← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 161

Sashe 107

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bahijje ki shigo mana"

Matar ko da za ta girmi Zaytoonah to ba zai fi shekara É—aya ko biyu ba.

"Hajiya kina da baƙi a falo"

"Baƙi kuma?, Ok, ki ce mu su ina zuwa"

Doguwar riga ne a jikinta dan haka gyalen sa kawai ta yane ta fito. Tana saukowa ta sa dariya " yanzu dama ku ne, shine Bahijje wai na yi baƙi"

"Af baƙin ne ai tunda dai ba a gidan mu ke ba"

"Azma har da ke ko"

"Anty Zaytoonah ai gaskiya ta faÉ—a"

"Haka ma za ki ce, to na fasa ba ki ƙanina"

"Dama mi za ta yi da shi muna da Munnir a gefe"

"Cin amanar da za ayiwa Salman É—ina kenan. To ba zan yarda ba"

Haka dai su ka yi ta tsokana tsakanin su.
Muhsinah ta ce sun zo danne ƙirji ne.

"Ba danne ƙirji ba Allah ya sa danna ɗuwa..."

"Lalala! Zaytoonah haka ki ka zama"

"Dama haka na ke".

Zaytoonah ta idar da sallan Azahar kenan Azma ta miƙo ma ta waya wai an kira ta. Tana karɓan wayan sai ga text ya shigo.

*Alhamdulillah! Allah ya tabbatar, duniya ta shaida Gimbiya Ghazala Amarya a gidan Yarima Yunus Galadiman Zazzau*

"Ghazala?" Zaytoonah ta furta a fili cike da mamaki.

"Wace Ghazalar?" Muhsinah da ke shan farfesun kayan ciki ta tambaya.

"Ghazala ya aura. Ghazala ƙanwar tsohuwar matar sa"

"Lallai kam. Dama duk take-taken ta dan ta aure shi ne. Zaytoonah kina da aiki a gaban ki"

"Hmm" kawai ta faÉ—a ta ajiye wayar.

"Ina text ta miki?" Muhsinah ta tambaya

Zaytoonah ta gyaÉ—a kai.

"Ki yiwa shegiya reply ta san cewa kema a shirye ki ke da ita"

Kaman ba za ta biyewa Muhsinar ba amma da Azma ma ta sa baki sai ta É—au wayar ta rubuta ma ta reply kamar haka:

*marhaban-marhaban Anty Amarya, ko Mama Amarya ne ma?😂 Uwargidan Galadima tana mi ki maraba da wannan matsayi. Daga ƙarshe dai duk wani jeka ka dawo, wani tarairayan Yara na ƙarya, wani kamala na bogi da aka yi ta yi yayi rana kenan. Ayyah! Congratulations fah, wannan matsayi abun murna ne gaskiya*

Muhsina ta so ta ƙara ma ta da wani abu amma Zaytoonah ta ce hakan ma yayi.

Gaskiya sun ma ta mutunci dan tun safe har yamma lis kafin su ka bar gidan. Ba ƙaramin jin daɗin zuwan su ta yi ba, zuwan su ya sawwaƙa ma ka kaɗaici da ƙunci da ta ke ji...

Kwana biyar da É—aura auren aka zo ka gyarawa Ghazala É—akin ta, an cire wa su kaya an saka sabbi wasu kuma an bar su yadda su ke.

Exactly kwana takwas da aure Ghazala ta tare a gidan. Ƙawayenta da wasu 'yan uwan ta ne su ka rakota. Sun zo da ɗan rana ne dan da safe su ka taso daga Zaria. Da ke Maman Tope ne da aiki shiyasa tun kafin zuwan su ta ce ma ta ta shirya abinci na tarban tawagar Amarya. Justice ya riga ya sanar ma ta tun jiya cewa yau ne Ghazala za ta tare.

Lokacin da su ka iso fiska sake ta fito daga ɗaki ta sauko ƙasa ta zo ta gaishe su.

"Saura ki ƙi fitowa ki karɓi Amarya"

"Ai dole na fita kin manta ni ce fa Uwargida"

"Uwargidan da ta yi wasa da damanta ba"

"Wuce nan kuma ai" ...

Hiran su kenan É—azu a waya tareda Muhsinah.

Su bakwai ta gani idan ka haÉ—a da Ghazala takwas. Mace É—aya ce tsohuwa a cikin su amma duk sauran sa'annin Ghazalan ne.

Tsohuwar ce ta ce " to Uwargida ga amanar Amarya mun kawo miki"

Kusan mutum uku su ka kwashe da dariya. Ɗaya a cikin su ta ce "Inna kenan. Wannan formalities ɗin ai sai yara. Da ma cewa ki ka yi Hajia Ghazala ta riƙe amanar wannan buredin sai mu ce kin yi dai-dai"

"Wa ya ga buredi" wata ta faÉ—a a cikin su, hakan ya sa dukkan su kwashewa da dariya.

Zaytoonah ta danne ɓacin ranta ta ce "barkan ku da zuwa outdated bitches" daga haka ta juya ta bar falon...

Da dare Justice ya haɗa su ya mu su nasiha tareda faɗin yadda za a dinga rabon kwana. Duk wacce ya ke ɗakin ta ita ke da alhakin kula da abincin sa da ɓangaren sa.

"Rabon kwana my foot" Zaytoonah ta faÉ—a a ran ta.

Kusan tana shiga ɗaki ya shigo shima. Ajiye ma ta leda yai a saman kujera sannan ya tambayeta ko tana buƙatar wani abu ta ce ma sa ba komai.

Har zai fita sai kuma ya juyo ya ce "Princess Allah ya tashe mu lafiya"
Ta amsa da amin a ƙasan ran ta ko duba mi ya kawo ba ta yi ba ta kwanta...

Bayan ya koma É—akin sa yai wanka ya shirya kafin ya wuce É—akin Amarya wacce ke jiran sa tun É—azu.
Ya samu tarba na musamman a wajen Hajia Ghazala sai dai gamsuwar da ya ke buƙatar samu babu shi. The aftermath feeling da ya ke son samu na kwanciyar hankali, shauƙi da tsananin soyayya babu shi.

Zare jikin sa yai ya wuce banÉ—aki ya je yai wankan tsarki yai alwala ya fito kafin nan ya kwanta.

"Ina ga zai kyautu ki fara yin tsarki kafin ki kwanta hakan yana da falala da fa'ida"

Bai sake maimaita maganar ba haka nan itama ba ta tashin ba har bacci yai awun gaba da shi...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 52

Bismillahir Rahmanir Rahim

*The kids*

Sokali ɗaya Raziya ta yi ta miƙe tsaye za ta bar dining ɗin.
"Miya faru?" Justice ya tambaya
"The food is peppery Daddy" ta faɗa ranta a ɓace.
Zaytoonah ta kalli yarinyar ta kuma kalli Justice tana jiran ta ji mi zai ce.

"Ki je ki cewa Atika ta haÉ—a miki abinda za ki ci"

A fakaice ta kalli Zaytoonah ta ma ta harara kafin ta wuce ta bar dining area É—in. Zaytoonah ta girgiza kai kawai ta cigaba da cin abincin ta.

Jollof rice ta yi da ke haɗe da carrot da green beans da spring onion sai ta suya plaintain sannan ta yi pepper chicken. Idan ka cire pepper chicken ɗin da za ta iya cewa yana da ɗan yaji to jollof rice ɗin kam ko rantsuwa za ta iya yi akan bai yi yaji ba. Tun a Zaria Baaba Nafy ta ce ma ta Justice ba ya cin yaji shiyasa duk girkin da ta ma sa ta dinga ƙoƙarin saita shi. Su ɗin ma ba wani Yaji su ke ci ba a gida saboda Mommy na da ulcer da ciwon ƙirji, idan ta ci yana damun ta.

Sauran yaran hankali kwance su ka ci abincin sosai, naman ne ma ba su wani ci ba tana tunanin ko dan yayi yaji ne.

Ta so magana lokacin da Justice ya cewa Raziya ta je a dafa ma ta wani abin amma ta sawa bakinta sakata kar a ce daga zuwa har ta fara ƙorafin yaran.

Noodles da soyayyen ƙwai Raziya ta zo da shi a plate ta zauna dai-dai sun gama cin abinci dan Zaytoonah ma na tattare wajen ne. Sai da ta bari Justice ya tashi a wajen ta ce " mutum bai iya abinci ba ya dage sai yayi. Muna da professional cook ba za a bari ta yi aikin ta ba sai anyi shishshigi. Mtsww"

Zaytoonah ba ta kulata ba dan ta san neman faÉ—a yarinyar ke yi ita kuma ba sa'ar ta ba ce balle har ta biye ma ta...

Washegari da sassafe ta tashi ta fita dan ɗaura abin karyawa amma duk sammakon ta sai da tarar da Atika a kitchen ɗin. Ganin ta riga ta fara sarrafa abubuwa ya sa ta haƙura da girkin ta koma ɗakinta dama ko azkar ɗin safiya ba ta gama ba ta fito saboda yau Monday ta san yaran da Justice za su yi fitan sassafe.
Tana idar da azkar ta yi tilawan da za ta yi ta kwanta.

Kamar yadda ya saba bayan ya gama shiryawa ya sauko ƙasa dan ya karya kafin ya wuce office. Yaran tuni suna wajen dinning sun fara karyawa.
Sai da ya zauna sannan ya kalli Raziya ya ce "ina Antyn ku"

"I dont know" ta amsa tana cigaba da cin abincin ta.

Bai ɗau amsar ta a matsayin rashin kunya ba sai ma ya miƙe ya haura sama, kai tsaye ya wuce ɗakin Zaytoonah.

Lokacin da ya shiga tana bacci dan haka ya juyo kawai dan kar ya katse ma ta bacci.

Zaytoonah ba ta tashi ba sai kusan ƙarfe takwas na safe lokacin sun jima da ficewa. Ta yi wanka ta shirya sannan ta sauko ta shiga kitchen ta nemi abinda za ta ci. Sauran pepper chicken da ya rage jiya da ta ajiye a fridge ta ɗumama ta haɗa da tea da bread ta ci. Da ta gama ba ta yi gigin kiran Atika ba sai kawai ta wanke abubuwan da ta ɓata da kan ta.
ÆŠaki ta koma ta É—au waya ta kira Muhsina su ka sha taÉ—i tana tambayarta yaushe za ta zo ma ta. Bayan sun gama wayar ta kira Mommy su ka gaisa duk da ita É—in ma tana class.

Bayan ta gama gyara É—akin ta sannan ta buÉ—e laptop É—inta ta fara kallo. Ita ba gwanar kallo ba ce amma yawanci idan ta rasa abinyi kan ta zauna shiru sai ta kunna kallo ko ta É—au littafi ta yi karatu.
Wunin ranan haka ya zo ya shige cikin kwanciyar hankali. Ba ta yi girki da rana ba dan abincin da ta ci da safe ya isheta. Yoghurt kawai ta ɗauka a fridge ta sha. Da dare ba ta yi gigin yi wa Justice girki ba dan ba ta son abinda ya faru jiya ya faru yau. Al'amarin mai aikin gidan da ma Yaran musamman Raziya sai a hankali, ga Justice ɗin ma ba ta gane alƙiblan sa ba. Atleast tunda ta zo gidan shi ya kamata ya faɗa ma ta dokokin sa amma shiru yai tun jiyan. Ban da lokacin da su ka haɗu za su ci abinci da ya cewa yaran "ga Antyn ku nan ku ma ta biyayya" bai ƙara cewa komai ba...
Chapter 107 · 0% Book details