← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 161

Sashe 52

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shepherd pie É—in da aka yi aka yanka shi kashi shida kowa aka sa ma sa yanka É—aya a plate ya saura yanka É—aya a glass bowl É—in. Zuhayr ya sa sokali ya É—au sauran ya É—aura shi a plate É—in Zaytoonah. Kallon sa ta yi ta na kumbura baki, yanzu ya nunawa Kakanninsa ita acici ce. Shi kuwa ko a jikin sa ya zauna ya fara cin na shi.

Yadda pie ɗin ya ma ta daɗi kuwa tas ta cinye tana lumshe ido, da da ƙari ma za ta ƙara, ashe dai gara da Zuhayr ɗin ya sa ma ta ɗaya slize ɗin, da slize ɗaya ta ci ba inda zai je. Su turawan nan sai su riƙa cin abinci kamar yara ƙanana.

Bayan sun gama cin abinci Kakannin Zuhayr su ka ce za su nuna ma ta gidan gonan su wanda a ciki aka haifi mahaifiyar Zuhayr, a nan tayi ƙuruciyarta har ta girma.

Wajen Shanu su ka fara zuwa, ta ga yadda ake tatsar nono da inji ba da hannu ba. Su ka je wajen Kaji ma ta gan su dayawa, wajen dawakai su ka wuce inda tuni su Zuhayr da Ben suna kan doki su na gudu.

Bayan sun iso wajen da su ke tsaye sau su ka tsaya.

Kallon su ta ke yi cike da sha'awa.

Mr Haddish ya tambayeta ko za ta hau dokin, ta gyaÉ—a kai.

Zuhayr ya ce "kin taɓa hawa doki ne?"
"There's always a first time"
Bai ce komai ba ya sauka ya taimaka ma ta ta hau, yana riƙe da linzamin dokin, Zaytoonah ta ce Mrs Haddish ta mu su hoto. Bayan anyi hoton da wayar Mr Haddish sannan ya fara jan dokin a hankali suna tafiya. Zaytoonah baki kamar zai yage tsabar dariya an hau doki. Sun ɗan yi nisa kaɗan Zuhayr ya tsaya saboda wayar sa da ke ringing ya tsaya amsa wayar ya sake linzamin ba tareda shi ko Zaytoonah sun lura ba Ben da ke gefe shima akan doki ya zaburar da dokin da Zaytoonah ke kai, nan da nan dokin ya hau gudu. Ihu Zaytoonah ta fara ganin yadda doki ke sheƙa gudu da ita.
"Mommy, Mommy, Zuhayr, Zuhayr help, somebody help" Dif sai ga ta a ƙasa dokin ya yarda ita cikin ciyawa.
Har su Zuhayr su ka iso inda ta ke ba ta ihu ba.
Ya miƙa ma ta hannu dan ya taimaka ma ta ta tashi ta saka kuka tana kiran ƙafarta.
Girgiza kai yai ya sa hannu zai É—auketa Ben ya tareshi.
"Ba za ka iya É—aukan ta ba, tanada nauyi, kuma daga nan zuwa gida akwai nisa"

Zai yi magana ya ce bari ya kira azo a ɗauketa da mota. Zaytoonah ganin ba wanda ya kulata ya sa ta cigaba da kukanta tana kiran ƙafarta.

Maimakon Mota Amalanken shanu ne ya zo. Zuhayr da Ben su ka cicciɓeta su ka sa ta a bayan Amalanken. Zuhayr ya zauna da ita yana ma ta sannu haka aka ƙarisa da su ƙofar gidan. Ben a doki ya biyo su amma idon sa ƙyam akan Zuhayr saboda ko kaɗan baya so jikin sa ya raɓi na Zaytoonah sai dai idan dole ne.

Ɗaki aka kwantar da Zaytoonah ana tambayar ina ne ke ma ta ciwo amma ta ƙi faɗa sai kuka. Mrs Haddish ta kira Likita wanda bayan minti shabiyar sai gashi ya zo. A gaban su ya fara duba ƙafan Zaytoonah inda ya ga targaɗe ta samu a ƙafan na ta, sai kuma gefen bakin ta da ya ɗan fashe. Bayan ya ma ta duk abinda ya dace ya ce ta huta kada ta yi amfani da ƙafar yau, zai zo gobe da safe ya ƙara dubawa.

Tsofin sai sannu su ke ma ta kamar su suka sa ta hawa dokin. Shi kuwa Ben ya so raunin da Zaytoonah ta samu ya fi haka.

Su da su ka zo da niyyar ba za su kwana ba sai ga shi za su kwana. Ben ba yadda bai yi da Zuhayr ba akan su koma Vegas idan ya so gobe sai ya aiko Driver ya ɗauko Zaytoonah amma ya ƙi ya ce Zaytoonah respinsibitity ɗin sa ce yanzu.

"Ka chanja plan ɗin ka ne?" Ya tambaya cike da fargaba dan ya san deal ɗin da Zuhayr yai da Zaytoonah. Zuhayr ya girgiza kai ya ce "a'a, na ɗauketa ne kamar ƙaramar ƙanwata ka ga kuwa dole na kula da ita. Besides na yiwa mahaifiyarta Alkawarin kula da ita kuma ka san ba na wasa da alƙawari"

Ben ya gyaÉ—a kai cikin gamsuwa da bayanin abokin na shi.

Ɗakin da Zaytoonah ta ke Mrs Haddish ta tura Zuhayr ta ce ya kwana da ita kar ta buƙaci wani abu cikin dare. Kamar ba zai yarda ba sai kuma ya amince da hakan, Ben yana gefe ya kumbura yayi fam kamar zai fashe. Yana gani Zuhayr ya buɗe ƙofa ya shiga ɗakin da Zaytoonah ke kwance.
Lokacin da ya shiga ɗakin ma Zaytoonah ta yi bacci, ya ƙarisa gareta ya gyara ma ta bargo sannan ya koma wajen kujera ya kwanta...

***

Muhammad Ilyas ɗa ne ga Alhaji Iliyasu Mai Auduga wani fitattaccen attajiri wanda ya ke da gonakan Auduga. A lokacin da Nigeria ke taƙama da Albarkatun Gona irin su Auduga, Gyaɗa, Robber, Cocoa, etc wajen samun kuɗin shigar ta. Alhaji Iliyasu na ɗaya daga cikin wanda su ke fita da Auduga ƙasashen waje.

Matan Alhaji Iliyasu biyu ne Hajiya Nenne da Hajiya Saudah. Hajiya Nenne sai da su ka shekara goma da ita kafin ya auri Hajiya Saudah 'ya'yan su uku Mata da Hajiya Nenne. Ita kuma Hajiya Saudah a shekarar farko da auren su ta haifi namiji aka sa ma sa Muhammad bayan shi sai da ta haifi mata uku kafin ta haifi Aliyu. Ita kuwa Hajiya Nenne ta haifi namiji sau É—aya bai zo da rai ba dan haka yaranta shiida duka mata ne.

Da ke Muhammad ne ɗa namiji na farko a wajen Alhaji Iliyasu sai ya zama yana nuna ma sa tsananin so. Ko kaɗan baya so a taɓa shi yanzu za ka ga ya hau faɗa. Bayan ya ƙare karatun secondary a Nigeria ya tura shi karatu a Harvard da ke Ƙasar America. Rayuwar turawa ya chanja Muhammad sosai, shine giya shine neman Mata. Ba shi da matsalar kuɗi tunda mahaifin sa yana tura ma sa. Bayan ya ƙare karatu Mahaifin sa ya buƙaci ya dawo ya dafa ma sa akan harkan noma da kasuwanci amma ya nuna ba zai dawo ba domin shi fa zaman America ya fi ma sa akan zaman Nigeria. Wannan ya sa Alhaji Iliyasu ya dena tura mi shi kuɗi tunda ya ƙi bin umurnin sa.
Wasa-wasa sai abubuwa su ka fara ja baya saboda ba kuɗi, gashi Visar sa ta kusa ƙarewa tunda karatu ya zo yi kuma ya ƙare. Sai ya koma kuɗin da zai yi buƙatun da ya saba ma babu. Hakan ya sa ya nemi aiki a wani restaurant a matsayin waiter. Tunani yai akan idan ya auri baturiya su ka haihu zai zama citizen ɗin ƙasar America dan haka sai ya fara neman yarinyar da zai nemi soyayyarta ta yarda ta aureshi.

Lucile-Abigail Haddish 'ya ce ga Thomas Haddish da Veronica Haddish. Iyayenta ita ɗaya su ka haifa a ƙaramin ƙauyen su da ke ƙarƙashin Clark County. Suna da babban gidan gona inda a nan su ke samun duk wani kuɗin shige da fice. Bayan Lucile-Abigail ta gama makaranta ta fara internship na ta wanda ya ke kamar bautar ƙasa kenan a Carson City, Nevada state. 'Yar ƙauye ce da ta yi karatu amma duk da haka ba ta da wayewar 'yan birni. Tanada mentality ɗin za ta samu prince Charming ɗin ta wanda za su yi aure su rayu happily ever after.
Ta haɗu da Muhammad ne a restaurant ɗin da ya ke aiki. Bayan ta gama cin abinci sai ya zo karɓan kuɗi sai ta duba jakarta ashe ta manta ba ta sa purse ɗin ta a ciki ba. Ƙarshen magana dai Muhammad ne ya biya ma ta ya ce ta tafi ba komai. Washegari sai ga ta ta dawo restaurant ɗin ta bashi kuɗin jiya amma ya ƙi karɓa ta yi-ta yi da shi ya ce ya yafe ma ta. Daga nan su ka ƙulla abota wanda ta kai su ga soyayya. Da zuciya ɗaya Lucile ke son Muhammad amma shi da biyu ya ke son ta.
Kafin ta gama internship ɗin ta sai da ta kaishi ƙauyen su su ka gaisa da Iyayen ta, ba su yarda da maganar da ta kawo mu su ba na cewa ta yi saurayi. Saurayi baƙin fata, ɗan Nigeria kuma Musulmi. Bayan ta gama internship ɗin ta ta koma gida inda ta nunawa iyayenta auren Muhammad za ta yi saboda shine Prince charming ɗin ta.
Iyayen ta su ka ƙi sam da maganar wannan ya sa Lucile ta bar gida ta koma wajen Muhammad su ka yi auren kotu.
Rayuwa ta cigaba da tafiya har Shekara É—aya wanda a nan ne Lucile ta samu ciki. Zo ka ga murna gun ma'auratan musamman ma Lucile. Da ciki ya kai wata tara ta haihu inda ta samu É—a namiji. Muhammad ne da kan sa ya sawa yaron suna Muhammad Zuhayr amma Zuhayr su ke kiran sa. Dama sun yi idan mace ne Lucile za ta sa ma ta suna idan kuma namiji ne Muhammad zai sa ma ta.
Chapter 52 · 0% Book details