Sashe 83
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yadda ka zo duniya salun ƙalun haka za ka koma ba tareda ka ɗau komai ba. Gidan sa, dukiyar sa Iyalin sa duka ba su amfani Zuhayr ba a lokacin da mutuwa ta riske shi. Ayyukan da ya aikata na Alkhairi ko na sharri shi zai je ya tarar a inda ruhin sa ya ke. Idan babu ruhi gangar jikin mutum fankololo ne ba shi da wani amfani amma a hakan mun fi son mu biyewa gina gangan jikinmu fiyeda tsaftace ruhin mu ta hanyar yin ibada da aikata ayyukan ƙwarai.
Bayan mutuwar Zuhayr ya riski Zaytoonah kwana biyu ta yi ba ta san inda kan ta ya ke ba. Tun da ta ga gawar Zuhayr sau ɗaya kafin a je a sallace shi ta suma ba ta sake sanin inda ta ke ba. Kusan kwananta tara a Asibiti ana jinyarta wanda sai ta nuna alamun ta samu sauƙi sai ta sake birkicewa wannan ya sa aka shirya yi ma ta CS kawai saboda tsiratar da lafiyar jariranta. Although cikin yana satin da ya shiga wata tara kenan amma EDD ɗin ta ya nuna ita da haihuwa ma sai nan da sati uku, a ƙalla sai cikin ya shiga wata na goma kenan.
Ranan Jumu'ah da ta kama kwanaki sha uku kenan da rasuwan Zuhayr aka ciro ma ta lafiyayyun tagwayenta maza wanda ɗaya ya ke fari ɗayan kuma baƙi...
*INTERMISSION*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 38
Bismillahir Rahmanir Rahim
*Killed*
"I neec to speak to my lawyer" maganar da Ben ke faɗi kenan lokacin da aka tisa ƙeyar sa cikin Mota a tafi da shi.
Tun kafin a wuce da Zaytoonah Asibiti aka ba ta taimakon gaggawa Allah ya sa ba ta jima cikin ruwan ba da shikenan sai dai wata ba ita ba a duniya.
Zuwa wayewar gari mafiya yawancin gidajen jarida da talabijin maganar kama Benedict Haddish ake yi a garin Las Vegas. A wannan kayaniya da ake yi ne Faisal Khan ya kira Zuhayr dan ya ma sa jaje tareda tambayar wani Asibiti aka kwantar da Zaytoonah. Hankalin Zuhayr ya yi ƙololuwar tashi dan baida masaniya gameda abinda ke faruwa a Asibiti ya ke inda ya ke samun kulawa. Jikinsa na ɓari ya hau yanar gizo dan ya tabbatar da abinda Faisal ɗin ya ce domin har lokacin bai gama gaskatawa ba.
"No Ben, No Zubayr. This is not true, he cant do this" ya faÉ—i yana girgiza kai.
Numbar Zaytoonah ya kira amma a kashe zuciyar sa ya buga da ƙarfi, ya dafa dai-dai wajen zuciyarsa yana nishi sama-sama...
***
Bayan kwana uku
Da ikon Allah ba abinda ya samu Zaytoonah ta dai kwana ɗaya a Asibiti kafin aka sallameta. Zuhayr kam sai da aka yi da gaske kafin aka dai-dai ta numfashin sa. Da ya tuna abin a ran sa sai zuciyar sa ta cunkushe numfashin sa ya dinga fita sama-sama, ranan kam da ya ji saƙon ya suma ya kai sau huɗu hakan ya sa aka ma sa allurar barci. Washegari daya tashi da yamma ci ne ya ga Zaytoonah a gefen sa wanda hakan ya sa shi samun nitsuwa kaɗan. Ita kan ta Zaytoonah ba ta san a Asibiti ya ke ba tunda business trip ya ce ma ta zai je. Da aka sallameta ne Mrs Haddish ta ce su wuce wajen Zuhayr dan shima na kwance a Asibiti. Tunkafin sun isa Asibitin ta ke tunanin ko dai dalilin abinda ya faru ne ya sashi shiga tashin hankali har shima ya kwana a Asibiti...
"Why? Why?" Zuhayr ya furta yana kallon ƙwayar idon Ben yayinda idon sa ke fitar da hawaye. Gobe za a fara zaman kotu kuma duk da evidence ɗin da aka tanada evidence ne gamsassu da babu ko tamtama akai amma hakan bai sa Zuhayr ya gama gamsuwa da komai ba. Yana so ya ji ta bakin shi Ben ɗin. Ben fa da su ka taso tare, Ben da kusan babu abinda bai sani ba na sa, shine ɗanuwa guda da yake ji da shi.
"I love you, I love you so much Zuhayr. You are my one and only love but..."
"Benedict" ya furta da ɗan ƙarfi tareda dafe ƙirjin sa yayinda dukkan jikin sa ke rawa. Ba zai iya cigaba da sauraron sa ba. Komai ke dawo ma sa yanzu kaman flashback ɗin shirin film.
Tun lokacin da Alinah ke yawan ƙorafi akan Ben yana ma sa wani kallo da bai dace ba tareda yi ma sa faɗa akan kusancin su yayi yawa zuwa lokacin da Zaytoonah ta fara ma sa complain akan Ben ɗin.
"Its my fault, its my fault" abinda ya ke faɗi kenan lokacin da ya fito. Tafiya ya ke yi amma baya ganin gaban sa dan duhu ne a ko ina kafin daga ƙarshe yai yijif ya faɗi ƙasa.
Tun kafin a wuce da Ben kotu ya ke wasu abubuwa da ke nuna alamun taɓin hankali. Ya fara hakan ne saboda Lawyer ɗin sa ya ce Mr Rogers yanada footage na shi yayinda ya ke sawa Zaytoonah maganin kashe jiki a abinci sannan anga littafin da ya rubuta na hanyoyin da zai kashe Zaytoonah, kuma ciki ne aka gano cewa duk abubuwan da ke faruwa shi ne musabbabin komai. Abinda ma bai sani ba shine tun lokacin da aka tsinti wayar shi akayi bincike kuma har aka kamo hitman ɗin da ya harbe Zuhayr duk da dai ba wai sun haɗu da Ben ba ne amma information ɗin da ya basu ya gamsar da su cewa Ben ne ya hiring hitman ɗin. An nuna cewa an watsar da investigation ɗin ne saboda a samu damar tattara sauran hujjoji akan Ben ɗin cikin wannan lokacin ne kuma aka kira tsohon ma'aikacin FBI wato Mr Rogers shi kuma yai badda kama ya je ya zauna a gidan Zuhayr a matsayin mai dafa abinci. Da taimakon Allah da kuma kaifin basira da sanin aiki irin na Mr Rogers sai da aka koma kan case ɗin mutuwar Alinah da aka rufe shekaru da su ka wuce aka binciko files ɗin. Duk yadda Ben yai amfani da kuɗi wajen an rufe case ɗin ba tareda an yi dogon bincike ba sai da Mr Rogers ya gano gaskiya. Hatta Mrs Taylor matar da ta shiga gidan dan kaiwa Alinah wedding gown ɗin ta sai da Mr Rogers ya nemo ta ya ma ta tambayoyi. Akwai wanda ya ba da shaidar cewa kafin Mrs Taylor ta shiga gidan ya ga wani mutum ya fito daga gidan Alinah ya bar gidan da sauri. Footage ɗin fitowar Ben daga gidan Alinah da aka jima da cirewa sai da Mr Rogers ya nemo duk da fiskar Ben ba ta bayyana yadda za a tabbatar da cewa shi ba ne kai tsaye saboda ya saka face cap kuma kansa ƙasa haka ya wuce amma anyi amfani da na'ura wajen gano cewa Ben ɗin ne. A lokacin da aka yi case ɗin Alinah ƙasar America musulmai na fuskantar ƙalubale shiyasa ba a damu an yi dogon bincike akan mutuwar ta ba kawai aka ba da report na cewa kashe kanta ta yi.
Bayan an gama irgawa Ben laifukan sa na kashe Alinah, Linda da kuma Mr Dawson tareda ƙoƙarin kashe Zaytoonah da yai a lokuta da dama aka nemi ya amsa laifin sa sai Ben ya ƙi magana. Daga ƙarshe sai Lawyer da ke wakiltan sa ya ce yana neman kotu ta yi alfarma akan client ɗin sa domin bashida lafiyar ƙwaƙwalwa yana buƙatar kulawa.
Alkali ya yanke hukuncin kashe Ben ta hanyar rataya,.daga nan kotu ta tashi.
Lawyer ɗin Ben bai tsaya a haka ba sai da ya ɗaukaka ƙara saboda ba ƙaramin kuɗi Ben ya sa aka tura ma sa ba.
Bayan sati uku aka sake sauraron ƙaran yayinda a wannan lokaci Alkalin ya ba da umurnin a kai Ben Psychiatric dan a tabbatar da lafiyar sa kafin a zartar ma sa da hukuncin rataya.
Duk da wannan batun rashin lafiya da ake bayarwa duk strategy ne na ganin an sauya ma sa hukunci daga rataya zuwa zaman gidan yari amma kusan hauka na zahiri na shirin kama Ben ɗin. Bai taɓa yin tsawon lokaci irin haka ba tareda ya ga Zuhayr ba. Yanzu ko muryar sa ba ya ji balle ya sa shi a ido. Lawyer ɗin sa ya gaya ma sa Zuhayr ba shi da lafiya saboda cancer ɗin sa ta dawo ga kuma ciwon zuciya da ya ke fama da shi. Duk case ɗin Ben ɗin daake yi ma shi yana kwance a gadon Asibiti wannan batu shi ya sake jirkita ƙwaƙwalwar Ben. Yana tunanin taya za ayi masoyin sa Zuhayr yana Asibiti ace shi yana nan kulle, ba wannan kaɗai ba ma babban damuwar shine ita yarinyar da ya ɗau fiye da shekara yana son ganin bayanta har yanzu tana numfashi a doron ƙasa waɗannan ma shi ya fi tada ma sa hankali fiye da rasin lafiyar Zuhayr ɗin tunda ya sa a ransa ba dan Zaytoonah ba da shi ne zai zauna da Zuhayr yana jinyar sa...
***
Daga jikin gallery room su ke kallon abinda ake yiwa Zuhayr. Radiation treatment ake ma sa domin a kashe cancerous cells ɗin da su ka sake dawowa. Kwance ya ke a kan wani gado daga shi sai boxers yayinda a hankali gadon ke shiga jikin wani babban na'ura kaman wani ɗaki yayinda wani haske da ke fitowa daga wani naura da ke saman gadon ke bin dukkan ilahirin jikin sa, ya fara daga kan sa har ya kai ƙafafun sa.
Zaytoonah ta damƙi hannun Mrs Haddish da ke gefenta tana hawaye. Dada Salamatu wacce itama ke gefenta ta dafa kafaɗarta ta ce "addu'a za ki ma sa Zaytoonah"
Tun kama Ben da sati biyu aka turo Dada Salamatu dan ta zo ta dinga kula da Zaytoonah ga jinyar miji ga kuma tsohon ciki. Dada Salamatu ƙanwa ta ke wajen Alhaji Iliyasu, ba ta taɓa haihuwa da mijinta ba har ya rasu hakan ya sa kusan shekaru bakwai da su ka wuce ta dawo gidan Yayanta da zama tunda 'ya'yan kishiyarta Mata ne guda huɗu kuma dukkansu su na gidajen mazajen su.
"Muhammadu Allah ya baka lafiya" Dada Salamatu ta furta a bayyane...