← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 161

Sashe 8

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya rabu da yaran ne ya shiga wajen mahaifiyar sa Iya ya gaisheta sannan ya wuce ɗakin kakar sa ita ma ya gaisheta kafin ya dawo ɗakin Goggo wacce har lokacin tana lazimi. A gabanta ya duƙa ya gaisheta ta amsa cike da farin ciki. T J ya tambayeta ko Baffa na ɗaki ta ce da alama bai dawo ba tunda ya tafi sallah. Cikin yaren fillanci ya fara ma ta bayani akan Nkiru da kuma dalilin kawota nan. Ya sani ko da sauran 'yan uwan sa ba za su fahimceshi ba to Baffa da Goggo za su fahimce shi.
Bayan ya gama bayani Goggo ta ɗaga ido ta kalli inda Nkiru ke zaune ashe ta yi bacci. Ta kalli T J ta ce "ba ni da matsala da zamanta a nan gidan amma ka san ko za ta zauna sai da yardar Baffan ku sannan za ka sha magana a wajen Iya sai dai ka yi haƙuri"

T J ya ce "na sani kuma zan amince da duk hukuncin da Baffa zai yanke, idan ma bai amince ba zan yiwa abokina Okafor magana ta zauna a gidan su"

Goggo ta ce " Allah ya taimaka, ka duba É—akin na sa ko ya dawo"

T J ya amsa da amin tareda miƙewa tsaye yana stretching hannayensa da su ka yi tsami.

"Zan sa a sa muku ruwan zafi da za ku yi wanka saboda jiki ya warware"

T J ya ma ta godiya sannan ya fita, kai tsaye É—akin Baffan sa ya nufa ya kuwa ci sa'a ya dawo. Ya ma buÉ—e kwanon tuwo kenan zai fara ci T J yai sallama.

Ba ƙaramin farinciki Baffa Habubakar ya ji ba ganin ɗan na sa wanda tun da ya tunkaro gidan yara su ka tareshi a hanya su na gaya ma sa Hamma Tijjani ya dawo. Dan haka da farin ciki ya shiga gidan.

Suna gaisawa ya ce T J ya wanke hannu su ci abinci ba mu su T J ya wanke hannu duk da ba yunwa ya ke ji ba dan ya siya musu Gurasa da nama sun ci a hanya.

Tare su ka cinye abinci sannan aka shiga hira yaushe rabo, daga baya T J ya bayyanawa Baffansa duk abinda ake ciki, ba abinda ya rage ma sa gameda labarin da Nkiru ta gaya ma sa.
Shiru Baffa yai bayan ya gama bayanin yana tunani kusan minti biyar yana nazari kafin yace " Ba zan ce ka kyauta ba ba zan kuma ce ba ka kyauta ba amma abu ɗaya na sani shine duk abinda ka yi ka yi shi ne da kyakykyawar niyya. Kasancewar ta kafira ba zai sa mu ƙyamaceta ba, dan haka za ta zauna har zuwa lokacin da za ka koma ɗin. Allah ya shige mana gaba amma..."

Bayan T J ya baro É—akin Baffa É—akin Goggo ya wuce, Goggo da Asma'u sun rasa yadda za su yiwa Nkiru bayani ta je ta yi wanka sai indiya indiya su ke, ita kuma ta baza ido tana son gane abinda su ke nufi. Da ta ga Asma'u na cuccuÉ—a jiki sai ta gane wanka su ke nufi, ta fara faÉ—a mu su idan ta yi wanka ba ta da wani kayan da za ta sa amma ba su gane ba.
Da T J ya shigo sai ya zauna ya zama interpreter tsakanin su. Bayan ya ji bayanin Nkiru ne ya sanar da Goggo akan zai fita ya siyo ma ta kaya kafin ta yi wankan.

"Haba Shehu, daga zuwa sai fita dan kayan da za ta sa yanzu kam ai akwai shi"

Ta je ta É—auko ma sa riga da zani cikin kayan da ta yi sallar Azumi da shi sau É—aya ta saka ba ta kuma sa shi ba.
T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru ya ma ta bayani ta amsa tareda godiya. Ta bi bayan Asma'u su ka fita.

Wanka ta yi da sabulu zalla ta cuɗa jikinta sosai, ita kan ta ta san ba ƙaramin datti ta yi ba. Ta so wanke gashinta amma tana ganin babu shampoo sannan ruwan ba zai isa ba. Ruwan kuwa da zafi sosai dan haka ta ji daɗin yadda ya ratsa jikinta sosai.

Da ke Goggo ba ta da jiki rigan Goggo da ƙyar ya shigi Nkiru dan ma wai ɗinkin zamanin da ne wanda ake yinsa da ɗan faɗi ba kamar na zamanin yanzu da ake yin fitted ba. Ta ɗaura zani ta fito bayan ta naɗe pyjamas ɗin da ke jikinta da.
Har lokacin T J na É—aki su na hira da Goggo haka ta shigo tana É—ari-É—ari ta so manta É—akin ma albarkacin takalmin T J da ta gani ne ya sa ta gane É—akin.

Sun riga sun yi magana da Baffa akan za ta zauna É—akin Goggo dan nan ne ba za ta samu takura ba. T J yai wa Nkiru bayanin za ta dinga kwana a É—akin Goggo ya kuma jaddada ma ta Goggo ba ta da matsala ba za ta samu damuwa ba, ya kuma nuna ma ta inda Goggo ke sallah ya ce ma ta private space É—in Goggo ne inda ta ke Ibadah dan haka kar ta je ta wajen. Nkiru ta gyaÉ—a ma sa kai.
Sai da zai tafi ya tambayeta ko tana jin yunwa ta ce a'a. Bayan ya tabbatar ba ta da matsala sannan ya fita.

A ƙasa aka ma ta shumfuɗi ta kwanta, a nan Asma'u ke kwana amma Asma'un za ta kwanta a kan gado tareda Goggo. Allah Sarki Nkiru na kwantawa ko minti goma bai kai ba ta fara bacci har da minshari. Da ke ba Goggo ke da girki ba bayan ta gama abubuwanta ta rufe ɗaki ta kwanta kusa da Asma'u da itama tuni ta yi bacci. Addu'an ta Allah ya sa kar zaman Nkiru ya jawo matsala a gidan.

Zuwa washegari duk girman gidan ya É—auka da zancen Hamma Tijjani ya dawo da wata Arniya kuma Inyamura...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*Free page*
*4-i'm not leaving*

Anyi biki lafiya ankai yara É—akunan su. A sashen Baffa Abubakar kam duk yaran sa mata ya aurar. Dama Murjanatu kaÉ—ai ta rage kuma anyi tareda wasu 'yan uwanta biyu, yanzu saura auren Tijjani da Muntari. Har gara Muntari da alamu yana da niyyar yi nan kusa amma T J kam tunda ya fara Jami'a baya so a ma sa maganar aure. Ba wai ya girma sosai ba ne dan shekarun sa ashirin da uku amma kasancewar yawancin samarin familyn na su daga shatakwas, ishirin zuwa ishirin da É—aya za ka ga sun yi aure. Mata kuma a ta girma dayawa agida shine shekara shashida.

Yau ta ke Christmas, duk da mabiya addinin Christianity ba su da yawa a garin hakan bai hana anƙi yin hidima ba. Iyalai da su ke celebrating wannan rana tun da dare ake ta murna ana ta shirye-shirye.
A jiya da daren ne T J ya kawowa Nkiru kyautar ta ya ce ka da ta buɗe sai safiyar christmas. With full excitement ta kwana tana tararradin mi T J ya siya ma ta. Da safe kuwa tana tashi gift ɗin ta buɗe da mamakin ta sai ga Bibble sai kuma ɗan ƙaramin box wanda ke ɗauke da ɗan kunne da sarƙa. Ta fara shafa sarƙan tana murmushi lokaci guda kuma ta tuna da iyayenta. Ta tuna yadda su ka celebrating christmas ɗin su last year, ta tuna yadda su ka decorating christmas tree ɗin su. Ta goge hawaye tana fata Daddy and Mommy su na heaven su na kula da ita shiyasa su ka turo ma ta mutumin kirki ya taimaka ma ta.

Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfar da T J ya siya ma ta wanda jiya aka karɓo ma ta ɗinkin. Ta sa kayan riga da skirt amma ta ka sa ɗaura ɗankwalin duk yadda ta ɗaura sai ta ga bai ma ta ba. Tana ganin Pendo na ɗaurawa amma ba ta ɗauka da wuya haka na. Ta san balbalin su Pendo amma ba ta son zuwa saboda Innar Pendo ba ta son ganinta, da sun zo da Pendo za ta fara yare tana tofe tofen yawu kamar ƙyamar Nkirun ta ke.

Tana haka sai ga T J ya shigo É—akin da sallama. Goggo ba ta É—akin Asma'u kuma ta je wanka. Tsayawa yai yana kallonta yadda ta yi kyau cikin kayan Hausawa.
"Thank you Teejay, i like the gift"
Ta faÉ—a bayan sun gaisa.
Tambayarta yai ko ta shirya ta ce ta shirya amma ta kasa É—aura É—ankwali ko ta barshi a gida ne. Ya ce a'a bari ya kira ma ta Pendo. Ya fita da sauri.
Shi da Pendo su ka dawo yana tsaye har Pendo ta É—aura ma ta É—ankwali sai gashi ta dawo Bahaushiya sak, kayan sun sake fidda kyan ta.

Ta É—au Bibble É—in da ya ba ta su ka fita. Wannan ne karonta na farko da ta fita daga gidan har anguwar ma, suna tafiya T J na ma ta bayanin yanayin zamantakewar 'yan garin.

Gidan su abokin sa Okafor su ka je, sun ma shirya dama shi su ke jira. Bayan ya gaisa da Papa da Mama Okafor sannan ya damƙawa Okafor amanar Nkiru yana jan kunnen sa akan ka da ya bari wani abu ya sameta. Okafor yai dariya ya ce ai Nkiru ƙanwar sa ce ba zai bari wani abu ya sameta ba. Yana tsaye su ka wuce church dan gudanar da bauta a safiyar ranar christmas. Sai da ya ga sun ƙule ma sa kafin ya bar wajen yana jin kamar ya bi su church ɗin.
Chapter 8 · 0% Book details