← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 161

Sashe 35

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya tashi ya zauna yana jingine bayan sa da pillow.
Maryam ta miƙa ma sa tea ɗin tana tambayar ko yayi brush ya gyaɗa ma ta kai.
Yana karɓan tea ɗin ya haɗa da hannunta ya jawota ta faɗa jikin sa wanda hakan ya sa tea ɗin ya zube. Duk da tea ɗin ya ɗan ƙona shi bai wani nuna damuwa ba.

"Muntari what are you doing" ta faɗa tana ƙoƙarin tashi.

Flipping É—inta yai lokaci guda ya zama ya ma ta rumfa da jikinsa.

"Muntari kana hauka ne, what are you trying to do. Ni matar yayanka ne"

"Na fi kowa sanin haka Maryam. Ke budurwata ce da Yayana ya min ƙwace. Ina son ki Maryam har yanzu zan..."

Ta fara ƙoƙarin tureshi amma ya riƙe hannayen ta biyu.

"Ki saurareni Dan Allah. Ba zan miki komai ba amma"

"Muntari ka rabu da ni dan Allah" tana faɗa da ƙarfi

"Ina so ki sani duk iya tsawon shekarun nan ke kaɗai na ke so ban taɓa son wata ba. Kuma na dawo ne dan na same ki, kin ga wannan gidan da ma duk abinda na mallaka naki ne, da sunan ki na sameshi"

Ganin maganganun sa ba su da kan gado ya sa ta fashe da kuka tana ƙoƙarin ƙwace kan ta daga gareshi amma ta kasa.

" ki yi haƙuri Maryam, son da na ke miki ne ya jawo wannan. Ina son ki fiye da tunanin mai hankali"

"Muntari dont do anything stupid. Ba zan yafe ma ka ba"

"Ina da kyau Maryam na fi Tijjani kyau, na fi shi kuɗi yanzu, na fi shi komai. Miyasa ki ka zaɓe shi? Miyasa ba za ki rabu da shi ki dawo gareni ba?"

Wani yunƙuri ta yi da ƙarfi ta tura shi tana gasa ma sa cizo a kumatunsa.
Hakan ya sa ya ɗage hannunsa yana ƙoƙarin shafa wajen. Ita kuwa ta samu daman sauka daga kan gadon ta yi hanyar waje da gudu.

Tana saukowa daga stairs ko takalmi babu ta ji muryan sa a bayanta yana cewa ta tsaya dan Allah. Saura stairs shida ta sauko ƙasa ya damƙo ta hakan ya sa su ka fara kokawa bisa kuskure ya tureta sai ga shi ta tumbling ta faɗo ƙasa. Hakan ya sa shi ƙwalla sunan ta da ƙarfi MARYAMMMM...

***

Tunda Likita ya ma ta bayanin rasa babies É—inta da ta yi ta ke kuka.
Three months twins É—ina sun tafi, abinda zuciyarta ke ta maimaitawa kenan.

Muntari ne ya shigo bayan fitan Likitan. Tana ganin sa ta sa ƙara tana cewa ya fita.

"Maryam ba niyya..."

"Get out, Muntari get out"

Kar ta tara ma sa Jama'a hakan ya sa ya fita yana jin ɗaci a ransa. Bai yi niyyar ƙuntata ma ta ba, niyyar sa ta yarda da soyayyar shi ta bashi dama tunda yanzu ya fi T J komai.

Kwana biyu da Maryam ta yi Asibiti ba ta yarda Muntari ya zo kusa da ita ba. Kuka kam ta yi shi harta godewa Allah. Bayan ɓarin da ta yi ba ta wani ji ciwo ba sai ɗan goshinta da ya fashe kaɗan kuma anyi ɗinki a wajen.

Bayan sati ɗaya da ta samu sauƙin jikinta ta je gidan Hajjo ta shiga har ɗakin Iya dan ba ta sameta a falo ba.

"Ya zaki shigo min É—aki haka kawai ba ko sallama"

"Ke ki ka haifi Muntari ko? Na kawo ƙarar sa for the first and last time, kaman yadda ki ke yiwa Tijjani magana ya ji ina so ki yiwa Muntari magana ya kama girman sa, ya kama girman sa ko kuma wallahi sai na yi sanadiyar da zai ƙarisa sauran rayuwar sa a kurkuku"

Iya ta gyara zama ta ce "ikon Allah. Ke gaki Alkalin duniya ko, to ki rufe shi mu gani. Wai ni kam kin auri Yayan sa na haƙura miye za ki je kwartonci wajen ƙanin sa? Saboda yanzu Allah ya buɗa ma sa yafi mijin ki arziƙi shine za ki koma wajen shi kwartonci ko? To bari ki ji idan har anyi duniya dan Muhammadu to ba abinda Muntari zai yi da ke. Ki fita harkan sa, waya sani ma ko cikin ba na Shehu ba ne za ki zo kina ɗagawa mutane hankali. Sai mi dan kin yi ɓari akan ki aka fara ɓari a duniya ne"

"Abinda za ki ce kenan? To ki sani matuƙar dabban da ki ke kira ɗan ki ya cigaba da bibiyana zan shayar da ke mamaki. Zan nuna miki duk iskancin sa bai fi ƙarfin hukuma ba"

Daga haka ta fita daga É—akin. Duk wani faÉ—an ma da tayi niyyar yi ta haÉ—iye.

Ranan da Hajjo ta zo duba ta a asibiti ta ke ce ma ta wai Muntari ne ya zo gida ya sanar mu su ta yi ɓari. Munafuki ya gaya mu su ta yi ɓari amma bai iya gaya mu su sababin da ya jawo hakan ba...

Gaba É—aya ta shutting Muntari daga duk wani abin da zai haÉ—a su. Yaranta ma ta hana su mu'amala da shi. Hatta motan sa ta hanasu shiga, ta nemo mu su dreban su na da.

Muntari ya shiga ruɗu sosai da yadda Maryam ta shata layi tsakanin su. Bai zo dan haka ta faru ba, abin da ya sha da sassafiyar ranan da abun ya faru ne bai sake shi ba lokacin da ta zo har ya sa shi ƙoƙarin nemanta ta karfi. It was never his intention ya sameta da ƙarfi, so ya ke ta zo gareshi a matsayin masoyiya yadda shi da ita za su nunawa junan su SO

***

*Bayan shekara biyu*

"Tijjani Zaytoonah get down"

Fiskarta shame-shame da hawaye da majina ta ke roƙon sa " Uncle I'm sorry"

'Yan aji kuwa sai dariya su ke ma ta.

"Tijjani Zaytoonah get down from that desk if i..." ya kai ma ta duka ta yi saurin komawa É—aya desk É—in tana ihu.

Ita ce ƙarama a shekaru amma kuma tafi kowa girman jiki. 'Yan ajin daga ma su shekara shaɗaya ne sai shabiyu amma Tijjani Zaytoonah Abubakar 'yar shekara goma ce da wata biyu. Akwai wani da su ke cewa Smally saboda guntu ne sosai shima shekarun sa goma amma kuma sai ƙwazo. Haka itama Zaytoonan ƙwazonta yayi yawa, shiyasa ma ta zana common entrance nata a primary 4 kuma ta ci.

Yanzu haka Sani da ke zaune a seat ɗin bayanta ne a aji ya ma ta waƙan 'Zaytoonah is a Big Fat Girl' shine ta ji haushi ta chaka ma sa biro a gefen hancinsa har wajen ya ɗan kumbura. To da Uncle Haroon form master ɗin su ya shigo shine ya samu Sani na kuka, ya tambayi bahasi 'yan aji su ka faɗi abinda ya faru.
Ya yiwa Sani bulala biyu saboda ya tsokani Zaytoonah ita kuma ya ce zai ma ta bulala uku saboda ta cakawa Sani biro. To tunda aka yiwa Sani bulala Zaytoonah ta ɗale saman desk tana kuka. Idan akwai abinda Zaytoonah ke tsoro to bulala ne. Ko a Islamiyya idan ta makara ko ba ta iya karatu ba Malam ya ce zai dake ta to drama ake yi ƙarshe sai dai a sata tsintar datti ko kneel down amma ba za ayi dukan ba.

"Tijjani Zaytoonah get down" Uncle Haroon ya daka ma ta tsawa. Ta fara ƙoƙarin saukowa sai ta ga ya ɗaga bulalar sama hakan ya sa ta yi baya da sauri ta tsallaka wani desk ɗin. Ai kuwa ya bi ta da gudu zai dake ta, ta zo za ta tsallaka wani desk ɗin ta zame ta faɗi yijif a ƙasa. 'Yan Aji mi su ka samu ban da dariya hatta Sani da aka daka shima dariyan ya ke sosai.

Uncle Haroon ya zo ya taimakawa Zaytoonah ta tashi saboda tunda ta faɗi ta ke kuka ta ƙi ko motsawa. Maimakon dukanta da ya ke son yi da sai ya koma rarrashinta yana ƙoƙarin duba hannunta ko ta ji ciwo.
Sai da ya dakawa 'yan Ajin tsawa kafin su ka tsakaita dariyan.
Ranan dai har aka gama lesson ɗin ƙarshe Zaytoonah ba ta dena kuka ba saboda yaran ba su dena ma ta dariya ba har da wata Kelechi ta hau desk ɗin tana gwada faɗuwan Zaytoonah.

Da aka tashi kuwa da hawaye ta tafi gida Manu na tambayarta ko lafiya amma ta ƙi kulashi, da ke Salman har yanzu yana primary session ya riga ta tashi. Shi kuma Auwal yana SS1 kuma ba a makarantar su ya ke ba.

Da ta je gida kuwa Maryam ta tsareta da tambaya amma ta ƙi kulata sai kuka. Ganin kukan ya koma na shiririta sai ta ƙyaleta. Abinci da Kuka sun zama kaman daily habit ɗin Zaytoonah ne.

Da yunwa ya isheta da kan ta ta haƙura da kukan ta wuce kitchen ta je ta ɗauko abincin ta ta hau ci. Tana ci tana yiwa Maryam da ke goge TV complain ɗin abincinta ya yi kaɗan kuma nama biyu kawai aka sa ma ta bayan ta ga ɗazu Salman ya ci nama uku.

"Ban sa ki dole sai kin ci ba, ki ajiye anjima Almajirai za su yi bara sai na miƙa mu su, su kan ko ba nama za su ci su sa albarka"

"Hhhenn dama Mommy you dont love me, that's why i miss my Daddy so much"
Chapter 35 · 0% Book details