← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 161

Sashe 160

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahil da Amir ba inda ba sa zuwa da ƙafafun su. Rigiman su kuwa tafi ta su Hashir da Hadid. Bayan su kuma ga naughty Alinah. Da ana cewa Falaq ce ba ta son magana amma wannan ta taka Falaq, tana ƙara girma kuwa kamannin ta da Falaq ɗin na sake bayyana. Haske da jiki kawai Alinah za ta fi Falaq amma kamannin su ta fiska kam kusan 90% sak ne.

Sai yanzu ne ma Zaytoonan ke nuna jarumta, kulawa da 'ya'yan ta da 'ya'yan mijin ta was not easy, duk da kuwa yanzu kyakykyawar alaƙa ne tsakanin ta da yaran.

Raziya ta gama secondary school ta ƙara hankali sosai. Yanzu kam har secrets ɗin ta tana gayawa Zaytoonah. Tun kafin ma ta faɗawa Zaytoonah ta riga ta gano soyayyar da ke tsakanin ta da ɗan uwan ta Ahmad. Ta san Galadima ba zai taɓa aurar da ita a sixteen years ba shiyasa aka saka Galadima a duhu zuwa lokacin da za ta kai kaman 18yrs sai a sanar da shi. Tana dai kula da lamurran yarinyar dan da ta yiwa Mommy maganar shawara ta ba ta akan ta sa ido akan ta sosai duk da cewa Ahmad ɗan uwan ta ne amma yanzu ba a shaidar maza 100%. Idan wani abu ya faru da Raziya sunan ta za a fara kira saboda ita ke zaune da su kuma kaman uwa ta ke a wajen ta.

Yanzu ma maganar karatun ta ne ya kawo saɓani tsakanin Galadima da Zaytoonah. Raziya ta nuna tana son ta yi karatu a ƙasar waje shi kuma Galadima ya ce ba inda za ta je a Nigeria za ta yi, ba zai barta ta je nisan duniya da ƙarancin shekarun ta ba. Zaytoonah kuma ta nuna ba komai acikin tafiyar Raziya ya dai bi ta da addu'a kawai shine fa Galadima ya hau fushi.

Lokacin da ya shigo É—aki tana haÉ—a ma sa kaya dan gobe za su wuce Zaria saboda bikin sallar Layya da za ayi, nan da kwana uku.

"Sannu da zuwa Sayyadi"

"Yawwa"

Kallon sa ta yi sadda ya zo ya shige banɗaki yana wani shan ƙanshi.
Ta sani itama ba ta yi adalci ba yadda ta gaya ma sa magana gatsal haka ranan. Duk da daga baya ta ce yai haƙuri amma still bai sake kulata ba.

*"ni na rasa yanzu ko tsufa ne ke taɓa ka. Idan har @51 kana irin wannan idan ka je 60 ya dai za mu ƙare a gidan nan. Idan fa mace za ta lalace ko tana karƙashin inuwar ka ce sai ta lalace. Ka barta ta tafi dan Allah, ko da anan ɗin za ta yi karatu we can only pray for her Allah ya kare mana ita"*

Yadda ya tashi tsaye ya shige ya barta zaune a falon ne ya sa jikin ta yai sanyi tabbas yau ta tsokalo Dodo.

Lokacin da ya fito daga banÉ—aki É—aure da towel ne tana zaune a bakin gado tana jiran sa.
Lokacin da ya ke ƙoƙarin shafa mai ne ta karɓi man a hannun sa ta fara shafa ma sa, bai musa ma ta ba sai ma maida kan sa gefe da yai.

"Allah ya ja zamanin Daddyn Alinah. Ka san Allah yau 'yar ka sai da ta bani tsoro a gidan nan"

Juyowa yai da sauri dan indai maganar 'ya'yan sa ne ba ya wasa da su musamman ma Alinah.

"Mi ya faru?" Ya tambaya ganin ta yi shiru.

Ƙaramar dariya ta yi ta ce "ai yanzu ka yi magana da ka ji zancen gimbiyar ka"

Ganin ya ɓata rai ta ce "haba Masoyi na, na ba da haƙuri fa, har sau biyu. A taimaki baiwar Allah, punishment ɗin ya isa haka Uban biyu biyu"

"Ki haÉ—a min tea"

"An gama Ranka shi daÉ—e" fiskarta É—auke da murmushi. Bayan ta taimaka ma sa ya saka kaya sannan ta fita daga É—akin ta yi kitchen da sauri.

Sai da ta isa falon ne ta tsaya turus ganin dramar da ake yi a wajen. Da sauri ta koma É—akin ta ce Galadima ya zo ya ga ikon Allah a wajen yaran nan.

Dukkan su biyu suka zubawa yaran ido.

Alinah ce kaÉ—ai zaune a kujera wani crown ribbon É—in ta da aka sa ma ta lokacin birthday É—in cika three years ne akan ta.
Hashir na ma ta fifita yayinda Ahil, Amir, Hashir da Suhailah su ke durƙushe a ƙasa wai ana Fadanci.

"Ina ga wannan karan idan mu ka je Zaria gidan Hajia Abu zan je na jibge 'yar nan, ba zan iya da wannan mulkin ba"

"Sai ki yi ai. Mulki ai gadon gidan su ne dole a gani a jikin ta"

"Hmmmm"

Ƙarasawa yai wajen yaran ita kuma ta wuce kitchen ɗin.

***

Da wasa ta É—auki maganar Galadima lokacin da ya ce hawan bana harda Alinah za ayi.
To her surprise sai gashi da kan sa ya kawo ma ta kayan da za a sawa Alinah.

"Sayyadi ba dai maganar Raziya ka É—auka ba"

"Ki shirya min ita"

"Daddyn Alinah cikin É—inbin mutane, ka san yadda..."

"Allah zai kare min ita"

Mi za ta ce kuma tunda dai 'ya dai tashi ce.
Washegari hawan sallah da aka yi kuwa harda Alinah. Dokin ta ke gaba yayin da na Galadima ke bayan ta. Mutane huɗe ke riƙe da dokin na ta suna kula da ita. Ranan kam ta nuna cewa ita ɗin 'yar Baban ta ne. Yadda ya ke murmushi a wasu waje, wasu wajen kuma ya haɗe rai haka itama ta ke yi. And duk inda aka ratsa kowa na ƙoƙarin ɗaukan hoton kyakkyawar yarinyar da ta cinye hawan wannan shekara. Wasu wajen idan su ka wuce sai ka ga yara da manya kowa na ƙoƙarin miƙa ma ta kyauta wanda hadiman ta ke karɓa ma ta.

Ba a jima da fara hawan ba Hajia Abu ta kira Zaytoonah da ke cikin ma'aikatan gidan tana lura da yadda ake ta gudanar da girke-girke, hidimar sallah was always tough for her. Tun safe har dare ba ta samu isashshen hutu, idan aka fara fitar da abincin sai ka ɗauka duka anguwar za'a ciyar. Ga baƙi nan ma su zuwa ta ko'ina.

"Zaytoonah da hankalin ki ki ka bari aka fita hawa da Alinah? Idan wani abu ya same ta fa? Ba wannan ba ma idon mutane fa guba ne"

Yau É—aya ta ji daÉ—in maganar Hajiya Abu, atleast dai yau ta damu da 'yar ta duk da ma ita É—in mace ce.

"Na ma sa magana ya ce wai na ma ta addu'a kawai"

"Allah ya kyauta, ni ban san miyasa ya ke son ta fiye da sauran ba. Yadda ya ke ji da ita ko Hassan da Hussain ba ya jin su haka. Allah dai ya tsare"

Zaytoonah ta girgiza kai tana jinjina ƙarfin hali irin na wannan mata. Yau da ita ta haifi Galadima da sun shiga uku.

Bayan Hajia Abu da ta kira Mommy ma sai da ta kira ta ma ta faÉ—a. Ita kam daga baya ma dariya su ka ba ta, ba fa ita ta É—au Alinah ta É—aura a doki ta turata waje ba fa. Wanda ta ke amsa sunan sa ne ya jagoranci komai.

An dawo da Alinah da wuri amma Galadima kam kafin ta samu kan sa sai kusan ƙarfe sha ɗaya na dare. Ko da ya dawo ma yana tareda baƙi ne all through daga baya kuma ya sake fita.

Taimaka ma sa ta yi yai wanka da ruwan zafi sosai. Gaba ɗaya jikin sa ne ke ma sa ciwo musamman kwankwason sa. Zama a kan doki, zama a fada, zama don tarban baƙi. Kayan da ya saka ma su kauri da naɗin turban da ke kan sa tun safe har yamma duk ya weighing na shi down.

Kwantawa yai ruf da ciki Zaytoonah ta shiga yi ma sa matsa.
Itama 'yar ta shi ta jigata sosai dan ƙarshe ma Zaytoonah na ba ta abinci ta buge da bacci. Zaytoonah ta ce rigimammiya gaba ma ki ƙara. But secretly kuma ta ji daɗin hawan da aka yi. She's proud of being the mother to Alinah.

Tun kafin a ƙarisa ma sa dannar shima bacci ya ɗauke shi. Sai da ta fita ta leƙa ɗakin 'yan'yan ta ta tabbatar kowa na bacci lafiya kafin ta dawo ɗakin Galadima ta kashe wuta ta kwanta kusa da shi da murmushi ɗauke a fiskarta

***

A watan da za a kai Raziya makaranta a Malaysia ne su ka je ƙauyen su Mommy, inda Mommy ta buɗe Asibiti da Makaranta a ƙauyen mahaifinta wato Ukwuohia mai suna *Caroline and Patrick Memorial Hospital* da *Caroline and Patrick High school* in memory of her parents.
Kwana uku Zaytoonah ta yi a ƙauyen ta koma Abuja saboda ita da Galadima za su raka Raziya, daga nan kuma su wuce Las Vegas. Farha ta haifi ɗa namiji watan da ya wuce tunda ba ta samu zuwa bikin ta ba ya kamata ta je ta ga baby boy wanda ya ci sunan Ayman Muhammad Chu. Nonetheless kuma ya kamata ta je ta duba lafiyar business ɗin ta dana 'ya'yan ta.

Su Mommy kam za su kwana biyu a chan dan wani mini vacation za su yi kafin su koma Zaria.

Mata da Miji sai Allah. A hankali Zaytoonah ta shawo kan Galadima ya amince Raziya ta yi karatu a Malaysia amma za ta zauna a gidan wani cousin É—in Galadiman ne ta wajen Uwa.
Maganar Ahmad da Raziya na nan dan last last Zaytoonah ta fito fili ta faɗawa Galadima komai shi kuma ya ce a bari zuwa shekara biyu idan ta ƙara girma. Shima Ahmad ɗin ƙoƙarin yin masters na shi ya ke dan haka abun zai faɗa mu su a dai-dai.
Chapter 160 · 0% Book details