Sashe 124
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ita kaÉ—ai ya zo saboda Ghazala ta je Lagos clearing wa su kayanta da su ka iso.
Ita ne ƙarshen zuwa ɗakin, ganin an cika a ɗakin ya sa zuciyarta ya karaya. Mi ya ke faruwa kamar Uncle Muntari zai yi ban kwana da duniya.
Mommy, Iya, Salman, Auwal, Humairah duk suna zaune jugum kamar wanda aka yi mutuwa.
Ko ma mi za a faɗa Junior yayi ƙaranci ya zauna a cikin taron nan.
Gefen Mommy Zaytoonah ta zauna tana faÉ—in "Mommy lafiya?"
"Baban ku ke son ganin ku"
Sai da aka shafe kusan minti bakwai bayan shigowar Zaytoonah kafin Muntari ya nisa ya ce " dukkan kunnan ni mai laifi ne a gareku. A lokacin ƙuruciya, a lokacin jahilci da son zuciya na aikata laifin da har abada ba zan taɓa yafewa kaina ba. Ina roƙon ku Dan Allah ko ba yanzu ba ku samu ku yafemin ko Allah zai yafe min."
Ya kalli Iya ya ce "kusan kaso hamsin cikin abinda ya faru yanada nasaba da ke Iya. A lokacin da ya kamata ki kwaɓe ni ba ki yi ba, a lokacin da Baffah, Gwaggo da ma Hamma Tijjani su ke ƙoƙarin nutsar da ni zuwa hanyar dai-dai ba ki ba su goyon baya ba. Iya ke ki ka hura wutar ƙiyayyar da na ke yiwa Hamma Tijjani. Ke ki ka jagoranci rashin jituwa da ke tsakanina da Hamma Tijjani"
Zuwa lokacin fiskar Iya ya jiƙe da hawaye, ta sa bakin gyalenta ta toshe bakinta saboda kar kukan da ta ke riƙewa ya fito.
"Maryam ni ne silar rabaki da mijin ki, Zaytoonah ni ne silar rabuwa da kukayi da Mahaifin ku a lokacin da ku ka fi buƙatar shi"
Yanzu kam kowa ido ya zubawa Muntari cike da tambayoyi.
"Ku yafe min dan Allah. Hamma Tijjani..." ya fashe da kuka.
Ba wanda ya ma sa magana dan kowa a ruÉ—e ya ke.
Mommy abinda ke yawo a ranta kawai Muntari kashe ma ta Barkindon ta yai.
"Ni na sa aka ma sa kurciya, ba zai taɓa waiwayowa inda Ahalinsa su ke ba, ba re taɓa zuwa inda Ahalinsa su ke ba. Tafiya zai yi ta yi har sai idan kurciyan da ke rinjayan sa ta mutu. Ban san ko yana raye ba ban kuma san yadda za ayi a karya asirin ba. Ku yafe ni"
"Muntari Muntari" Iya ta faÉ—a tana fashewa da kuka.
"Allah ya isa Uncle" Salman ya faɗa yana jin tsanar Muntari har da jin haushin kan sa na ƙoƙarin taimaka ma sa da yai.
Zaytoonah da Humairah kuka su ke yi wiwi kowa na tuno ƙuruciyar sa da Daddyn na su.
Mommy dai zare jiki ta yi za ta fice ba ta ce komai ba ko kukan ma ba ta yi ba. Zaytoonah ta kirata "Mommy"
Ba ta ce komai ba ta juya ta fice daga É—akin.
Kai tsaye Motar ta ta nufa, tana shiga ta sa ma ta wuta, da wani mahaukacin gudu ta bar farfajiyan Asibitin.
Ba kowa a gidan na su dan Junior ya tafi Islamiyya. Ɗakin ta ta shiga ta duba ƙarƙashin gado ta jawo wani akwati. Hannunta har rawa ya ke lokacin da ta buɗe shi. Hoton TJ ta ciro ta saka a ƙirji sai kawai ta fashe da kuka, kukan da rabon da ta yi irin sa tun ranan da TJ ya ɓata...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 61
Bismillahir Rahmanir Rahim
*The birthday party*
"Hajiya lafiya kuwa?"
Ta yi firgigit daga nisan tunani da ta yi. Ta É—ago ido ta kalli Maman Tope da ta zuba ma ta ido da alaman damuwa.
"Hajiya tun É—azu na ke tsaye a nan har na kashe gas ba ki ji ba. Hope all is well Ma?"
Sai a lokacin ta maida hankalinta ga kan tukunyar da ke gaban ta. Girki fa ta ke yi amma ta manta da shi ta buge da tunani. Tunda ta baro Zaria ta rasa nitsuwarta, kewar Mahaifinta ne ya dawo ma ta sabo. Ko ina ya ke?, mi ya ke ci?, a ina ya ke rayuwa?, shin ma yana raye? KaÉ—an daga tambayoyin da su ke damunta kenan tunda Uncle Muntari ya gaya mu su abinda yai wa Mahaifin su.
"Ba komai, kawai na shafa'a ne"
Maman Tope da kallo kawai dan ba ta yarda da abinda ta faÉ—a ba.
Kwashe abincin kawai Zaytoonah ta yi ta bar wa Maman Tope ta kai dinning.
Ɗakin 'yan biyu ta wuce dan ta gyara mu su dan Bahijje ta tafi ƙauye.
Da ta gama ta shiga É—akin su Raziya suma ta gyara mu su sannan ta wuce na ta É—akin...
Ƙyalƙyalewa ta yi da wani Mahaukacin dariya lokacin da baturen da ta kira ya gaya ma ta ya gama aikin da ta sa shi har ma ya tura ma ta hoton aikin ya ce ta duba email ɗinta za ta gani.
"Sak" ta furta lokacin da ta ga hoton
"Shege Bature, wato shi dai bature Tantiri ne, indai ya ga kuÉ—i ba abinda ba zai iya yi ba"
Aiki ya kammala dan haka za ta tura ma sa balance ɗin sa ta jira ya shipping ɗin kayan zuwa Nigeria. Tana sa ran zuwa sati biyu ma su zuwa saƙonta zai iso hannun ta.
***
"Wannan kukan na minene?"
Ta yi saurin saka hannu ta fara goge hawayen da ya riga ya ɓata ma ta fiska.
"Zaytoon we've talked about this, miyasa ba kya jin magana ne wai. Kuka zai dawo miki da mahaifin ki ne? Ko kuma zai maida hannun agogo baya?"
"Ka yi haƙuri Dan Allah"
"Seriously za mu yi faɗa idan na sake kamaki kina kuka. Addu'a za ki ma sa, addu'a Zaytoon. Ba abinda ya fi ƙarfin Allah. Shi za ki kaiwa kukan ki bawai ki tsaya kuka na ɗaga hankali ba"
"I'm sorry"
Kama hannunta É—aya yai ya jawota jikin sa ya ce " jiba yadda kika koma Dan Allah. Ni kaina kin hanani sukuni balle ke kan ki. Yanzu yaushe rabon da ki tanade ni?"
Murmushi ne ya suɓuce ma ta ta ce " wannan Tsoho akwai jaraba" ta ɗan ja kumatun sa
"Indai jarabar ta ki ce na yarda, kin san ke ta daban ce" ya faÉ—a yana kissing wuyan ta.
"Ranka shi daÉ—e"....
Washegari tana yiwa 'yan biyu shirin makaranta su ka fara yi ma ta gulma. Hashir ne ya fara faÉ—in
"Mom wai muma ba za mu yiwa Daddy wani abu ba ne kamar na su Suhailah?"
"Wani abu kenan?"
"Wai gobe ne birthday É—in Daddy"
"Ba gobe ba ne jibi ne Da Allah" Hadid ya gyara ma sa.
"Daddyn ne ya gaya mu ku zai yi birthday"
"A'a, Suhailah ce kuma Hajiya ma ta ce mu su kar su faÉ—a mana, wai su kaÉ—ai za su fita ranan"
Abin ma dariya ya ba wa Zaytoonah. Wato dan ranan zai kama ranan kwananta shine har da cewa su kaɗai za su fita. Daɗin abin ma ba ta da lokacin ɓata rai akan wannan, idan ranan ta ne su yi duk abinda su ka ga dama ta riga ta san yadda Ranka shi daɗe ke komawa idan yana Fadar ta.
"Mommy miyasa muma ba za mu yi celebrating birthday É—in ba. He's our Daddy right?"
ÆŠaga hannun sa ta yi sama ta fesa ma sa turare ta kuma É—aga É—ayan ma ta fesa sannan ta ce "Of course he's your Daddy Muhammad. Amma Daddy baya celebrating birthday É—in sa so ba abinda za mu yi"
"Noooo" Hadid ya faɗa da ƙarfi
"To ai su Hajia da su Suhailah sun ce za su je yawo a ranan mu miyasa ba za mu je ba"
"O'o ni Zaytoonah. Yaran nan yaushe kuka fara sa'ido haka"
"Mooom" su ka faɗa suna ƙanƙance ido kamar yadda su ke yi idan suna so ta mu su wani abu.
"Ok ok, zan duba abinda za mu iya yi ma sa, but its a secret. Kar na kuskura na ji shi a kunnen wani kun ji"
"Yes Mom" su ka faÉ—a a tare suna dariya...
Da dare da ya dawo suna cin abinci suna hira ta sako zancen birthday.
"Alamu sun nuna jibi muna da grand party a gidan nan, tunda ba a sa damu a ciki ba za mu zuba ido kawai"
ÆŠago ido yai yana kallon ta. Ta san ba zai yi magana ba shiyasa ta cigaba. "Ina nufin birthday party É—in ka jibi"
"Birthday party kuma?"
"Oh ba ka sani ba"
"Birthday party sai ka ce Yaro"
ÆŠan jan gemunsa ta yi kaÉ—an ta ce "My Baby, ni a wajena kai yaro ne ai"
"Ni kinga na ma manta jibi ne. I dont celebrate birthday ai. Amma ba zan ƙi special party a ɗaki na ba, iya mu biyu"
"Not so fast É—an saurayi, jibi fa kai da Amarya ne, babu ruwana a ciki" ta faÉ—a tana dariya
Irin kallon da ya watsa ma ta ne ya sa ta yi saurin gimtse dariyar tata.
"Idan ma wayo za ki yi yau dai sai an min special party É—in nan. We'll do Pre-Birthday and Post- Birthday duka a yau"
"Dole na Sayyidi" ta faÉ—a tana kai ma sa sokali dai-dai bakin sa...
***
Tanadi na musamman Ghazala ke yi na birthday ɗin Maigidan na su. Allah ya taimaka ma ranan zai faɗa Saturday ne dan haka plans ɗinta duka zai tafi dai-dai. Da safe za su fita da yara su je wajen shaƙatawa zuwa da rana sai su dawo. Da dare kuma ta riga ta booking mu su hotel wanda honeymoon suit ne na gani na faɗa wanda karɓan irin sa ma sai da connection, a nan ta ke so su kashe dare suna raya sunna. Sati guda ta yi tana zuwa ana ma ta gyara dan kulawa na musamman ta ke son ba wa Yallaɓai a daren.
Yau da Ghazala ta karɓi girki ta ke sanar wa Justice kan cewa gobe za su fita da yaran dan an kwana biyu ba a fita ba. "Za ku iya tafiya ba matsala"
"Dear, na ce dukkan mu ai za mu fita tunda mun kwana biyu bamu yi irin fita haka ba"
"Inada É—aurin aure da zan je gobe sannan zan yi ziyara"