Sashe 148
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasiha ya fara ma ta akan illar sata wanda ya sa ta ji jikin ta yayi wani laƙwas duk abinda ya faɗa ya shigeta.
Sai kuma ya karɓi wayan ya tura audio ɗin ya umurceta da ta goge na wayarta. Ba musu ta karɓi wayan ta goge.
"Ba na son jin wannan maganan a wajen kowa Kubrah"
Kubrah ta gyaÉ—a ma sa kai.
Har za ta tafi ya ce ta tsaya ya karɓi account numbarta da numbar wayarta, a take ya ma ta transfer ɗin dubu ɗari. Ya ce ta ji tsoron Allah ta dena sata ta kuma nemi halal.
Bayan tafiyar Kubra Galadima ya saurari audio É—in nan ya fi sau biyar. A hankali kuma sai zargin da ya ke yi akan Ghazala su ka fara zama gaskiya. Kafin tafiyar su Las Vegas akwai ranan da ya tsinkayi Raziya na faÉ—awa Ghazala za ta tona ma ta asiri idan ta sake dukan ta a gidan nan. A lokacin Ghazala da ta hangoshi sai ta buge da dariya tana É—an dafa kafaÉ—ar Raziya tana faÉ—in "kin iya acting sosai"
Daga baya ya samu Raziya a gefe akan wani asiri ta ke son tonawa Ghazala amma ta ce babu wai suna gwada acting scene É—in wani film ne. Bai yarda da ita ba amma sai yai shiru da zancen.
Raziya ta yi hakan ne saboda tsoratar da ita da Ghazala ta yi akan indai gaskiya ta fito har da ita za su raba hukuncin Galadima tunda ta san ya tsani ƙarya. The way Ghazalar ta tsara maganganunta ya sa Raziyar ta ji tsoron faɗawa Daddyn su gaskiya.
Bai wani jima da tafiyar Kubra ba shima ya fita daga office ɗin ya wuce makarantar su Raziya. Zuwa yai wajen principal ya sa aka kira ma sa ita. Lokacin da ta fito ta ga Daddyn ta a office ɗin principal maimakon ta ji daɗi sai tsoro ya mamayeta. Daddy bai taɓa zuwa school ɗin su haka ba.
Godiya yai wa principal ɗin sannan ya miƙe ya fita Raziya ta bi bayan shi ƙirjinta na dukan uku-uku.
Office É—in sa su ka wuce. Tun a mota Raziya ta tambayeshi mi ya ke faruwa, amma ya nuna ma ta ba komai akwai abinda za ta ma sa a office É—in ne.
Bayan ta zauna, ya sa aka kawo ma ta maltina mai sanyi amma ta ce ruwa kawai za ta sha. Sai da ya tabbatar ta nitsu kafin ya kira sunan ta a hankali "Fatima"
Duk lokacin da ya kirata da sunan Fatima to he's in a very serious mood.
"Yes Daddy" ta faɗa tana ƙyafƙyafta ido.
"Zan miki wata tambaya and i want you to answer me with absolute truth. Idan kika min ƙarya Fatima zan mugun saɓa mi ki. I want to hear only the truth"
Gumi ne ya fara tsatstsafo ma ta hannunta da ta dunƙule sai rawa ya ke yi.
"Wani sirri ki ka sani gameda Hajiyar ku?"
Raziya ta ƙwalalo ido waje lokaci guda kuma ta fara jera hiccups akai-akai. Ruwan da ke gaban ta ya ɗauka ya miƙa ma ta, ta karɓa ta sha.
"Ina jin ki"
"Daddy i'm sorry" ta faÉ—a tareda fashewa da kuka.
Da farko lokacin da Raziya ta fara magana ya ɗauka maganan da zai ji makamancin na Kubra ne but it took him offguard lokacin da ta sanar da shi gameda tsoratar da Zaytoonah da su ka dinga yi har ya sa ta hauka. Tana maganar tana kuka tareda roƙon shi akan ya yafe ma ta. Ta yi haka ne saboda ba ta son Zaytoonah a lokacin.
"But now i like her Daddy, i really like her. She's a good person. Ta fi Hajiya kirki"
Goge ma ta hawayen fiskarta yai ya ce ta dena kuka shikenan komai ya wuce.
Lokacin da ya ce ta je driver ya maida ta school cewa ta yi "Daddy please don't punish me"
"Ba abinda zan miki tunda kin faÉ—a min gaskiya. Je ki kawai"...
Ranan bai koma gida da wuri ba, yayita jujjuya abubuwa dayawa a ran sa. Abu na farko da ya zo ma sa shine ya rabu da Ghazala a take, but sai ya chanja ra'ayi yana so ya ga how far Ghazala za ta je saboda baƙin kishi ko ya ce son zuciya. He took a deadly risk, but its worth it.
Lokacin da ya je gida bai nuna komai ba. A ɗakin Zaytoonah ya ke shiyasa ma ya ƙara danne ran sa dan kar ta gane akwai matsala.
Washegari kuwa Ghazala ta karɓi girki. Tun kafin ya bar office a jiyan su ka yi magana da Ahmad akan how fast zai saka mi shi camera a ɗakin sa. Lokacin da Zaytoonah ke yawan maganan tana ganin Ben especially lokacin da ta yanki Raziya shine ya sa aka sa ma sa CCTV footage a gidan. But bayan Mommy ta tafi da Zaytoonah sai kawai ya cire na ɗakunan ya bar na falo, corridor, kitchen da waje.
Da safe kusan ƙarfe shaɗaya su ka dawo gidan shi da Ahmad da wani abokin Ahmad ɗin bayan ya samu tabbacin Ghazala ta tafi Shagon ta. Ɗakin sa da na Ghazalar aka sawa camera, bayan sun tabbatar komai ya tafi dai-dai sannan su ka bar gidan. Da ke Zaytoonah ma ta tafi saloon dan haka ba wanda ya san abunda aka yi. Maman Tope da ke gidan kuwa ba ruwanta da gulma, da kaman Atika ce da magana ta tafi kunnen Ghazala.
Lokacin da ya dawo daga office Ghazala sai wani rawan kai ta ke yi. Ta yi kwalliya sosai tana fidda ƙanshin different turaruka da ta fesa. Bayan sun gama cin abinci ya ce zai ɗan yi aiki a study room ɗin sa.
Wannan ne ya ba ta daman saka layar a ƙasan pillow da ke gefen da ya ke kwanciya.
Duk abinda ta ke yi yana gani a computer, hatta wajen da ta saka gashin na sa a jikin layar ya gani. Abun kaman a film. Yana tunanin É—azu da su ke cin abinci ne ta samu daman cire gashin.
Ko kaɗan bai tsorata ba dan yayi imani ba abinda zai sameshi. Tun jiya ya sa aka ma sa sadaka a wajaje da dama. Ya kira wani Malamin sa da ya ke ɗaukan karatu a wajen sa duk lokacin da ya ke Zaria ya gaya mi shi halin da ya ke ciki. Malamin ya ce kar ya damu ya sa a ran sa ba abinda zai sameshi sai da yardar Allah. Ya ce idan ya ga layar yai Bismillah ya taɓa, alkadarin jikin sa zai warware gaba ɗaya.
Ghazala ta zauna zaman jiran Galadima zuciyarta na dukan tara-tara saboda abu ne da ba ta taɓa yi ba. Burinta kawai abin nan yai ma ta aiki yadda ta ke so. Bayan kaman minti talatin sai Galadima ya shigo ɗakin.
"Abu Razz akwai aiki gobe fa ba za ka zo ka kwanta ba"
Ya kalli agogo shaɗaya har da rabi da minti biyu. Ya ce bari ya ƙara watsa ruwa dan zafi ya ke ji.
Har zai shiga banÉ—akin sai kuma ya juyo ya ce ta É—auko ma sa ruwa ya manta bai sha maganin sa ba.
Da ta je falon ta duba fridge sai gashi akwai fruits da lemo amma ba ruwa, wanda Galadiman ne da kan sa ya kwashe ruwan ciki. Dan haka dole ta sauka kasa babban falo kafin ta É—auko ruwan.
Bayan fitan Ghazala daga ɗakin ya je ya ɗaga filon sama sai ga layar da aka ajiye. Ba tareda tsoro ba yai Bismillah ya ɗau ka layar ya ƙare ma ta kallo kafin ya ɗau wayar sa ya ɗauka hoton layan kafin ya mayar da layar yadda ya same ta. Ya wuce banɗaki yana jinjina wannan al'amari. Bayan ya watsa ruwa sai da ya haɗo da Alwala kafin ya fito.
Lokacin da ya fito Ghazala ta dawo. Ya karɓi ruwan da ta kawo ya sha magani, sannan ya ɗauko Sallaya ya tada sallah. Yai addu'ar Allah ya kare shi, 'ya'yan sa da kuma Zaytoonah daga sharrin Ghazala. Kafin ya idar Ghazala kaman ta je ta shaƙe shi tsabar haushi. Ta sani Galadima mutum ne mai yawan yin nafilfilu amma yau kan haushin sa ta ji da ya fara sallan.
Lokacin da ta ga ya sa hannu yana kaɗe gefen sa kaman ƙirjinta zai fito saboda bugun da ya ke yi da ƙarfi. Gani ta ke kaman zai ce zai ɗaga filon sai kuma ta ga kaɗewar kawai yai sau uku kamar yadda Manzon Allah ya faɗakar.
Sai da ta ga ya kwanta akan filon kafin ta ji hankalinta ya kwanta.
Galadima baccin sa mai lafiya yai yayinda Ghazala ta yi bacci rabi da rabi.
Da Asuba da ya fita masallaci ta cire layan ta kai ta ɗakinta ta ɓoye akan zuwa da safe sai ta je ta bisine.
A ranan da ya mu su maganar zai raba mu su gida Ghazala ta fara gwada sa'arta akan lallai sai dai Zaytoonah ta zauna a gidanta da ke Zuba. Jin bai musa ba ya sa ta ƙara tabbatar da aikin layar da aka ba ta.
Yanzu ma maganar honeymoon da ta ma sa na sati uku da ta shirya kafin Azumi bai mu sa ma ta ba ya ce duk inda ta ke so su je za su je.
Abinda ta shirya ba wai honeymoon ɗin ba ne. So ta ke su je a ma ta artificial insemination. Dan da gaske ta ke yi sai ta haihu da shi, not just haihuwa but haihuwar namiji. Tunda natural way ya ƙi yiwuwa gara kawai ayi hanyar bature. Tunda ta same shi a hannu ta yi imanin idan su ka je ba zai ma ta mu su ba idan ta gaya ma sa ainihin dalilin tafiyar ta su sai dai kash...
***
Lokacin da su ka iso Zaria maimakon su tafi gidan su sai Ghazala ta ga sun yi hanyar anguwar su Hajia Abu.
"Abu Razz ba gida za mu fara zuwa ba ne?"
"Na fi so mu fara zuwa sallaman yanzu, kinga zuwa yamma mun dawo gida sai kawai mu huta tunda gobe za mu koma"
"Hakan yayi gaskiya"
Yayi murmushi, irin murmushin da ke nuna cewa akwai sauran rina a kaba.