← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 161

Sashe 14

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Iya ya fara rawa, yadda Baffah ke magana da ƙarfi ya sa ta kuma tsorata.

Ya kalli T J ya ce " kalleni Shehu"

T J ya É—ago rinannun idanun sa ya kalleshi.

"Wallahil Azim duk ranan da ka saki Maryam to a bakin auren mahaifiyar ka"

T J ya rikice da jin wannan magana. Itama Iya ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba da jin abinda Baffah ya ce.

"Kinga Aishatu duk ranan da ki ka sa Shehu Tijjani ya saki matar sa kaman na sake ki ne, kuma Allah ko bayan rai na kika sa shi rabuwa da ita ba zan taɓa yafe miki ba. Haba, haba Aishatu. Ke kina ƙara girma kina ƙara rashin hankali ne, yaron nan kullum hantarar sa ki ke yi ba dama ya so abu sai ki dinga kushewa. Wai shin ma kyautar da Allah ya mi shi ki ke so ya yar? Wani jahilci ke damunki da za ki dinga irin wannan furucin"

Ya kalli T J ya ce "tashi ka tafi wajen matarka"

"Baffah ka yi haƙuri" ya faɗa murya a raunane

"Tashi ka tafi"
Haka ya tashi simi-simi ya bar ɗakin. Baffah ya cigaba da yiwa Iya masifa duk wani abu da ya ke shanyewa tun da sai da ya amayar ma ta da shi. Ta fara kuka wiwi har da majina. Rabon da Baffah ya ma ta irin faɗa haka tun tana Amarya, watarana da ta je ɗakin Maryama ta kwarara ma ta ruwa bokiti biyu a cikin ɗakinta. Ranan sai da Modibbo ya shiga tsakani dan duk yadda ya ke da haƙuri sai da ya mareta a ranan.

Yana shigowa ɗaki kai tsaye gado ya hau ya jawo Maryam jikinsa ƙyam yana sauke ajiyar zuciya. Tana bacci ta ji an rungumeta hakan ya sa ta buɗe ido, jin yadda jikinsa ke ɓari ya sa ta yi saurin juyowa ta kalleshi.

"Miya faru?" Ya girgiza ma ta kai ya kuma jawota jikinsa yana faÉ—in "I love you Maryam, ba zan iya rabuwa da ke ba, I love you. Idan aka rabani da ke zan shiga tashin hankali, without you I cant have a happy life"

"I love you too" ta faÉ—a tana shafa gashinsa tana hura ma sa iska a kunne...

Washegari Baffah ya kirashi ya kuma jaddada masa maganar sa ta jiya tareda cewa ya shirya ya tafi da Maryam Zaria. Idan ba shi da wajen da zai ajiye ta ne to zai bashi kuÉ—i ya kama mu su haya a chan. Ya haÉ—a da cewa Maryam amana ce a gareshi dan haka kada ya ci amanar ta Allah zai kama shi.

Ba su tafi tare ba amma bayan kwana huÉ—u da tafiyar sa ya dawo ya É—au Maryam su ka koma garin Zaria. Hayar É—aki É—aya ya kama mu su suke zaune hankali kwance suna shan soyayyar su ba mai takura mu su balle a sa mu su ido.

Lokacin da T J ya ƙare Masters na shi ba ƙaramin karramawa ya sha ba saboda kasancewar sa haziƙin ɗalibi, gashi thesis ɗin da yai ya kawo cigaba a Faculty na su dama makarantar gaba ɗaya. Aikin lecturing aka bashi saboda makaranta na buƙatar haziƙin mutum kamar sa.
Bayan sun samu gida a quaters na school T J da Maryam su ka je Ringim inda su ka tattaro duk kayan ɗakin Maryam ɗin su ka kawo sabon gida tunda wannan a wadace ya ke ba kaman ɗaki ɗaya da su ka fara zama ba, aka ƙara da wasu siyayyan

Abu na gaba da ya fara yi shine ya fara bincika wa Maryam yadda za ayi ta samu takardun makarantar ta. Aka rubuta letter aka aika chan makarantar su. Kafin a dawo da reply sai da ya ɗau kusan sati bakwai, a saƙo na gaba da suka turo ne aka haɗo da sabbin copies na results ɗin ta. Nan da nan T J ya shiga nema ma ta gurbin karatu a nan ABU Zaria cikin ikon Allah kuwa ta samu. Law ta cika saboda tunda ta auri T J ta gaya mi shi ra'ayinta na son ɗaukan fansa kan abinda Uncle Udodiri yai wa iyayenta kuma T J ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.

Zaman lafiya su ke ba wani tashin hankali, zai fita koyarwa ta fita ɗaukan karatu idan an dawo da yamma ya koya mata ƙur'ani da kuma iya litattafan addini. Duk ilimin da ya samu na addini to a wajen Kakan sa Modibbo ya samu kuma yana ƙara godiya daya sa alokacin ya maida hankali kan karatun gashi yau ta ma sa rana.
Duk ƙarshen wata T J ke zuwa ganin iyayen sa ita kuma Maryam Nkiru sai bayan wata uku ta ke zuwa duba su. Har lokacin babu wani chanji a tattare da Iya dan tunda Baffah ya ma ta faɗan nan ta sake watsar da kashin T J da Maryam ko kallon kirki ba su isheta ba, abun na bala'in damun T J musamman yanzu dayake ganin a hankali za su zo su fara tara iyali da shi da Maryam. Goggo na yawan kwantar ma sa da hankali akan ya cigaba da yiwa Iya addu'a watarana komai zai dawo dai-dai.

Muntari sai da yayi shekara ɗaya da wata biyar kafin ya zo gida nan ma zuwa yai ya leƙa Iya dan ya san ita kaɗai ne hankalinta zai tashi da rashin sa. Duk yadda ta ma sa faɗa akan ya dawo gida ya ƙi, cewa yai saboda Hamma Tijjani yayi boko shiyasa aka walaƙantashi aka aurawa T J Maryam bayan kuwa an sani shi ke sonta. Iya ta tsorata da lamarinsa saboda ta ɗauka iya lokacin nan ya manta da batun Maryam. Tsanar Maryam ya kuma dira ma ta a zuciya ta sawa ranta Maryam Mayya ce shiyasa ta kama ma ta 'ya'ya har biyu. Ga Tijjani ya zama tamkar wawa a kan Maryam shi kuma Muntari ma tana tunanin hauka yayi.

"Sai na yi kuɗi, Aradun Allah sai na yi mahaukacin kuɗi ta yadda ko ta Maryam sai ta yi nadamar auren Hamma Tijjani da ta yi. Sai na nunawa dukkan wanda su ka zalinceni cewa Boko ba komai ba ne, Arziƙi shine mutum"

Kamar Iya za ta yi kuka haka ta dinga roƙonsa akan ya haƙura da Maryam ya nemi wata a ma sa aure amma ya ƙi.

"Ni kam na shiga uku ni Aishatu, Yasin wannan Inyamuran ta gama da ni. Muntari ka dubi Allah ka dubi Annabi ka haƙura da ita, ga kyawawan 'yan mata nan ka nema ka aura. Ba wacce za ka nema da za ta ƙi ka"

"Iya ki bar zancen nan ko zan yi aure ba yanzu ba. Idan ban cimma burina ba bazan taɓa samun sauƙi ba"
Ya buga ƙirjinsa ya ce " ki yi haƙuri amma son Maryam yanzu na fara shi"

Kwana biyu yai a gidan ya bar garin wannan karan ba Kano ya tsaya ba Lagos ya wuce neman kuÉ—i...

***

Shekaru biyu kenan cur da auren Maryam da Tijjani kuma har lokacin ba ta samu ciki ba. Ita ne ma ta fara damuwa amma shi kam ba ruwan sa kullum ce ma ta ya ke lokaci ne bai yi kuma ai ba su jima da aure ba ma. Itama ta fara damuwa ne tun lokacin da su ka kai ziyara gida matan gidan ke ce mata sun ji shiru har yanzu. Yanzu kam ta iya Hausa kuma Fulatancin ma ba laifi ta kan ji kuma tana amsawa daidai gwargwado.

Zuwan su na ƙarshe gida bikin Pendo ne. Zainaba wacce ake cewa Pendo ta samu gudummawa sosai a wajen Maryam. Allah ya haɗa jininsu tun ranan da su ka fara haɗuwa kuma duk yadda aka ƙyamaceta a gidan kafin ta musulunta Pendo ba ta taɓa ƙyamar ta ba. Mijin Pendo ma dai duk ɗan cikin gida ne amma a Dutse ya ke aiki a wani ma'aikata, da Sakandare ya fara aikin amma yanzu ya fara karatu a Jami'ar BUK saboda mahimmancin Ilimi daya gani.
Ta so ta bi 'yan kai Amarya amma T J ya hana ya ce ta bari idan an kwana biyu za su kai ma ta ziyara har Dutsen.

Bayan bikin Pendo Baffah ya fara jinya wanda bai cika wata uku ba ya rasu mutuwar da ta girgiza iyalen gidan gaba É—aya musamman ma T J da Maryam. A wajen rabon gado ne T J ya tambayi yayansa Usman Manga ko ya san inda Muntari ya shiga, ace Baffah yayi jinya har ya rasu amma Muntari bai zo ba.
Usman ya ce ai ya rabu da shirmen Muntari wai Lagos ya tafi neman kuɗi. T J ya taɓe baki yana mamakin halin ƙanin na sa. Sam tun tasowar yaron baya ji kuma daɗin daɗawa Iya da ta dinga ɗaure ma sa gindi ya sa ya sake botsarewa. Ko lokacin da ya gudu daga makaranta ma ya ce ba zai yi karatu ba Iya ce ta fara supporting ɗin sa, har ta kai dole Baffah ya haƙura ya barshi ya tafi Kano wai neman kuɗi.

T J ya ce Allah ya shirya shi.

Gadon Muntari aka damƙawa Iya ta ajiye mi shi zuwa lokacin da zai dawo...

Bayan rasuwan Baffah da wata shida watarana yayar Iya wacce su ke cewa Inna Saratu ta kawo ma ta ziyara da 'yar ta Hajara da su ke cewa Hajjo a wannan zuwan su ne kuma su T J da Maryam su ka zo gida. Yadikko ce ba lafiya, ita tun rasuwan Abubakar ma bata jin daɗi dan mutuwar ya girgiza ta, ɗan ta ƙwalli ɗaya a duniya ya tafi ya barta.
Hajjo ta ƙyalla ido ta ga T J nan ta sanar da Inna Saratu cewa ta samu mijin aure. Dama wani tsoho ta ke so saboda kuɗin sa a chan ƙauyen su amma yanzu da ta ga T J ɗan boko wayayye kyakyawan saurayi sai ta ji ba abinda za ta yi da Alhaji Rabe.

"Amma Hajjo kin san fa watan nan za a sa mi ki rana kike maganan kinga mijin aure a nan. Dan uban ki Alhaji Raben ba mijin aure ba ne?"

Hajjo ta yi dariya ta ce "Inna wallahi ina faÉ—a miki sunan sa za ki rikice, aiko an É—aura auren za ki sa a warware"
Chapter 14 · 0% Book details