Sashe 9
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru-shiru yana ta tsumayin dawowar Nkiru amma shiru har yamma lis babu alamun ta hakan ya sa ƙarfe shida na yi ya wuce gidan su Okafor. Yana zuwa ya samu Iyayen Okafor da ƙannen sa amma babu Okafor da Nkiru. Wai ba su dawo daga church ba, hankalinsa ya tashi wani irin church ne tun safe har dare. Ya bar gidan ransa a ɓace ba tareda ya mu su sallama ba. Ya san church ɗin ai, zai je koma miye ne ya ga ni. Sai dai ko da ya je an tashi, church ɗin ma a kulle ya ke. Kan sa wani juyawa yai ya fara jin wani jiri-jiri. Ba abunda ya hango irin hoton Okafor da Nkiru tsaye ana ɗaura mu su aure gashi har Okafor ya sa ma ta zobe. Bai san ya aka yi ya bar church ɗin ba ya dawo gida, da ƙyar ya je yai sallar Magariba, da ya dawo ya sake leƙa ɗakin Goggo amma su ka ce ba ta dawo ba. Ya fito ƙofar gida yana dakon dawowanta lokaci zuwa lokaci yana duba agogo.
Bayan ya dawo daga sallar Isha ne da ya leƙa ɗakin ya ganta zaune tana naɗe kayan da ta cire.
Tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa ma mi zai ce ma ta. Ga shi fiskarta ko alamun ta damu da daÉ—ewar da ta yi bai ba.
"Nan gaba ki dinga dawowa da wuri" ya faɗa yana danne ɓacin ran sa. Ta fara ma sa bayanin dalilin da ya sa ba ta dawo da wuri ba. Pastor ne ya buƙaci ganinta shine Okafor ya kaita gidan sa bayan an tashi daga church to shine bayan sun ci abinci ya tambayi labarinta ta gaya ma sa shine yai ma ta addu'a tareda cewa ta dawo gidan sa da zama ko kuma gidan su Okafor saboda za ta fi samun nitsuwar yin Bauta.
Tunda ta fara bayani ya ke kallon ta yana jin wani fargaba na taso ma sa musamman ma da ya tuna hasashen da yai É—azu.
Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tareda ya ji ƙarashen bayanin ba.
Ta ɗauka abu zai je ya yi ya dawo amma har ta yi bacci bai dawo ba. Washegari da ya zo ya gaishe da Goggo ba ta tashi ba saboda gajiya sai kusan ƙarfe takwas ta tashi. Wasa-wasa har rana ba ta ga ko ƙeyar T J ba. Muntari ne ya shigo ya ma ta sallama akan zai wuce Kano, sai da ta sha dariya sosai saboda turancin sa. Shi kuwa ganin tana dariya sai ya dage yana ta zuba labari. Da zai tafi har da ma ta alƙawarin zai dinga zuwa duk sati yana dubata, shi da ya ke tafiya yai wata ɗaya biyu bai leƙo gida ba amma yanzu wai zai dinga zuwa duk sati.
Yammacin ranan Okafor ya zo gida ya aiko aka kirata. Gidan pastor su ka je, wannan karan ma ƙoƙarin convincing ɗin ta su ke akan ta bar gidan su T J amma ta ƙi cewa ta yi idan ta bar gidan su T J ba ta mu su adalci ba.
Su kuwa su Pastor sanin gidan ne ya sa su ke tsoron zamanta a gidan musamman saboda sashin Modibbo da ta ke zaune. Zamanin Modibbo anyi babban malami, 'yan uwansa kaf É—in su kiwo da noma su ka ba wa muhimmanci amma shi karatun addini yai mai zurfi shiyasa ma ake kiransa da Modibbon saboda malami ne masani sosai akan addini. A zamanin sa ya yi sanadiyar musuluntar da mutum tara. Tsoron su kar zaman Nkiru a gidan ya sa ta musulunta duk da kuwa yanzu babu Modibbo a gidan.
Ita dai duk yadda su ka yi da ita ta ƙi, ƙarshe su ka fito ma ta da wani salo akan ta dinga zuwa tana yini da su saboda su san juna sosai. Ba tareda ta kawo komai ba ta amince da hakan. Da za su tafi Pastor ya ja Okafor gefe ya ƙara jaddada ma sa akan maganar su ta jiya.
Ƙarfe tara ya wuce lokacin da su ka iso ƙofar gidan. Hamma Tijjani na cikin wasu abokanan sa ana hira amma shi hankalinsa na kan hanya yana baza ido ya ga dawowar Nkiru, ya ga fitan su ɗazu da ya ke dawowa daga masallaci.
Hango su da yai ya sa shi tashi ya shige gida. Baccin kirki bai iyayi ba, yana so yai baccin ko dan ya samu sauƙin abinda ke damunsa amma ya ka sa. Yana son mata magana amma bai san mi zai ce ba, duk yadda ya juya abun shine bai da gaskiya Nkiru na da daman komawa gidan su Okafor saboda ɗan uwanta christain ne kuma yaren su ɗaya duk da sun zo daga gari mabanbanta. Amma kuma bai yarda da Okafor ba, to miye na shi a ciki tunda ita ta zaɓe shi sama da shi. Haka dai yai ta tunani kala-kala har daga baya bacci ya sace shi.
Washe gari da ya shigo gaishe da Goggo ne Nkiru ta tambayeshi ina ya je jiya bai leƙo ta ba. Wani kallo ya watsa ma ta sannan ya tashi ya fita. Jikinta yai sanyi ta lura kwana biyun nan baya kulata amma ta rasa dalili. Ƙarshe ta fara zargin ko ya fara gajiya da ɗawainiyar da ya ke ma ta ne, sai kuma ta yi saurin kauda zancen da cewa Teejay ba zai yi ma ta haka ba.
Da rana ya dawo daga sallar Azahar ya shigo É—akin Goggo ta ce ma sa Pendo da Nkiru sun fita za ta raka Nkirun kitso. Ba su gama zancen ba sai ga Pendo ta shigo É—akin. Ganin ita É—aya ne ba Nkiru ya sa T J tambayarta ina ta bar Nkirun. Pendo ta ce ma sa sun je gidan kitson ne matar ta ce ba za ta yiwa Arniya kitso ba, wai ance idan ka yiwa Arniya kitso kana da zunubi. T J girgiza kai da jin jahilcin mutanen na sa. Ya ce "sai ki ka bar ta a ina?"
"Mun kusa isowa gida ne mu ka haÉ—u da abokin ka shine ta bishi"
"Okafor?" Ya faÉ—a a fusace
Ta gyaɗa ma sa kai. Da sauri ya fice ɗakin Goggo da Pendo su ka bi shi da ido. Sai da yai tafiya mai nisa kafin ya tsaya. Zuciyar sa ce ta faɗa ma sa babu amfanin zuwa gidan su Okafor, Nkiru da kan ta ta bishi miye na shi a ciki, idan ma gaba ɗaya za ta koma chan kaman yadda Pastor ɗin su ya buƙata ai ba matsala ba ne. Haka ya juya ya koma gida zuciyar sa na tafarfasa. Ranan ma dai bai sake kulata ba, sai dai duk da haka hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga ta dawo gida kusan ƙarfe biyar na yamma.
Da safe da ya shigo ma tana gaishe shi haka ya amsa ko kallon ta bai yi ba. Goggo tana lura da shi kwana biyun nan yadda ya ke share Nkiru. Ba ta dai ma sa magana ba ne amma yau kam ta kasa yin shiru.
"Barkindo yarinyar nan ta ma ka laifi ne?"
Duk da ya san wa ta ke magana akai amma ya dake ya ce "wa ce yarinya kenan?"
"Ungo na ka Barkindo"
Yai dariya ya ce "Goggoji na cewa ki ka yi yarinya, zai iya zama Asma'u, Pendo, Kulu, Hadiza... kai yara mata a gidan nan ai dayawa"
Ganin ya raina ma ta hankali ya sa ta ce "koma wacece dai abu ɗaya zan gaya ma ka. Ka ga kai ka kawota garin nan kuma a duk faɗin garin nan babu wanda ta yarda da shi sama da kai. Idan har za ka dinga nuna ma ta fushi ba tareda ka sanar da ita laifin da ta yi ba za ka sa yarinyar ta tsaneka. Kwana biyun nan kullum sai ta yi kuka ko mi ya ke damunta na san ya na da alaƙa da kai. Idan laifi ta yi ka gaya ma ta sai ta gyara amma sai ka shigo min ɗaki kana ta kumbure-kumbure, ba abinda hakan zai haifar"
"Ni ba na fushi da kowa"
"Tashi ka bani waje, Ja'iri"
T J ya fita yana dariya.
Tana ganin ya fita ta fara matsa ƙwallan da ya taru ma ta. Miyasa ita kaɗai ne ya ke ɗaurewa fuska? Rabon da ya ma ta murmushi tun ranan christmas...
***
"Asma'u tashi ki kai wa Hamma ki ce ya zo ya tambayi boÉ—É—iyon sa ko za ta sha furan na ga sai kallona ta ke lokacin da na ke damawa"
Yarinyar ta tashi tana ɗan kumburi dan ba a fara bata na ta ba sai na Hamma Tijjani ta ɗau ƙwaryan ta fice da sauri. Ba ta jima ba ta dawo da ƙwaryan wai ba ya ɗaki.
Asma'u ta ɗau na ta ta fara sha. Goggo ta miƙawa Nkiru nono da fura wanda tunda ta fara damawa ta zuba ido tana kallon duk wani motsinta.
Suna sha Goggo ta tsinkayi muryan T J yana yiwa kakar sa Yawuro tsiya. Maganar aure ta ke masa shi kuwa ya dage ita zai aura.
"Maza tashi ki kai ma sa ya dawo"
"Assalamu Alaikum, ga ni nan a bani rabona"
Ta ce an duba shi É—azu baya É—aki.
"Asma'u tashi ki kai ma sa"
"Batta tasha a hankali, Nkiru za ta kawo min"
Yai wa Nkiru magana akan ta É—auka ma sa kindirmon. Ta tashi da sauri ta É—auka ta bi bayan sa.
Tana ajiye ƙwaryan ya kira sunan ta a hankali "Inkiru" ta ɗaga jajayen idonta ta kalle shi.
"Will you like to taste it?"
Ta gyaÉ—a ma sa kai da sauri
Ya buɗe ƙwaryan ya ɗau ludayin da aka ɗaura a kai ya ɗebo kaɗan ya kai saitin bakinta. Ganin ta tsaya tana kallon sa ne ya sa shi gyaɗa ma ta kai hakan ya sa ta buɗe bakinta ta ɗan kurɓi furan.
"You like it?"
"Its sugary" ta faÉ—a tana murmushi
"Bafulatanin kenan" ya faÉ—a yana murmushi shima