Sashe 50
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wannan shawara ta kwana bayan ta yi istikhara akai.
Washegari da hantsi ta je gidan Alhaji Iliyasu. Bayan an ma ta iso wajen sa ta gaishe shi ta ce ma sa ta zo neman Alfarma ne akan ya representing É—inta a Fadar Sarkin Ringim.
Ya tambayeta mi ya ke faruwa ya ce ta gaya ma sa gaskiya. Maryam ta yiwa tsohon bayanin abinda ke faruwa gameda hukuncin da Muntari ya ɗaukar na aurar da Zaytoonah. Ba ta ɓoye ma sa sharaɗin da ya gindaya ma ta ba na ta aureshi shi kuma zai fasa aurar da Zaytoonah.
"Ikon Allah. Duniya dai sai dai mu godewa Allah kawai. Yanzu Hassada da gaba ta mana yawa Allah ya shiryemu ya sa mu fi gane gaskiya"
Maryam ta amsa da Amin.
Shiru yai na kusan mintina goma har Maryam ta yi zaton ko dai akwai matsala ne dan tsohon sai a hankali.
"Da za ki yarda ma sai na haɗa yarinyar da jikana da ke ƙasar waje. Sai ta yi karatun a chan dan shima Muhammadun Sarkin Boko ne. Abinda ya sa na faɗi haka shine ko da an fasa wannan auren ba haƙura zai yi ba. Ko ta ƙarfi ne zai iya ba da auren 'yar ki ko mi kika gani"
Maryam ta sauke ajiyar zuciya. Ana wata ga wata. Ta bar gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga da niyyar za ta yi shawara ta dawo.
***
It was a tough desicion amma kuma ta tabbata alama da ta gani kaman akwai Alkhairi a shawaran da ta yanke wa 'ya mace guda da ta haifa. Her first sign of motherhood...
Idan Muntari na ji da kuɗi, Alhaji Iliyasu ya taka shi. Idan Asali ya ke ji da shi Alhaji Iliyasu ya ma sa fintinkau dan Alhaji sananne a ciki da wajen ƙasa, dan haka ƙarya ne ya ce zai ja da shi. Sai da aka je Fadan ma ashe Mai Martaba Sarkin Ringim ya san Alhaji Iliyasu domin Malamin sa ne, ya koyar da shi a Sakandare.
Sarki yayi mamakin wai case É—in da ya kashe shekaru kusan ishirin da biyar shine ya sake dawowa hannun sa. Bayan an gabatar da bayanai Sarki yai nasiha sannan ya zartar da hukunci na bayar da auren Zaytoonah ga Jikan Alhaji Iliyasu. Ranan da aka saka dai za ayi bikin ranan É—in aka bari sai dai maimakon a family house da aka sa auren an maida shi cikin Fada za a É—aura auren kuma kamar yadda Sarki ya zama Alwalin Maryam a lokacin auren su wannan karan ma shine na Zaytoonah.
Ko Zaria ba ta koma ba ta aikawa Muntari da gajeren saƙo.
*"Check Mate"*
Yadda Muntari ya sha kunya a shekarun baya haka wannan karan ma ya amshi kashin sa a hannu.
Maryam da kan ta je Bauchi ta É—auko Zaytoonah.
Da su ka koma gida ta zaunar da ita ta ma ta bayanin hukuncin da ta yanke ma ta.
As expected kuka ta fashe da shi.
Fushi sosai ta yi da Mommyn ta kulle kan ta a É—aki tana faÉ—in Mommy ta tsaneta tunda ta yadda a aurar da ita duk da ta san burinta na son zama babbar Lawyer.
As days past, Maryam ta dinga kwantar ma ta da hankali tana nuna ma ta karatu kam za ta yi shi dan sai ta samu admission ma kafin ta bar ƙasar.
Still ba ta ji nitsuwa ba har da cewa ƙila mutumin mummuna ne.
Maryam ta nuna ma ta hoton da Alhaji ya ba ta. Nan da nan Zaytoonah ta fara washe baki, atleast ba da wani mummunan mutum za a haɗa ta ba ko kuma wanda bai yi karatu ba. Tsabar ɗoki sai ta je ɗakin Auwal tana nuna ma sa hoton shi kuwa kishi ya sa ya korota. Ya riga ta ganin hoton infact ranan da su ka yi waya da Mommy ma yana wajen. Dan Maryam ba ta yarda da Auren ba sai da ta yi waya da yaron ta ji shi ɗin wani irin mutum ne ya kuma ɗauki Alkawarin zai bar Zaytoonah ta yi karatu har ta gama sannan ba zai walaƙantata ba...
Ranan Jummu'ah 1 November 2009 aka É—aura auren Zaytoonah Tijjani Abubakar da Muhammad (Zuhayr) Muhammad Iliyasu bisa sadaki dubu Hamsin wanda Kakan sa ya bayar.
'Yan uwa sun hallara kuma anyi hidima dai-dai gwargwado sai dai babu Muntari ciki. Shi tun da Sarki ya yanke hukunci a Fada bai sake zuwa Ringim ba.
Zaytoonah kam kamar ba matar aure ba tunda ba yanzu za ta tafi wajen miji ba. Ta cigaba da rayuwar ta normal. Sai dai Mommy da ke takura ma ta da nasiha once in a while. An bata numbar Zuhayr amma bai kirata ba itama ba ta kirashi ba.
Bayan wata uku aka sama ma ta admission a University of Nevada, Las Vegas. Shi mai girma Ango É—in a Las Vegas É—in ya ke aiki.
Lokacin da aka gaya ma ta ranan wuni ta yi tana farinciki, barin ma da aka turo ma ta admission ɗin ta gani. Ita Auren ma baya gabanta karatu kawai ta ke hangowa tunda wata ɗaya da ya wuce Zuhayr ya kirata kuma sun tsara komai. Auren na su suna ne kawai amma zama za su yi tayi karatu har ta ƙare kafin ya saketa ta kama gabanta (🤔Tam)
Bayan an confirming admission É—in ne ta je ta fara processing visa wanda Alhaji Iliyasu ne ya É—au nauyi. Ita da Mommy su ka je embassy aka yi cike-ciken takardu har komai ya kammala. Bai jima ba bayan sun dawo gida aka kirata akan Visa É—in ta ya kammala. Dan haka aka fara shirye-shiryen tafiya.
Sai da tafiyar ta zo kusa ne kuma jikin Zaytoonah yai sanyi, duk wani ɗoki da ta ke yi ya tafi. Kewar Mommy da ƙannenta ya fara shigarta. Komawa ma ta yi tana kwana da Mommy saboda wai ta ji ɗumin mahaifiyarta. Maryam ma daurewa ta ke yi amma tana jin wannan rabuwan a ranta. Addu'arta a koyaushe shine Allah ya sa auren nan ya zamewa Zaytoonah Alkhairi.
A Abuja su ka kwana gidan Hajiya Fatima. Dukkan su suka zo rakiya, hatta Auwal da ke baya-baya da ita tun lokacin da aka yi aurenta sai da ya zo rakiyan. Anyi koke-koke tun ma kafin a je airport É—in, saboda rabuwa ce da ba a san ranan haÉ—uwa ba kuma iya ka ci sai dai su ga juna a waya ko computer idan su ka hau skype.
Rungume Mommy ta yi tsam tana kuka.
"Mommy i'll miss you, i'll miss you so much. I love you"
Maryam ma hawayen ne a idonta tana É—an bubbuga bayan 'yar tata a hankali.
Sai da aka fara kiran passenger É—in jirgi mai number A2265 kafin Maryam ta breaking rungumar tana faÉ—in ki je kar ki missing jirgin.
Ta rungume Salman wanda shima hawayen ya ke yi.
"Ki dinga kiran mu kullum kin ji"
Zaytoonah ta ce "Insha Allah"
Auwal kam da sauri ya bar wajen ganin yana shirin yin kuka shima.
Ta É—aga junior sama tana faÉ—in " big boy ban da rigima"
Ya girgiza ma ta kai yana dariya.
Sai da ta ajiye shi ta fara jan jakarta tana tafiya bayan ta yiwa Mommy last hug.
"Aytoonah" ta ji muryan Junior ta juya ta ganshi yana É—aga ma ta hannu, yana hannun Mommy dan da bin Zaytoonah ya ke son yi.
"Aytoonah Bye Bye ya ke faɗi har Zaytoonah ta ƙule"
***
With full excitement ta shiga jirgin wannan ne karo na uku da ta taɓa shiga jirgi, sau biyu ta taɓa shiga jirgi zuwa Lagos tareda Muntari. Sau biyun kuma da za a tashi sai da cikinta ya wani juya ta sa hannu biyu ta riƙe shi dan kar ya zazzago a yadda ta ke tunani. Lokacin tashi da lokacin saukan jirgi duk sai ka ga ta tsure saboda fargaba.
Business class ticket aka yanka ma ta dan haka za ta É—an samu ta wataya kaÉ—an ba kamar zuwan su Lagos da su ke tafiya a ticket na economy class ba.
Tana zama ta kalli mutumin da ke gefenta wanda ya ɗaga littafi yana karatu, littafin ya tareshi ba ta ganin full fiskarsa sai dai gefen fiskar sa sannan fararen dogayen yatsun da su ka riƙe littafin zai ƙara tabbatar ma ka mutumin fari ne sosai, tana tunanin ma ƙila Balarabe ne.
Ta gyara zamanta da kyau tana miƙe ƙafa saboda akwai space sosai. Jakar da ke hannunta ta buɗe ta fidda wani ziplock bag da ke cike da plantain chips wanda Mommy da kanta ta soya ma ta.
Ya san an zauna a gefen shi kuma ya lura mace ne shiyasa bai ma yi ƙoƙarin duba ta ba amma wani ƙanshi mai sanyi da ke fita a jikinta ya sa shi tantamar ko dai ya juyo ya kalleta ne, chan kuma ya ce ƙila matar aure ce.
Ƙurumus ƙurumus ƙurumus. Ya fara ji alamun dai ana tauna crispy abu haka. Hakan ya sa ya ɗan sauke littafin da ke hannunsa ya juyo a hankali ya kalleta. Cikin abinda bai kai 2 seconds ba ya gane inda ya taɓa ganin yarinyar, ya ƙura ma ta ido yana tunanin irin wannan coincidence ɗin. Juyowar da Zaytoonah za ta yi sai su ka haɗa ido lokacin ta cika hannunta da plantain chips za ta kai baki. Sai da ta tura duka a bakinta ta miƙa ma sa ledar tana faɗin "wants some?" Ya girgiza ma ta kai ya maida littafin sa ya cigaba da karatu, ya ce a ran sa da alama ba ta gane shi ba.
Ba a jima ba aka fara announcing akan a saka seat belt ayi wata tsiya-wata uba. Zaytoonah ta saka seat belt É—in bayan ta maida sauran chips É—in cikin jaka.
Lokacin da jirgi zai tashi rufe ido ta yi ta damƙe hannun kujeran tana jero addu'o'i. Tsabar tsoro addu'ar da ta zo ranta kawai ta ke karantowa.