← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 161

Sashe 40

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zan iya ba Barkindo. Ba zan Iya ba. Mahaifiyar ka ba ta sona na sani amma ba ta isa ta dinga wasa da hankalina ba, ba ta isa ta dinga juya rayuwata ba. For God's sake Barkindo ita fa ba Allah ba ce da za ka ce za ka dinga bin maganan ta from A-Z koda kuwa maganar tan son zuciya ne. This time i wont accept this injustice ko da kuwa hakan zai sa na rabu da kai i'm ready to do it. Haba, Haba kai fa ba yaro ba ne da za ta dinga ma ka barazana da cliche saying "zan tsine ma ka" to ta tsine ma kan mu gani"

Ba ta jira mi zai ce ba ta fice daga É—akin dan idan ta biye shi sai ta faÉ—i abinda za ta iya danasanin sa daga baya. Haba ita Iya kullum ba ta son zaman lafiyar ta da Tijjani gashi aure yanzu har da 'ya'ya.

T J barin ta yai bai sake maganan ba a ranan dan ya san ta É—au zafi ba za ta fahimce shi ba. Washe gari ta kasance Lahdi bayan yaran sun tafi Islamiyya tana wanke-wanke a kitchen ya zo ta bayanta ya rungumeta ya kissing wuyanta ya ce "I love you Maryam"
Ba ta kulashi ba dan har lokacin haushin sa ta ke ji.

"Ki yi haƙuri, i know its not fair. Amma Iya is my mother kuma kin san ta tsufa, and na yarda akwai jahilcin zamantakewa da kuma addini a tattare da ita but still..."

A fusace ta juyo ta kalli cikin idon sa ta ce "idan ba za ka iya gaya ma ta ba ni zan gaya ma ta. Enough is enough, idan na cigaba da aiki ta haÉ—iye zuciya ta mutu ni ba damuwata ba ne. I dont care"

"Maryam please"

"Idan ka na sona yadda ka faɗa you'll fight for me. So na wa aiki na yana rufa ma na asiri ta wani wajen? So nawa na ke representing mutane kyauta a kotu duk dan na taimaka mu su a bi mi su haƙƙin su su zo nan gidan su yi ta min addu'a. Idan ka ce na bar aikin nan Tijjani tamkar ka yadda karuwanci na ke yi kamar yadda Iya ke faɗa"

"Nooo Maryam, Nooo"

"Then kar ka roƙeni dan ba zan bari ba even at the expense of our marriage"

Ya rasa bakin magana dan tunda Maryam ta faɗi haka to da wuya ta chanja ra'ayinta shi tsoron sa ma kada ya kuma yin magana ta tattare kayanta ta bar gidan kamar yadda ta taɓa yi...

Yana kwance a ɗaki yana tunanin yadda zai ɓullowa lamarin wayar sa ta fara ringing. Ɗazu ya ga Maryam ta sa hijabi ta fita ya ɗauka za ta je ta siyo abu ne.

Hanne ce matar Muntari ke kiran sa. Ya É—auka kiran tareda sallama.

"Hamma Tijjani ka zo gidan mu Anty Maryam da Iya su na faÉ—a"

Innalillahi ya faɗa ya miƙe da sauri ya fita.

Maryam kam zuwa ta yi gidan Muntari dan ta jaddadawa Iya ta fita harkanta ta sake ma ta mara ta yi fitsari.
Zuwanta ta samu Iya na cin ferfesun kaza tana ci sanyin AC na ratsata tana kallon wani chinese film irin na da É—in nan wanda za ka ga ana faÉ—a a saman bishiya ana tafiya a kan iska.

Daga fara magana Iya ta ce indai ba karuwanci ba miyasa ta ke tuƙa mota Alhalin T J bai da mota. Martanin da Maryam ta bayar ne ya sa Iya ta tashi ta tsinkawa Maryam ɗin mari ita kuwa ta cigaba da kiranta jahila.

"Wallahi ki koma Islamiyya ki ɗau karatu dan jahilci babban cuta ce. Dan na riga mijina hawa mota sai ya zama karuwanci na ke yi? Kin min ƙazafi, kin min sharri ki ji tsoron Allah Iya, dan idan ban yafe ba wallahi za ki sha azaba a kan haka ranan gobe"

Ita kuwa ta fara tafi tana ahayye wai har Maryam Inyamura ce za ta ma ta wa'azi lallai ƙarshen duniya.

"Ba zan tsaya magana da ke ba dan ba ki kai na yi jayayya da ke ba amma kisani ƙazafin da ki ke min Allah zai tambayeki, ki tambayi Malamin da ki ka yarda da shi, ki nemi duk wanda ki ka yadda da fatawar sa zai gaya mi ki babban zunubin da ki ke ɗauka wa kan ki"

Ta juya za ta tafi Iya ta ce "Ni dai Allah ya isa da É—ana ya haÉ—a shimfiÉ—a da Karuwa kuma Kwartuwa"

Kalmar kwartuwa shi ya tinzira Maryam fiye da karuwan da ta ce.

Tana juyowa ta yanke Iya da wani mahaukacin mari dai-dai nan T J ya shigo gidan kuma ya ga marin da Maryam ta yi. Duk lalacewar mahaifiyar sa ya sani Maryam ba ta da ikon marin ta.

"Maryam" ya daka ma ta tsawa. Yana ƙarasowa ya wanketa da mari ya ce "you dont have any right to slap her Maryam, ka da ki sake"

Iya na ganin haka ta fashe da kuka tana faÉ—in "Allah ya kawo mu zamani da matar É—a za ta mari uwar mijin ta. Tur da wannan zamani, Tur da wannan aure, Tur da É—an da ya zauna da irin wannan mata"

A hankali ta buÉ—e idon ta ta É—aura su a kan na T J da yai jaa zur. Tunda ya mareta idon ta ke rufe saboda yadda shock É—in marin ya shigeta.

"Barkindo"

"Shhhhh ki koma gida" ya faɗa yana nuna ma ta ƙofa

"Ba inda zan je sai ka sawwaƙa min. Ka ji dai mi mahaifiyar ka ta ce "Tur da kai idan ka zauna da ni" dan haka i'll only leave when you divorce me because i can take it anymore"

"Ki je za mu yi magana idan na dawo"

Dariya ta fashe da shi dan yau kam tana jin kan ta a Barrister Maryam Nkiru Uzodinma É—in ta.

"Wani cin mutunci ne ba a min a gidan ka ba Tijjani? Wani haƙƙi ne ba a tauye mun ba? Ka tuna lokacin da mahaifiyar ka da yayarta su ka zo da wani mahaukaci wai Sarkin Mayu su ka sa shi ya jibgeni kamar jaka? No, ka tuna lokutan da na ke karɓan girkin Hajjo na yi saboda tana laulayi? Ka tuna yadda na yiwa yaran Hajjo hidima amma lokacin nawa aka ce min Zaytoonah shegiya ce babu wanda ya ke ɗaukan ta balle a taya ni reno. Ka tuna lokacin da ka yi gini aka hanani komawa gidan? Ka tuna lokutan da ake cewa karuwanci na ke zuwa yi a Abuja. Ko ka manta yadda ta ke fifita Humairah akan Zaytoonah to the extend Adaeze ba ta san mi ake nufi da wasan Kaka da Jika ba. Wanne ne ban faɗa ba? wanne na manta ban faɗa ba? tuna min Tijjani, tuna min."

Girgiza kai kawai T J ya ke yi saboda abubuwan da ya ke ji suna fitowa daga bakin Maryam wanda ya sa shi cikin tashin hankali da tsantsar nadama.

"Ba ka taɓa tsaya min ba, kullum sai dai 'Maryam i know its not fair but ki yi haƙuri, I love you' to yau haƙuri na ya ƙare, ba zan iya zama ana tauye min hakki ba"

Ta kalli Iya ta ce "Hajiya Iya ba zan taɓa yafe miki ba. Duk wani ƙuntatawa da ki ka min ban yafe ba, ban yafe ba ƙazafin karuwanci da ki ke min har rana ita yau, ban yafe ba shegenta min Zaytoonah da ki ka yi, ban yafe ba shegenta min 'yan biyu na da ki ka yi"

"Mmmmaryam" T J ya faɗa murya na rawa. Bai gane maganganan ta na ƙarshe ba, wa su 'yan biyu kenan?

"Da ni da mahaifiyarka za mu haɗu a gaban Allah Tijjani. Ko a kafira ka aureni iya abinda zai sa Mahaifiyar ka ta tsaneni kenan balle ina musulma, i didnt deserve this treatment. Musulmi ɗan uwan musulmi ne haka ka koyar da ni amma mahaifiyarka ta jahilci hakan. For 21yrs da mu ka yi aure Mahaifiyar ka ba ta taɓa mutuntani ba, is it because Musulunta na yi? Is it because na fito daga ƙabilar Igbo?, or is it because kana sona despite ni ba Bafulatana ba ce?. A yau zan bar gidan ka Tijjani. Ka je Iya ta sa ma ka albarka kar ka lalace, ka je ka haƙura da ni kar tsinuwar Iya ya kamaka dan aiki kam yanzu na fara. But let me tell you one thing, indai akwai hakkina a kan Iya to daga yau har ƙarshen rayuwarta ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. And as for your crazy brother idan ya sake zuwa kusa da ni da niyyar yin wani abu zan kashe shi"

Hannunta ya kamo yana kiran sunan ta a hankali, ta wafce hannun ta ce " barin gaya ma ka gaskiya. I regret meeting you, i regret following you that day, i regret saying YES to marrying you, i regret the night you make me a woman, i regret every single moment i spend with you, i regret loving a man like you Tijjani Abubakar Modibbo..."

Zuwa lokacin kuka ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarisa faɗin abinda ta yi niyya.
Juyawa ta yi za ta bar wajen ya damƙe hannunta da ƙarfi.

"Maryam what twins? Wwwwhat twins?" Ya faɗa yana hawaye jikinsa na ƙyarma.

" Au Iya ba ta faÉ—a ma ka ba, ashe kai ma tana munafurtar ka kenan. To bari ka ji Lokacin da ka tafi Oxford i was pregnant and that's when Muntari came back, he tried to rape me and while struggling with him he pushed me and i hit my stomach so hard that i end of loosing my 3months old twins. My twins Tijjani, our twins. And when i told your mother ta shegenta min su, ta ce ba cikin ka ba ne, ta ce ni kwartuwa ce, ta ce..."
Chapter 40 · 0% Book details