← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 161

Sashe 71

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ciki?" Ta furta tana kallon sa.

"Yes Zaytoon kinada ciki"

Lokaci É—aya sai jikinta ya hau rawa. "Ciki?" Ta sake faÉ—i a ruÉ—e.

Ya gano abinda ta ke tunani dan haka yai saurin jawota jikin sa yana faÉ—in "forgive me Zaytoon, I actually, I..."
Wayar sa ta shiga ƙara dan haka ya sa hannu ya ɗauka. Zaytoon's Mom ya gani a screen ɗin.
Allah Sarki ba su ma kiraba amma ita ta kira.

"Mommy ce" ya faÉ—a yana nuna ma ta screen É—in. Har ta gama ringing É—in bai É—auka ba.

"Ina tunanin kar mu gaya ma ta abinda ya faru saboda kar hankalinta ya tashi"

Ta gyaÉ—a ma sa kai. Lokacin da ya kirata ringing É—aya ta yi aka É—auka.
Bayan sun gaisa ta ke tambayar ina Zaytoonah dan tun jiya tana neman numbarta ba ya shiga. Ba ta san tun jiyan wayar na hannun 'yan sanda ba.

"Wayar ce ta samu matsala" Zuhayr ya faɗa a taƙaice sannan ya sawa Zaytoonah wayar a kunne.

"Adaeze kina lafiya dai ko?"

"Mommy" sai kuma kuka ya kuɓce ma ta.

"Adaeze miya faru? Ba ki da lafiya ne? Zuhayr ya miki wani abu ne"

"Mommy pray for me" ta faÉ—a cikin kuka.

Hankalin Mommy ya tashi ta ce " ba wa Zuhayr na ma sa magana"

Zuhayr ya maida wayar kunnen sa.

"Mi ya samu 'ya ta? Mi ka ma ta?"

Ya sani a yadda ta rikice ɗin nan indai ta ji abinda ke faruwa da 'yarta ƙila heart attack zai kamata dan haka yai gyaran murya ya ce "she's pregnant, tana kuka ne saboda ba ta da ƙwarin jiki ba ta iya karatu kuma sun kusa fara exams"

Mommy tunda ta ji kalmar Pregnant sai ta ɗan ji sanyi a ranta. Bayan ya ma ta bayani sai ta nemi magana da Zaytoonah inda ta yi ta ma ta nasiha tareda ba ta tips na yadda za ta kula da kan ta, da yadda za ta dinga duba karatu. Zaytoonah ta daure ta ma ta godiya sannan ta ƙara jaddada ma ta akan ta ma ta addu'a. Mommy ta ce kullum ma tana yi ma ta.

Bayan Mommy ta ajiye wayar sai ta riƙe baki, yadda su ke waya da Zaytoonah da kuma video call sai ta ke gani kamar ba abinda ke shiga tsakanin ta da Zuhayr har ta ke gani ko Zuhayr ne ya ɗaga ma ta ƙafa zuwa ta ƙara girma kaɗan ashe-ashe, dama tsakanin miji da mata sai Allah.
Bayan ta gama jimamin zancen cikin Zaytoonah sai kuma T J ya faÉ—o ma ta.
Ta goge hawayen da ya fara zubo ma ta tana faÉ—in "duk inda ka ke na san Allah na tare da kai, ina ji a raina ba ka mutu ba kuma za ka dawo garemu. Za ka zo ka tarar da É—an ka Abubakar da É—an ko 'yar Zaytoonah"
Daren farkon su ne ya faÉ—o ma ta, yadda ta samu soyayya daga wajen T J, ta kuma ji jiki a wajen ÆŠan Fulanin ta.

Ta buɗe drawer da ke gefen gado ta ciro hoton sa. Hoto ne lokacin yana bautar ƙasar sa, a duk lokacin da ta ga hoton nan tunowa ta ke yi da mafarin komai, mafarin haɗuwar su wanda ya kawo su har ga aure da samun zuri'a.
Ta sa hannu tana shafa fiskar T J da ke É—auke da dariya...

Abincin da Zuhayr ya kawo ma ta kaɗan ta iya ci saboda ko kaɗan ba ta jin taste ɗin komai a bakin ta. Kamar yadda Mommy ta koya ma ta lokacin ɓatar Daddyn su shi ta tuna takeyi. Da ta tuna ana tuhumar ta da laifin kisa sai ta fara furta Hasbunallahu wa ni'imal wakil nan da nan sai ta ji ranta yayi sanyi.
Cikin da ke jikinta kuwa zuciyar ta kokonton abin ya ke. Wai 'yar ita É—in nan ne ta ke da ciki, wai lokacin da su ka je Finland Zuhayr ya ma ta irin abinda ake yi idan anyi aure, sai kuma ta ji kunyar Zuhayr ya kamata.

Motsi kaÉ—an Zuhayr zai fara tambayar ta ko lafiya. Bayan ta yi sallah ta kwanta daga baya da Zuhayr ya je yai wanka shima ya zo ya kwanta kusa da ita ya jawota jikinsa ya rungume.

Ko jimawa da bacci ba ta yi ba ta fara mafarkin abinda ya faru gawar Linda da ta gani, yadda police su ka sa ma ta ankwa su ka tafi da ita, tambayoyin da aka fara ma ta bayan sun isa station har ya sa ta suma a wajen saboda gigicewa.

"I didnt kill her, i didnt kill her" ta farka a zabure tana faɗa da ƙarfi jikinta na ɓari.

"Hey Zaytoon relax, relax, i'm here" ya fara faÉ—a a kunnenta bayan ya rungumeta jikinsa sosai.

Kafin bacci ya kuma É—aukan ta sai kusan bayan awa biyu.

Bayan ya tabbatar baccinta yayi nisa ne ya miƙe ya shige banɗaki ya ɗauro alwala.
Alinah ta faɗa ma sa duk lokacin da ya ke cikin damuwa ya tashi da dare yai nafila raka'a biyu ya gaya wa Allah damuwar sa Insha Allah zai samu sauƙi. Rabon da ya tashi sallah da dare tun kafin Alinah ta rasu. Bayan rasuwanta kusan ya koma gidan jiya ne dan duk wani abubuwa na ibada da ta ɗaurashi a kai watsar da su yai.

Ya jima yana yiwa Zaytoonah addu'a bayan yayi sallar kafin ya dawo ya kwanta kusa da ita.

Washegari za su je station ƙarfe goma dan haka tun ƙarfe tara su ka shirya. Wa su 'yan jarida sun zo gidan sa tun da sassafe amma ya sa securities ɗin sa sun kore su.

Lokacin da su ka fito daga mota yana riƙe da ita yayinda Zaytoonah ta rufe fiskarta da gyalenta.

"Mr Zuhayr dama kana da aure ne? Ance matar ka minor ce ba ta cika shekara shatakwas ba gaskiya ne?"

"Mr Ilyas wasu mutane na faÉ—in mutuwar Linda Cannel yana da nasaba da mutuwar tsohuwar budurwar ka Alinah Jones mi za ka ce gameda haka?"

"Mrs Ilyas miye haÉ—in ki da wacce kika kashe Miss Linda Cannel?"

Kaɗan daga tambayoyin da 'yan Jarida ke musu kenan kafin su shiga station ɗin amma babu wanda yai magana cikin su, Zaytoonah kam ko fiskarta ba a gani balle ma tayi magana, shi kuma gogan baƙin glass ya saka ya murtuke fiskarsa.

Ta samu words of encouragement daga wajen Zuhayr kafin zuwan su dan haka ta É—an nitsu lokacin da ake ma ta tambayoyin.

Bayan an gama da ta fito Zuhayr ya riƙeta su ka fita a wajen. A wajen tambayar ta yi hawaye kam amma ba ta yi kuka wiwi ba kamar ranan farko.

Daga station su ka wuce gida inda private investigator da Zuhayr ya É—auka ke jiran su da information É—in da ya samu.
Ba a kawo report na Autopsy da aka yi ba tukunna amma cross examination da aka yi a wajen crime scene ɗin an samu shaidar ƙafar takalmin namiji a wajen, sannan duk da an ga finger print na Zaytoonah a jikin wuƙar babu a wani wajen banda jikin rigan Linda, wanda taɓata da Zaytoonah ta yi ne ma ya sa aka samu. Wanda kuwa da ace kokawa su ka yi kafin ta daɓa ma ta wuƙa da za a finger print na ta a wasu sassan jikin ta.
Zuhayr ya ji daÉ—in feedback É—in da ya samu dan dama ko kaÉ—an bai ji a ransa cewa Zaytoonah ce ta kashe Linda ba, a wani dalilin za ta kashe ta?.

Ben kam yana chan yana ƙoƙarin bibiyar investigation ɗin ko za a iya samun abinda zai sa a gano shi, da zai je gidan Linda ba ta ƙofar gaban gidan ya zo ba sannan yayi disguising kan sa kafin ya shiga gidan. Ya yi amfani da extra precaution ta yadda ba za a ga finger print ɗin hannun sa ba ko ma wani abu da zai tona asirin sa.

Da yamma yana bawa Zaytoonah abinci a baki a ka kirashi ake sanar ma sa wai Farha Jubril ƙawar Zaytoonah na son ganin sa.
Ba ya son hayaniya dan haka ya ce ace ma ta ba shi da lokaci. Sake kira aka yi wai ta ce tanada abu mai mahimmanci da za ta bashi ne.
Ya taɓa ganin yarinyar a Asibiti lokacin da aka kwantar da Zaytoonah amma yanayin yarinyar kamar bai yarda da ita ba sai dai a halin yanzu yana buƙatar duk wani taimako da zai sa a warware case ɗin nan a clearing sunan Zaytoonah.

Sai da ya gama ba wa Zaytoonah abinci kafin ya sauko ƙasa.
Bayan Farha ta gaishe shi ne ta miƙa ma sa wani hard drive ta ce " Akwai wasu evidence da na haɗa a nan wanda zai iya taimakawa Zaytoonah. Incase ma an jirkita wasu evidence ɗin wannan ma zai iya taimakawa"

"Calls da aka yi tsakanin Zaytoonah da Linda ne tun lokacin da su ka exchanging contacts ɗin su sannan akwai footage na lokacin da Zaytoonah ta shiga library da lokacin da ta fita. Akwai kuma na lokacin da taxi ya sauketa a ƙofar gidan Linda, idan an fitar da result na autopsy za a duba time ɗin mutuwar Linda da kuma time ɗin shigar Zaytoonah gidan"

"Thank you Farha" ya faÉ—a yana saka hard drive É—in a aljihun sa.

"How's she?"

"She's fine"

Ta miƙe tsaye ta ce ma sa za ta tafi. Ya ƙara yi ma ta godiya kafin ya wuce sama dan ko kaɗan baya son barin kusa da Zaytoonah.

Farha na fitowa ta yi kiciɓis da Ben zai shigo gidan. Tsorata ta yi da yadda ya ke kallonta amma ta dake ta wuce shi ba tareda ta ma sa magana ba...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 31

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Ustadzh Ben-Zubair*

A rana ta huÉ—u da abin nan ya faru Uncle Aliyu ya zo gidan su. Shi bai san abinda ya ke faruwa ba sai da ya gani a jarida. To daya kira Zuhayr shine ya confirming cewa gaskiya ne abinda aka rubuta amma kuma Zaytoonah ba ta yi kisan ba. Ya ma sa faÉ—a kam na yadda bai kirashi ya faÉ—a ma sa babbar matsala kaman wannan ba.
Chapter 71 · 0% Book details