Sashe 143
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa ya taya shi murnan samun lafiya da yai. A iya zamansa a wannan gari kyawawan halayen sa ya kawar da zargi da ake ma sa farko-farkon zuwan sa garin. Ba a taɓa kamashi da banzan hali ba. Abu ɗaya mutane su ka fi aibanta shi da shi wato rashin aure. A duk lokacin da aka ma sa zancen aure to baya so. Akwai lokacin da wani abokin sa ya ma sa jagora wajen neman auren wata bazawara amma ko da aka kai gaban iyayenta su ka ce ba za su ba shi ita ba saboda ba a san asalin sa ba. Da ke dama Malam Shehu ba son auren ya ke ba ya watsar da zancen. Dayawa mutane sai su ka ɗauka ko bashi da lafiyar gaba ne.
"Ni mutumin Ringim ne amma a Zaria na ke zama"
Malam Zulkiflu yai kabbara
"Ina da iyali. Mata na biyu. Ina da 'ya'ya..."
Ya É—aga yatsar sa ya fara irgawa "Princess Zaytoonah, Aisha Humairah, Salman da Abubakar Sadiq"
"Sadiq Sickler ne, ban san ko har yanzu..." kuka ya kuɓce ma sa.
Malam Zulkiflu ya shiga ba shi haƙuri tareda jaddada ma sa Insha Allahu zai tarar da iyalin sa lafiya.
Idan da ta tashi ne a ranan ya ke son komawa ga iyalin sa amma alfarmar da Malam Zulkiflu ya nema akan ya bari sai washegari ya sa shi haƙura.
Daren ranan kasa bacci yai yana tunanin ya zai tarar da iyalin sa. Ƙila Zaytoonah da Humairah sun yi aure, ƙila Salman ya gama Jami'a ko ya kusa gamawa. Ko Zaytoonah ta dena damuwa da ƙiban ta?.
Akwai abinda zuciyar sa ke hasasowa amma ƙoƙari ya ke ya danne saboda barazanar da abin ke yi ga nitsuwar sa.
"Ko Maryam ta yi aure?" Ya faɗa daga ƙarshe yana me dafe ƙirjinsa da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Kusan Asuba da bacci ya tafi da shi yai mafarki mai daɗi wai gashi nan tareda Iyalin sa suna zaune cikin wasa da dariya wanda ke nuni da tsantsan farinciki. Cikin mafarkin ya ga wai jikokin sa biyu na wasa da gemun sa. Lokacin da ya farka addu'a ya shiga yi yana mai fata mafarkin sa ya zama gaskiya...
***
"Mommy na tafi gidan su Iya"
"Allah ya kiyaye hanya" ta faÉ—a ba tareda ta kalleta ba.
"Mommy" Zaytoonah ta faɗa a shagwaɓe
Mommy ta É—an zare eye glass É—in ta ta kalli Zaytoonah ta ce "ya aka yi Mrs Millionaire?"
"Mommy is not fair. Shikenan kin fi damuwa akan na zauna da Daddyn Raziya even if i'm not happy?"
"Allah ya kiyaye hanya Zaytoonah. Ki gaishe su"
Zaytoonah ta kumbura fiska. Mommy ta ƙi fahimtar ta, ta ma ƙi bari su sake magana akan zuwan ta. Ta ba ta haƙurin siyan gida da ta yi out of anger amma still Mommy ta ce ba ruwanta itakam yanzu ido ne na ta.
Zaytoonah za ta fita sai ga Salman ya shigo rai a ɓace. Jakar sa ta goye ya cilla saman kujera.
"Ya dai?" Mommy ta faÉ—a tana kallon sa.
"Mommy saura sati biyu mu fara exams fa, exams ɗin ƙarshe fa but wai ASUU sun tafi strike"
"Ba warning strike ba ne"
"Mommy to ai daga warning É—in ne ake zarcewa"
"Be optimistic Bro, za su dawo nan da two weeks ɗin Insha Allah. Kafin nan ma ƙila ka gama project ɗin ka" Zaytoonah ta faɗa
"Gara su dawo fa, saboda gaskiya ni ina gamawa Aure zan yi, ba zan iya da bokon nan ba"
"Lallai Salman. Yanzu har ka kai aure?"
"A'a ban kai ba. Sai na shekara saba'in zan kai aure" yai maganar yana watsa ma ta harara ita kuwa ta fara dariya.
Sai da ta gama dariya tukunna ta juyawa za ta tafi Salman ya tambayeta ina za ta je da rana tsaka ba tareda Alinah ba. Ta ce za ta je gidan su Iya ne, Humairah ta mu su É—anwake.
"Ke dai da kwaÉ—ayi"...
A wani madaidaicin tray na silver Humairah ta zuba mu su É—anwaken su ka zauna a tsakiyar falo suna ci iskar fanka na kaÉ—a su.
"Anty Zaytoonah har yanzu fa Hamma Auwal shiru, kuma wallahi Idris ya ce zai turo"
Sai da Zaytoonah ta kai lomar ɗanwake guda biyu kafin ta kora da zoɓo mai sanyi da ke gefe sannan ta ce to ki gaya ma sa mana.
"Na ce ma sa mi?" Humairah ta zaro ido
" ki ce ma sa saurayin ki zai turo iyayen sa, ki ji mi zai ce"
"Ni gaskiya ina tsoro. Sai dai idan ke za ki gaya ma sa"
"A'a ke za ki gaya ma sa sai ki observing reaction É—in sa. If you see any hint of jealosy, 'yar uwa he's into you kawai"
"Allah Anty?"
"I'm very sure Airah"
Humairah ta fara murmushi.
"Ƙaromin ɗanwaken nan kaɗan"
Humairah ta tura ma ta sauran gabanta dan ita kam ta ƙoshi...
***
Shekaru shaɗaya ba wasa ba ne. Duk da dai a inda ya rayu akwai cigaba na rayuwa sosai amma shigowar sa Zaria after all this years sai garin ya ma sa girma, ya ma sa sabo sai ya zama tamkar bai taɓa zama a garin ba.
Daga inda aka sauke shi a tasha ya nemi keke wanda ya ma sa kwatancen anguwar su. Anguwar ta cika ta yi girma shiyasa yanzu kusan anguwanni uku ne cikin É—aya da ya sani a da. Sai da yai kwatance sosai kafin daga bisani daya furta sunan gidan Alhaji Ilyasu Mai Auduga mai keken ya ce ya san wajen farin sani.
Malam Shehu ya riƙe bagco bag ɗin da ya taho da shi da kyau. Duk wani abinda ya mallaka a chan ya kyautar wasu kuma ya sadakar da su. Tsarabar da Malam Zulkiflu ya bashi ne kawai a cikin jakar da ya riƙo.
Koda su ka shiga anguwar sabbin gina-gine ya sa bai gane gidan ba har sai da Mai Keken ya tsaya ya ce "mun iso"
An chanja fentin gidan da gate É—in gidan.
Cewa yai Mai Keken ya ɗan yi gaba saboda ba nan zai sauka ba. Sai dai har su ka kusa ƙarisa layin bai gane gidan sa ba. Ƙarshe ya sauka a keken ya fara dawowa baya yana irga gidajen da ya sani a wajen da har ya kai gidan da ya ke tunanin nan ne gidan da ya siyawa Maryam, sai dai yanayin yadda aka sauya fasalin gidan completely sai ya ji jikin sa yayi sanyi ko dai sun tashi ne? Ko dai wasu ne a wajen yanzu?...
Tunda Junior ya dawo daga makaranta yaran ke ta wasan banza a falo. Sune ma su ka tashi Alinah da ke bacci a É—aki. Mommy ta É—aukota ta goyata saboda kuka da ta ke yi, gashi uwarta daga tafiya cin É—anwake ba ta dawo ba.
Daga ɗaki Salman da ke ƙoƙarin baccin rana ya daka wa yaran tsawa tareda cewa idan ya zo ya same su a falon sai ya karya ƙafar su.
"Ku je compound ku yi wasa" Mommy ta faÉ—a dai-dai za ta shiga kitchen.
Yaran su ka fice daga falon da gudu wannan na cewa ayi ball wannan na cewa tseren keke za su yi.
A chan ɓangaren Zaytoonah kuwa kaman da wasa tana duba wayarta sai ta shiga duba status ɗin mutane, nan ta ga status ɗin Ghazala inda ta ga ta ɗaura hoton ta da na Justice a cikin jirgi, Galadima na zaune riƙe da jarida ta mu su selfie ɗin. Duk da idon sa na kan jaridar ne amma ba ƙaramin kyau yai ba. Hoton ba na yanzu ba ne, dan ta tuna wani lokaci da aka yi biki a Yola shine su ka je tareda ita. Lokacin ma ta zo Zaria yin wani abu su ka tafi amma dan neman tsokala sai da Ghazala ta tura ma ta hoton. Ranan ta gani ta kwana da kishi.
Abinda aka rubuta a ƙasan hoton ne duk ya dagula ma ta lissafi *7days to our 2nd honeymoon trip. Guess where we are heading to?*
Wato ya saketa, yayi banza da ita yanzu kuma sai honeymoon.
Da farko danne zuciyarta ta yi kamar ba komai musamman da ya ke Iya ta joining na su a falon. Amma daga baya ta miƙe ta wuce ɗakin Humairah. Tana shiga ta rufo ƙofa ta fara kuka. Ta rufe bakinta dan kar su Iya su jiwota.
This past two days tanayi kaman ba ta damu da rabuwan da su ka yi da Galadima ba, but deep inside her ta san ƙarya ta ke yi. She loves him, she misses him, she wants to be with him badly and yet a lokaci guda kuma she's angry and she hates him...
Malam Shehu na tsaye a bakin gate É—in ya rasa ya zai yi ya shiga. What if ba iyalinsa ba ne a gidan yanzu?
Hayaniyar yara da ya ji daga ciki ya sa shi ƙwanƙwasa gate ɗin gidan.
"Hashir je ka duba waye?"
"Ba zan je ba" ya faɗa yana cigaba da tuƙa keken sa. Sun sani sarai idan su ka fita da keken waje Uncle Salman sai ya zane su. Akwai wani zuwa da su ka yi su ka fita waje da keke suna wasa wani mai babur ya buge Hadid. Allah ya sa abin ya zo da sauƙi bai wani ji ciwo ba sai buguwa kawai da yai kaɗan.
Junior na gyara kachar keken sa da ta zube shiyasa kawai Hadid ya nufi gate ɗin ya buɗe tunda Hashir ya ƙi zuwa.
Malam Shehu ya kalli yaron da ya buɗe ƙofan bugun ƙirjin sa ya yawaita. Ba ta inda zai ce yaron yayi kama da wanda ya sani. Shikenan ta tabbata iyalinsa ba sa wajen.
"Malam lafiya? Wa ka ke nema?"
Hadid ya jera ma sa tambayoyi lokaci guda.
Malam Shehu ya gyara riƙon jakar bagco ɗin hannunsa ya ce "nan ne gidan Maman Zaytoonah?"
Yes ya faɗa haɗeda gyaɗa kai hakan ya sa bugun ƙirjin Malam Shehu ya ƙaru.
A hakan dan ya ƙara tabbatar da Maman Zaytoonan da ya ke nufi shi yaron ke nufi ya ce "ina nufin Maman Zaytoonah da Salman"
"Yes, ai GrandMa É—in mu kenan"
"GrandMa É—in ku?, as in Kakar ku?" ya faÉ—a a ruÉ—e.
Hadid ya gyaÉ—a kai.