa hira Mommy ta ce "Adaeze are you happy with Zuhayr"
For the first time sai ta ji kunyar Mommyn. Ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Kina son kwanciyar hankali da lafiyar shi ko"
Ta yi saurin rufe ido tana murmushi.
"Mu je falo na baki wani labari"
Kusa da kusa su ka zauna yayinda Zaytoonah ke wani sunne kai wai kunya. Wai yanzu fa duk abinda su ke da Zuhayr Mommy ta sani tunda ta hanyar hakan aka sameta.
"Kinga girma ya kamaki tunda gashi nan da wasu watanni za ki zama UWA, dan haka ina so ki nitsu ki saurareni da kyau. Kin ga a duniyar nan babu abinda ya kai addu'a da haƙuri daɗi. Yadda su ke da daɗi haka kuma su ke da wahalar yi. Kinga haƙuri da addu'a shiya kawomu rana ita yau. ba dan wannan ba bana tunanin za ma ki zo duniya balle ƙannen ki su biyo baya. Mijin ki na buƙatar wannan abu biyu daga gareki kuma na tabbata idan ki ka bashi wannan za ku samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ki yi haƙuri da rashin lafiyar Zuhayr ki kuma dage da yi ma sa addu'a har Allah ya sa ya samu ya warke gaba ɗaya"
Zaytoonah ta kalli Mommy da mamaki
"Zuhayr ya gayamin yana da Leukemia. Idan kun koma za a fara ma sa treatment ina roƙo dan Allah ki ma sa abu biyun nan. Idan kika tada hankalin ki ko kika dinga kuka ba zai kwantar da hankalin sa ba shima, haka nan ba zai sa ya samu lafiya ba. Ki tayashi da addu'a sosai ki kuma dinga tawakkali da abinda Allah ya ɗaura ma sa har Allah ya kawo ma sa sauƙin sa"
Kukan da ta ke yi ne ya sa Mommy rungumeta tana cigaba da yi ma ta nasiha.
2/11/21, 10:04 PM - ****: 33
Bismillahir Rahmanir Rahim
*family*
Kusan ƙarfe ukun dare ya tashi saboda zafi da ya sa shi a gaba, jikin sa duk zufa. Duk da yanayin sanyi da ake ciki hakan bai hana shi jin zafi ba, da zai kwanta ma da ruwan sanyi yai wanka.
Ya kalli Zaytoonah da ke bacci cikin kwanciyar hankali, yai murmushi da ya tuno cika bakin da ta yi jiya wai dole za ta je gidan su ta ga Mommyn ta. Tana fitowa daga wanka da ta bi lafiyar gado ko minti biyar ba ta yi ba bacci ya tafi da ita.
Ya shiga banɗaki ya tari ruwa yai wanka dan shower ɗin ba ya yi. Da ya fito zama yai a bakin gado yai tagumi yana nazarin rayuwar sa. Yana da kuɗi, ko yau ya dena aiki yanada abinda zai isheshi har ya ƙare rayuwar sa. Kuɗi ba su ne matsalar sa ba yanzu samun lafiya ce damuwar sa. Idan har sun koma zai gayawa Zaytoonah ciwon sa dan ko ya cigaba da ɓoye ma ta ma za ta gane tunda treatment ɗin zai ɗau lokaci. Yana fata a gama komai lafiya saboda ya samu damar sake tsarin rayuwar sa. Yayinda ya ɗau shekaru yana rayuwa domin kuɗi yanzu yana so ya rayu ne rayuwa mai inganci, rayuwar da zai tallafawa mutane ya kuma inganta rayuwar wa su.
Kusan har Asuba bai samu ya kuma yin bacci ba daga baya ma Alwala yai ya kama yin nafila...
Zaytoonah da ke maganar ƙarfe shida tana gidan su sai gashi ƙarfe shidan ma ba ta tashi daga bacci ba.
"Baby ƙarfe bakwai saura ki tashi ki yi sallah" ya faɗa yana shafa kumatunta. Ta ɗan muskuta gefe tana faɗin "i want to sleep"
"Ki yi sallah sai ki koma ki kwanta kin ji"
Sai da ta ƙara kusan minti biyu tana mutsu-mutsu akan gado kafin daga baya ta tashi zaune. Ta mitsitstsika idonta kafin ta ce "ƙarfe nawa?"
"6:39am"
"Ya Allah! Shine ba ka tasheni ba"
"Na nawa kenan?"
Ta tashi daga kan gadon tana faÉ—in "ni dai ba ka tasheni ba, da ka tasheni ai zan tashi"
"Ok, Sorry. Next time ruwan sanyi zan watsa miki"
"Da kuwa ka kwana a station" ta faÉ—a tana shigewa banÉ—aki...
Duk yadda ta so ta tafi ya hanata cewa yai yayi wuri da yawa. Breakfast da aka kawo mu su ma ba iya ci tayi ba, tea kawai ta sha dan ta ce a gidan Mommy za ta karya.
Ganin yadda ta ke haÉ—a kayanta ya sa shi tambayar inda za ta kai su.
"Gidan mu mana"
"A gidan ku za ki dinga kwana?"
"Sosai ma, rabona da su tun yaushe. I really miss them"
"Ok ni ma ki haÉ—a da nawa kayan a chan zan kwana"
Ta É—ago ido ta kalleshi da mamaki.
"Yeah, a chan zan kwana nima"
"Kai ba ka jin kunyan surukai ne za ka kwana a gidan mu?"
Ya kwaikwayi maganarta ya ce "Ke ba kya kunyan mijin ki ne za ki gudu ki barshi shi É—aya?"
Fashewa ta yi da dariya tareda matsowa kusa da shi tana faÉ—in "my D abin na ka har da sharri ne. Yaushe na ce zan gudu?"
"Gashi kin gama haÉ—a kayan ki"
"Gidan mu ne fa, ba nisa ma da nan gidan"
Ta ɗan yi murmushi ta ce " Allah Sarki! kamar ba mu yi sintirin zuwa karɓan sadaka a nan gidan ba. Lokacin muna yara duk Jummu'a da an dawo daga masallaci za mu zo karɓan sadaka a wajen Alhaji"
Ya rungumota jikin sa ya ce "yanzu ma ba ta ɓaci ba barin baki sadaka"
"Ban yadda ba, ɓata min kwalliya za ka yi"
"To bari na É—an sha janbakin kaÉ—an"
"Nop"
"KaÉ—an fa"
"Nooooo"
" a taimaka"
Ta kai baki dan ta ma sa light kiss sai shikuma ya riƙe bakin bai saketa ba sai da ya shanye janbakin tas. Dama karanbani ya sa ta shafawa wai dan yai matching da jan Arabian gown da ta saka...
Ƙarfe goma da kwata su ka fito daga gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga su ka nufi gidan su Zaytoonah. Suna tafiya tana ma sa bayanin gidajen da su ke maƙotan su, ya so su ɗau mota amma ta ce ba nisa dan haka ya fasa karɓo key ɗin. Sai kuma da su ka iso gidan ya tabbatar ba nisa ɗin. Lokacin da ta nuna ma sa gidan da Daddynta ya gina sai ya ga ai ya fi wanda za su shiga girma.
"Miyasa ku ke zaune a nan? na ga kamar wancan gidan ya fi girma"
Zaytoonah ta ce "Hmmm, Mommy ba ta son barin nan. Ta ce akwai memories ɗin Daddy a gidan kuma wai duk ranan da Daddy ya dawo gidan zai fara zuwa duba su. Har yanzu tanada yaƙinin zai dawo"
Ya kalleta dai dai sun isa ƙofar gidan ya ce " ke fa kin yarda zai dawo?"
"A duk inda ya ke ina ma sa addu'a Allah ya jiƙan sa ya kuma yi ma sa rahama" ta yi maganar tana buɗe ƙofar falon gidan da sauri dan ba ta son Zuhayr ya ga hawayen da ya ke shirin zubo ma ta.
"Assalamu Alaikum Jama'an gida" ta faɗa da ƙarfi bayan ta goge idonta da bayan hannu.
"Ina kuka shiga ne, gamu mun faso fa"
Ta wuce kitchen tana leƙawa ko Mommy na ciki amma ba ta nan.
"Ko ina 'yan gidan su ka je su ka bar ƙofa a buɗe" ta faɗa tana ƙarisawa ɗakin su Salman. Ba kowa a ciki dan haka ta wuce ɗakinta a nan ta buɗe baki saboda ganin Salman da ta yi yana kwance a kan gadon ta, da alama ma nan ne ɗakin sa yanzu.
"Kai-kai, Salman"
Salman yai firgigit ya buÉ—e ido. Kamar a mafarki sai kuma ya ga Zaytoonah tsaye a kan sa.
"Adaeze ke ce?"
"Shine ku ka bar gida a buÉ—e, tukunna ma wa ya baka izinin dawowa É—akina?"
"Ba É—an welcoming hug É—in nan, daga zuwa za ki hau ni da faÉ—a" ya faÉ—a da muryarsa a dashe.
Ta ɗan ranƙwashi kan sa ta ce "ka rena ni fa" sai kuma ta rungume shi tana faɗin "i miss you Bro"
Ya ce "i miss you too Sis"
Lokacin da ya tashi daga gadon ne ta ke tambayar sa ina Mommy ta je sai ya ce wai Iya ce ba lafiya tana gudawa tun tsakar dare shine da Asuba Anty Hanne ta kira ta faÉ—a ma ta to sai Mommyn ta je da mota ta kaita Asibiti.
"Shine tuntuni ba ta dawo ba" Zaytoonah ta faÉ—a tana tsuke fiska.
"Inaga ta dawo ƙila suna gidan ne"
"Wai ina Junior ne?"
"Baya gida ko? Ja'iri, yanzu haka gidan su Kamal ya tafi. Maganin mura fa na sha na kwanta na barshi yana kallo a falo kafin na shigo É—aki, ashe fita yai"
"Zo mu je ka gaida mijina" ta faÉ—a cike da burga.
Salman na fitowa ya miƙa ma Zuhayr da ke zaune hannu yana faɗin "ashe dai kafi hoto kyau"
Zuhayr yai murmushi yana tambayar sa ya gari.