Sashe 90
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanda ya dawo daga masallaci sannan ya zauna da yaran sa uku su ka ci abincin dare ana ci ana hira kowa na kawo complain ɗin sa. Ƙarfe tara da rabi kamar kullum su ka ma sa sallama dan lokacin baccin su kenan, ita kam Suhailah tuni ta yi bacci dan haka a kafaɗar sa ya ɗauketa ya kaita ɗaki.
Bayan ya gama tofa mu su addu'o'i kafin ya fito daga ɗakin na su ya wuce na sa ɗakin. Kujerar da ya ke aiki ya hau ya buɗe Laptop ɗin sa yana duba wasu saƙonni, aƙalla ya kai minti Arba'in yana aiki kafin ya kashe ya hau gado ya kwanta. Bayan ya tofa addu'o'i sannan ya rufe idon sa, sai dai me? ba abinda idon sa ke gani sai hoton Yarinyar nan shekaru shida kenan da su ka wuce, yana ganin yadda take tauna plaintain chips ɗin yana ba da sautin ƙurmus, ƙurmus, ƙurmus. Ya tuna lokacin da ta kira shi da Uncle ɗin ta bayan an hanata shiga wajen hall ɗin da ake dinner.
*"Majesty ko dai za mu yi Amarya kwanan nan ne?"*
Maganar marigayiya matar sa kenan lokacin da ya ke ba ta labarin Zaytoonah bayan ya koma gida. Shi kan sa mamakin kan sa ya ke yi yadda ya zage yana ba ta labarin Zaytoonah hadda mimicking irin maganar ta da expression na fiskarta.
*"Na gaya miki yarinya ce fa"* amsar da ya ba ta kenan a lokacin. A ranan har ƙaramar muhawara su ka yi a kan Zaytoonah.
Ya buÉ—e ido yana kallon sama duk da wutar É—akin a kashe ya ke, duhu kawai ya ke kallo.
Ba zai iya faÉ—in takamaimai dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba har ta kai yana son sanin wani abu gameda ita da rayuwar da tayi a baya.
Shi ba yaro ba ne ya lura da yadda Ni'ima ke ta kawo ma sa hiran Zaytoonah tun a chan Zaria. A yadda ta ke nanata ma sa cewa Zaytoonah Bazawara ce mijinta ya rasu ya barta da 'ya'ya biyu ya san inda tunanin ta ya tafi. Duk da matsin da ya ke samu daga wajen Hajia Abu kan yai aure ko dan su Raziya ba ya tunanin zai iya biyewa Ni'ima. So what idan Zaytoonah Bazawara ce? She's still young ai.
Ya dai sani zai iya ƙoƙarin sa akan ganin ya grooming ɗin ta kan wannan case ɗin da za tayi, duk da ma ya lura yarinyar akwaita da yarinta da shiririta.
Ya jima yana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da shi.
2/11/21, 10:04 PM - ****: 41
Bismillahir Rahmanir Rahim
*Barrister Zaytoonah*
"Daɗin abin ma dai Bazawara ce ake ta wani azarɓaɓi akan ta"
Humairah kenan ke wannan maganar.
Auwal bai kulata ba sai ma cigaba da taje gashin kan sa da ya ke yi. Ba yau ta saba kiran 'yar uwar tata da suna Bazawara ba, da gayya ta ke kiranta da haka shi kuma ba zai kulata ba tunda abinda ta ke so kenan.
" mace daga haihuwa sau ɗaya ta gwajaɓe ta zama buhu, laɓaɓa kamar bagen tumatir. A haka ana wani rawar ƙafa akan ta kamar akan ta aka fara zama Barrister"
Sai da ya gama feshe turare sannan ya juyo ya kalleta.
"Aisha kenan, duk abinda ki ke faɗa gaskiya ne babu ƙarya a ciki amma akwai saura da ki ka manta ba ki faɗa ba wanda su suka fi komai mahimmanci. Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar jarumar mace ce wacce ta yi fama da ƙalubale na rayuwa daga ƙarshe kuma ta kai matsayin da har abada ba za ki taɓa kai wa ba. Kin san cikin shekaru huɗu mi ta zama tun bayan rasuwan mijin ta?" Yai murmushin rainin hankali ya ce "ki ɗauko biro da littafi na lissafo miki dan na san ƙwaƙwalwar ki ba zai iya lissaftawa ba. I'm proud of Zaytoonah i will always be"
"Hamma kenan. Ka zageni yadda ka ke so ba zai chanja kasancewar Zaytoonah Bazawara ba"
Wuceta yai yana faÉ—in "zan turo miki hotuna"
Sai da ya fita daga ɗakin hawayen baƙin ciki su ka zubo mata. Wai miyasa har yau Auwal ya fi son Zaytoonah akan ta ne? A da ba soyayya ta ke yiwa Hamma Auwal ba amma kusan shekaru uku kenan tana dakon soyayyar sa. Dalilin sa ta amince ta sake rubuta NECO ta fara remedial kafin ta samu shiga aji ɗaya a ABU har ta kai yanzu da ta ke aji biyu inda ta ke karantar Biology Education.
Lokacin da ta gama Sakandare aure ta yi niyyar yi musamman yadda saurayin ta Farouƙ ya buɗe ma ta kunne da soyayyar sa ta ƙarya. Ya so ya samu kan ta tun a waje amma duk iskancinta a waje ya tsaya bai kai har ta yi Zina ba. Har Farouƙ ya aika magabatan sa Ringim an bashi Humairah. Daga baya ya zo ya ce ya fasa. Humairah kamar ta yi hauka lokacin saboda ta shirya komai, yadda Zaytoonah ta auri mai kuɗi itama tana son auren mai kuɗi. Bayan abin ya faru ne daga baya Auwal ya siya ma ta form ɗin remedial ta fara. Da farko ta fara abun reluctantly ne daga baya kuma ta ɗan sa himma a karatun.
Tunda Zaytoonah ta dawo Nigeria ta ke lura da take-taken Auwal É—in. Yadda ya ke shishshige ma ta da ita da yaran ta. Daga ya dawo daga office chan gidan Mommy ya ke wucewa ya ci abinci ya sha zaman sa kafin chan dare ya dawo. Idan weekend ne ma to duk a gidan ya ke yi, ko kuma ya É—ebo Yaran su zo gidan su yi ta wasa daga baya ya fita da su shan ice cream.
Allah na gani ba za ta bari Zaytoonah ta samu abinda ta ke muradin samu ba. Hamma Auwal na ta ne...
***
Dukkan gidan aka je ma ta, don wannan ranan farin ciki ne ga iyalen Tijjani. Babu wanda ya kai Mommy farin ciki a wannan rana, kamar yau ta gama Law school lokacin tana da tsohon cikin Zaytoonah sai ga shi 22yrs later 'yar ta ta samu zama Barrister itama. Tana fata É—aya burin na ta ya tabbata a kan Zaytoonah.
"Our daughter is a Barrister now. A duk inda ka ke na san za ka yi alfahari da ita" Mommy ta yi maganar tana kallon hoton T J da ke kan wayarta.
"Grandma lets take picture" Hadid ya faÉ—a yana kama hannun Mommy. Su dai yaran ba sa gajiya da hoto, gajiya ma ta yi da É—auke-É—auken hoton ta zo ta zauna.
Tana son ce mishi a'a ba yanzu ba sai ga ɗan uwansa shima ya riƙe ma ta hannu yana faɗin ta zo su yi hoto, ba yadda ta iya kawai ta tashi ta bi jikokin na ta.
Kwanan su biyu a Abuja kafin su ka dawo Zaria...
Yau Jumu'ah kuma yau ne za su je gidan Kakan su yin weekend dama tare su ke zuwa sallar jumu'ah da Baba Tsoho. Wani lokaci su kan leƙota kafin su tafi gaba ɗaya wani lokaci kuwa daga sun tafin shikenan sai kuma Sunday da yamma. Randa aka ɓata mu su rai kuwa tun Asabat za su dawo gida wani lokaci su ce su Allankatafir ba za su sake zuwa gidan Baba Tsoho ba suna maganar ba su minti talatin za ka ga sun dawo suna ƙasa-ƙasa da murya wajen Mom suna "Mom za mu je gidan Baba Tsoho" tsofin gidan ba ƙaramin tarairayan 'yan biyun su ke ba. Babu sanda za su je ba su dawo da tsaraba ba wani abin ma har mamaki ya ke bawa Zaytoonah, yadda su Hajiya Saudah da Hajiya Nenne ke yi wa yaran tamkar su kaɗai ne 'ya'yan jika a gidan.
Sai da ta gama shirya Hashir ta ɗaga ido ta kalli Hadid da ya takure gefe guda yana kumbura baki shi a dole yayi fushi. Ganin sa a haka da ta yi ya sa ta tuna da Zuhayr yadda ya ke tsokalarta idan tana kumbura baki. Ta yi murmushi wanda sai da ƙwalla ya zubo ma ta, ta yi saurin gogewa tareda cewa "Sweetheart zo na saka ma ka kaya"
Hadid ya maƙe kafaɗa yana faɗin "hun'um"
Tunda ta ce a Hashir za ta fara sawa kaya ya takure gefe yana fushi.
"Mom turare" Hashir ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Zaytoonah ta miƙe dan ta kamo Hadid sai kuma yai hanyar ƙofa yana faɗin shi ba zai sa kaya ba.
Tsayawa ta yi ganin Auwal a bakin ƙofa ya riƙe hannun Hadid yana tambayar sa miya faru. Hadid ya fara bayanin wai kullum Mom ba ta sa ma sa kaya sai ta sawa Hashir, kuma sai ta ce Hashir ne Babba.
Tana tsaye har ya shigo da Hadid ɗakin ya saka ma sa riga sannan ya warware towel ɗin da ke ɗaure a ƙugun sa ya saka ma sa wando. Da Hadid da Hashir ɗin duk shi ya fesa mu su turare har ta taje mu su baƙin gashin su mai yelƙi. Bayan sun fita daga ɗakin ne ya kalli Zaytoonah da ke tsaye ya ce " sannu da ƙoƙari"
"Kai zan cewa sannu ai, ba dan ka zo ba sai mu wuni a nan ina neman sakawa Hadid kaya"
"Mommy ba ta nan ne?"
"E ba ta dawo daga school ba, tanada class 2-4pm"
"Ayya! To bari mu wuce masallaci ko"
Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo yana kallon ta. Ganin kallon yayi yawa ne ya sa ta ce "Ya Auwal ka gama ɗinki na kuwa?"
Ya fara sosa kai yana faÉ—in " Insha Allah gobe zan kawo"
"Ki dai alƙawarin ku na teloli sai a hankali"
"Yi haƙuri Uwar biyu, aikin office ne ya ke riƙe ni kwana biyun nan amma zan ƙarisa gobe da yardar Allah"
Bayan ya fita ta tsaya kallon kayan jikin ta ko da wani abu da ya gani ya ke ƙura ma ta ido har haka. Ba ta ga aibun kayan da ta sa ba, simple doguwar riga ce mai guntun hannu, a sake ya ke dan bai kama ma ta jiki ba. Ta yi saurin kauda wani tunani da ya zo ma ta zuciya. Ita ba ta wannan ma take ba yanzu...