← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 161

Sashe 34

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A jikin ledar maganin an yi bayani kan yadda za asha. Za ka iya zubawa a shayi marar sugar ka sha ko kuma ka zuba shi a ruwan zafi zalla. Ko wani leda É—aya za ka sha shi sau biyu a rana wato da safe da kuma dare.

Zaytoonah was so excited, a lokacin ta haɗa guda ɗaya ta shanye da ƙyar saboda ɗaci gashi itama kaman T J ta ke, son zaƙi ne da ita kamar me.
A lokaci guda ta shanye leda ɗaya ta je ta wanke kofin ta kai maganin ɗakin ta ta ɓoye a ƙarƙashin pillow.

Da dare kafin ta kwanta ta kuma haɗa wani wannan karan leda biyu ta haɗa a ƙoƙarin ta na son zama siririya cikin sauri.
Baccin awa ɗaya ta yi ciki ya birkice ma ta. Ta shige banɗaki da gudu sai gudawa fuyaaaaa. Ta gama ta fito amma kafin ta ƙara kwantawa wani ya kuma zuwa ta sake komawa da gudu.
Cikin minti talatin Zaytoonah ta galabaita sosai gashi dama 'yan kwanakin nan da ba ta cin abinci sosai jikinta yayi weak.
A karo na biyar da ta fito daga banÉ—aki ne ta yanki jiki ta faÉ—i tunma kafin ta kai É—akin ta...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*13-mental health*

Bismillahir Rahmanir Rahim

"Wani duniya ka shiga? Its being 14 no 15yrs fa"

Muntari yai wani murmushin gefen baki ya ce "mun tafi neman kuÉ—i kuma mun samu"

"Oh really! zauna ka ban labari. I cant believe wai yadda ka ke ji da Iya za ka iya rabuwa da ita har iya tsawon waÉ—annan shekarun"

"Wow! you can speak Hausa fluently now. That's amazing"
Ya faÉ—a yana zama kujera opposite da wanda ta zauna.

"Your English is superb too"

"Thank you My Dear"

Ba ta kawo komai a ranta ba ganin kamar yana son ya impressing É—in ta ne as always.

"Mi ka ke yi a Lagos all this years?"

"Ko ruwa ba za a bani ba"

"Forgive my manners i'm excited to see you ne"

Lokacin da ta tashi idon sa tarr a kanta yana bin jikinta da kallo har ta wuce kitchen.
Ta ɗan ƙara buɗewa kaɗan ko dan haihuwa amma ga yadda ya santa a shekarun baya chanjin kaɗan ne. She's still beautiful, the only beautiful woman he ever loved and will always love.

Coke mai sanyi da ruwan satchet ta ɗaura a ƙaramin tray ta haɗa da glass cup ta kawo ma sa. Ta ja center table zuwa gaban sa ta ɗau coke za ta buɗe da opener da ta riƙo a hannunta ya ce " water will be fine"

Ta ajiye kwalbar coke ɗin ta ɗauki ruwan ta tsiyaya ma sa a kofi za ta ajiye kofin yai saurin sa hannu akan hannunta ya riƙe. Ta yi saurin cire hannunta ta koma kujera ta zauna tana zuba ma sa ido. He has really changed.

KaÉ—an ya sha ruwan ya ajiye kofin ya ce " ina yarana?"

"Su na maƙota, sun dameni da surutu"

"Ayya! Sun kai biyar ko?" Yai tambayar kamar bai san komai ba gameda rayuwar aurenta.

"Su biyu ne for now, A girl and a boy"

"Allah ya mu su albarka" ta amsa da Amin.

Shiru ne ya biyo bayan haka kafin daga baya Maryam ta ce "daga wajen Iya ka ke?"

Yai murmushi ya ce " daga gidana na ke"

Ta ɗaga gira tana jiran ƙarin bayani.

"Na yi gini a nan anguwar"

"Wow that's lovely, ba ka son ka yi nisa da Iya kenan?"

"Kusan haka dai"

"A ta ina ne gidan? And na san by now ka yi aure har da yara"

Murmushi yai ya ce " na taɓa aure amma mun rabu sannan bamu haihu ba"

"That's sad! Allah ya baka Mata ta gari"

Ya amsa da Amin.

Hira dai ta ɓarke tsakanin su na bayan rabuwa. A tunanin Maryam yadda ta ga Muntari ya waye looking matured yanzu ya manta da abinda ya faru kafin aurenta da T J musamman da ya ce ya taɓa yin aure.
Ga Muntari kuwa ya zo ne yai yaƙi, ko da zai rasa komai na sa indai zai samu masoyiyar sa bai damu ba.

A haka yaran su ka shigo su ka same su inda Maryam ta introducing Zaytoonah da Salman a matsayin 'ya'yan da Allah ya ba ta.
Kallo ɗaya za ka yiwa Zaytoonah ka san mahaifiyarta ta ɗauko sai dai ita baƙa ce. Shi kuwa Salman T J junior ne.

"Zo nan Baby" ya faɗa yana miƙawa Zaytoonah hannun.

"Mommy who is he?"

"He's your Uncle"

Sai da ta ƙare ma sa kallo sannan ta ce "he's evil just like Iya"

Maryam ta buge ma ta baki duk da kuwa ta san kamannin Iya da ta gani a fiskar Muntari ya sa ta faÉ—i haka.

Sai da ta ma ta faÉ—a kafin ta je wajensa, shi kuwa Salman tuni ya riga ya É—ale jikin sa yana ma sa tambayoyi...

Muntari bai bar gidan ba sai chan yamma bayan ya ci abincin rana tareda su.
Tareda Auwal da Salman su ka tafi gidan Hajjo amma Zaytoonah fir ta ƙi bin su. Itama Maryam ba ta takura ma ta ba dan tunda Iya ta aske ma ta gashi ta dena zuwa gidan ko aika ba ta turata...

Kwana uku kenan da zuwan Muntari wanda dukkan su ya kai su zuwa gidan da ya gina wanda ba nisa sosai da gidan su dan a tafiyar ƙafa ba za ka fi minti shida zuwa bakwai ba za ka isa.
Gida ne Babba upstairs wanda ya ƙunshi ɗakuna takwas da falo biyu, akwai kitchen da store. Yana da parking lot wanda aka ajiye motoci uku kuma ya ce duka na sa ne. Akwai ɗakin maigadi a bakin gate ɗin.
Angama komai na gidan amma ba a zuba furnitures ba.
Iya baki ya ƙi rufuwa dan ganin danƙareren gidan da ɗan ta ya gina, sai albarka ta ke sa ma sa.

Maryam ta yi mamakin girman gidan, kamar yadda ya faÉ—a ma ta siye da sayarwa ya ke yi, yana aiko kaya daga Lagos ana siyar ma sa a Kano. Wai yanzu haka yana da manyan shaguna guda biyar kuma ya fara shirye-shiryen buÉ—e shago a cikin garin Zaria.
Addu'ar Maryam shine Allah ya sa ba sata ya ke yi ba cause abin da mamaki...

Kullum sai ya zo gidan sau uku, da sassafe kafin su fita zai ɗauke su a motar sa ya kai yara makaranta ya wuce da Maryam office. Ranan Saturday ya zo ya ɗauki Maryam su ka je gidan sa ya ce ta ƙara duba gidan ta bashi shawaran wani irin furnitures za a sa. Ta gaya ma sa ra'ayinta har da tsokanar sa cewa da yanzu yana da Mata da ita za ta bashi shawara. Yai dariya ya ce zai yi aure nan ba da jimawa ba.

Cikin sati biyu gida ya kammala, an saka komai a ciki wanda ya sa gidan ya ƙara kyau. Har kafin a kammala gidan a gidan Hajjo ya ke kwana amma kusan wuni duk a gidan Maryam ya ke yi, hatta abinci na ta ya ke ci.

"Muntari maganar aure fa?" Iya ta tambaya bayan ya sanar da ita zai koma gidan sa tunda yanzu komai na buƙata akwai ciki.

"Zan yi idan lokaci yayi"

"Nufin ka haka za ka yi ta zama kai É—aya a gida ba Mata?"

"Iya na lokaci kaÉ—an ne fa, zan yi aure"

"Gaskiya kar ya wuce wata uku idan har ya fi haka to ni da kai na zan je na nemo maka Mata"

"Haba Iya sai ka ce ƙaramin yaro"

"Ahaf kar ka yi auren ka gani, wannan irin gida haka ace kai kaÉ—ai za ka zauna ba Iyali ai sai a zarge ka"

Yai dariya ya ce ba mai zargin shi...

***

Kaman da wasa har sun fara sabawa da Muntari, yanzu Zaytoonah ma da ke baya-baya da shi ta sake jiki saboda yawan kayan ƙwalama da ya ke kawo ma ta. Ga shi kullum shi ke kai su school a motar sa. Har Maryam ta sallami mai mashin da ke kai su da.

Muntari bai taɓa nuna ma ta wani alama da zai nuna akwai wani abu da ya ke ji gameda Maryam ba. Wasa da dariyan ƙanin miji kawai ke tsakanin su, abinda ta ɗauka kenan.

Wata ranan Lahdi sai bai zo ya karya ba kaman yadda ya saba hakan ya sa Maryam ta aiki Auwal ya kai ma sa abincin gidan sa. Da ya dawo sai ya ce ma ta wai Uncle ya ce ba shi da lafiya ne shiyasa bai zo ba.
Bayan yara sun tafi Islamiyya ta kimtsa gida ta shirya ta fita. Kitso za ta je amma za ta fara biyawa ta ga jikin Muntari tukunna.

Daga falo ta zauna tana sallama tunda Maigadi ya ce ma ta Muntarin na ciki.

Jin shiru ya sa Maryam ta haura sama. Ta tsaya a bakin ƙofar sa tana sallama

"Muntari ka na ciki ne? Muntari, Muntari are you OK"

Murya ƙasa-ƙasa Muntarin ya amsa ma ta da ta shigo ba ya jin ƙarfin jikin sa ne.
Ta tura ƙofa ta shiga.

Daga tsaye ta ce "Muntari ba za ka je Asibiti ba? Ka ci abincin kuwa?"

"Ba na jin daÉ—in bakina shiyasa ban ci ba"

"Ko na haÉ—a ma ka tea sai ka sha sai mu je asibitin"

"That will be good" ya faɗa yana maƙyarƙyatar ƙarya.

Fita ta yi daga É—akin da sauri ta sauko kasa ta yi hanyar kitchen.
Cikin sauri ta ke haɗa tea ɗin saboda yadda ta ga Muntari na rawan sanyi ba ƙaramin jin jiki ya ke ba...

ÆŠakin ta koma bayan ta haÉ—a tea É—in ta sameshi still yana kwance.

"Muntari tashi ga tea É—in"
Chapter 34 · 0% Book details