Sashe 96
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Galadima yai murmushi dan ya san ko ya ma ta bayani ba fahimta za ta yi ba. Duk da tazarar shekaru da ke tsakanin Hajia Abu da Ni'imar hakan bai hana su samun saɓani ba har ta kai ba sa ga maciji tsakanin su. Hakan ya samu Asali ne lokacin da Hajiya Abu ta turo Sadiq wajen Ni'ima lokacin tana ajinta na ƙarshe a Jami'a. Sadiq ɗan babban gida ne shima kuma mahaifin sa da Mijin Hajiya Abu Abokai ne na ƙut da ƙut. Ƙin auren Sadiq da Ni'ima ta yi shine mafarin faɗan na su kuma har yau ba sa shiri.
Hajiya Abu mace ce me son zuba iko da mulki a duk inda ta ke, tana da girman kai har na sayarwa.
Shi kan sa yayi mamaki da Maimartaba ya kira shi akan tabbatar da maganar da ya ji daga wajen Hajja wacce ta ke mahaifiyar Ni'ima kuma Uwar riƙon sa.
Ya riga ya sanar da Ni'ima akan ta ajiye maganar zuwa lokacin da za a gama case É—in Mommy kafin nan ya gama yanke shawarar abinda zai yi, sai gashi ita kam ta kai shi har gaba. Da ke dama an matsu yai auren shiyasa ma da aka sanar da Maimartaba da wuri ya kirashi dan ya ji ta bakin sa.
"Aka ce yarinyar Inyamura ce" Hajiya Abu ta faÉ—a ita a dole fa ba ta so Galadima ya auri yarinyar da Ni'ima ta kawo.
"Hajiya har yanzu ban yanke shawara ba tukunna, dan haka ina buƙatar addu'a Allah ya zaɓa min mafi Alkhairi" daga haka ya ma ta sallama ya fice daga falon ta, ba dan ta buƙaci ganin sa ba ma ba abinda zai kawo shi gidan.
***
Kallon Zaytoonah ta ke yi da ke bacci hankalin ta kwance. Gobe za su wuce Owerri saboda shigar da ƙara da za su yi. Mommy ta halarci last zama da aka yi a case ɗin da Zaytoonah ta jagoranta kuma ta ji daɗin yadda 'yar tata ta jajirce a wajen. She won the case kuma hakan na nufin Zaytoonah za ta iya tunkaran babban case kamar na ta. Whatever the outcome, za ta yi alfahari da cewa 'yar ta ce ta tsaya ma ta.
Wannan karan ba za ta yiwa 'yar ta dole ba. Duk min girma da daraja irin na Galadima ba za ta taɓa ba shi Zaytoonah a matsayin Alfarma ba, matuƙar ba Zaytoonan ce ta ce tana son auren ba.
Zaytoonah deserves to marry the person she love.
Haƙuri ta ba wa Ni'ima lokacin da ta kawo ma ta zancen da ya rikitata har ta ke tunanin anya ba za ace ita ta yiwa Galadima tallen Zaytoonah ba?.
Addu'a ta karanto a hannu sannan ta shafa a fiskar Zaytoonah kafin ta gyara ma ta bargo...
Kaman daga sama Chief Udodiri ya tsinkayi takardar kotu da ke tuhumar sa da abubuwan da ya jima da mancewa ma ya yi su.
Nkiru is alive? Ya furta maganar cike da rashin yarda. Mary-Nkiru dai da ta gudu shekaru kusan talatin da su ka wuce.
Da farko abin ma dariya ya bashi saboda tunanin ko 'yan 419 ne su ke son damfarar sa amma daga baya da ya tuntuɓi Lauyan sa ya kuma sa a ma sa bincike sai ya gano gaskiya. Hoton Maryam da aka kawo ma sa ya ƙurawa ido, tabbas ita ce Mary-Nkiru 'yar Yayan sa.
Nan da nan hankalin sa ya tashi. Bai san mi take da shi ba a matsayin evidence, ga uwa uba Sunan sa da zai ɓaci idan case ɗin nan ya fito fili tunda ga zaɓe na ta ƙaratowa kuma har an bashi ticket a jam'iyyar su.
Wannan ya sa ya kira zama da Lawyoyin sa dan a san ta inda za a tari matsalar...
Da Mommy da Auwal ne ke tare da ita kasancewa yau ne za a fara sauraron ƙara. Tun da Asuba ta kalli text ɗin Justice da ke ma ta Addu'ar samun nasara tareda nuna ma ta cewa ka da ta ji tsoro domin Allah na tareda ita. Su Mommy ma maganar su kenan har su ka isa court ɗin.
Kotu ya cika maƙil saboda Chief Udodiri ba ƙaramin mutum ba ne a Jahar. Wannan ya sa kowa ke son sanin yadda za ta kaya domin dayawa ba su yadda da wannan ƙara ba tunda abu ne da aka yi shi shekaru da dama da su ka wuce yawanci ma an manta yadda abin ya faru. Hatta a cikin 'yan uwa an riga an manta da labarin wata wai Mary-Nkiru.
Ranan da aka yi zama na farko kaÉ—an ya rage Zaytoonah ta yi hawaye saboda yadda Lawyan Udodiri ke kore duk wani magana ko tambaya da ta yi. Ikon Allah ne kawai ya sa aka tashi daga kotun nan lafiya ba tareda Zaytoonah ta yi kuka ba.
Gaba É—aya ta karaya da yadda abubuwa su ka tafi. Ba ta yi kuka ba sai da ta shiga banÉ—aki sannan ta zauna ta dinga kuka tana yi tana rufe bakin ta dan kar Mommy da ke É—aki ta jiyota.
An ɗaga ƙara zuwa kwana shatakwas ma su zuwa amma a yadda ƙaran ke tafiya ba su da wani hope a tattare da su ko kaɗan. Ita kan ta Mommy jikin ta yayi sanyi.
Sun fito daga hotel inda driver ke jiran su ya kai su Airport kenan sai ga wasu baƙaƙen motoci guda uku ma su kyau sun shigo harabar hotel ɗin.
Dreban su na ƙoƙarin ficewa daga hotel ɗin wani bodyguard yai saurin tsare shi.
Auwal da ke gaba ne ya fito yana yiwa bodyguard É—in magana da turanci yana tambayar ko lafiya zai shiga gaban su.
Magana ya ma sa tareda nuna ma sa motocin da su ka shigo wanda shima É—in daga É—aya daga cikin su ya fito.
Kamannin su É—aya sai dai É—aya ya fi É—aya furfura a gashin kai. Atleast iya banbancin da su Mommy su ka gani kenan lokacin da su ka fito daga mota yayinda waÉ—annan 'yan biyu su ka tunkare su.
Dukkan su biyu Mommy ke kallo tana son gaskata idon ta, dan waÉ—annan 'yan biyu suna yanayin kama da mahaifiyar ta.
" ke ce Mary-Nkiru Uzodinma ko?" ÆŠaya daga cikin su yai tambayar yana kallon Mommy.
Mommy ta gyaÉ—a kai.
"Ke ce 'yar Caroline Asibong?"
Maimakon Mommy ta bada amsa sai ta ce " ku ne ƙannen Mama na?"
Kuka ne ya kuɓcewa Mommy lokacin da mutanen nan su ka gabatar da kan su a matsayin Paul Asibong da Peter Asibong 'ya'ya ga Chief James Asibong. Ɗaya bayan ɗaya su ka rungumeta suna hawayen farin ciki. Maimakon su tafi Airport su koma chan gida sai kawai su ka bi Uncles ɗin Mommy a motar su daga Owerri har Calabar.
Tun a hanya su ka sanar da Mommy cewa Kakan ta na raye kuma yana tsananin son ganin ta. Tun lokacin da labari ya iso mu su cewa Caroline da mijin ta sun mutu ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba. Tun lokacin Chief James ya samu paralysed wanda daga baya ne da aka fita da shi jinya ƙasar waje shine ya samu lafiya.
Udodiri shi ya sanar da su Mary 'yar Caroline ma ta mutu shiyasa ba su neme ta ba. Sun koma America da zama wanda shekaru biyu kenan da dawowar su. Case É—in nan da Peter ya gani a Jarida ne ya sa shi bin bahasin labarin har ya gano gaskiyar lamari cewa Mary-Nkiru 'yar yayar su dai na raye ba ta mutu ba.
Gida ne mai girma, gini na zamani su ka sauka inda dukkan su suka isa wajen Kakan Mommy wanda ke zaune a kan wheelchair yana dakon zuwan su.
Babu tantama dai wannan jikar sa ce dan ga kamannin Caroline da ta ke da shi.
Batun komawa Zaria ajiye shi aka yi a gefe aka shiga hiran abubuwan da su ka faru. Chief James yayi kuka sosai da ya ga Mommy domin ganin ta ya sa shi tunowa da 'yar sa da kuma wautar da yai wanda yai sanadiyyar rasa 'yar sa Caroline. Da ace tun farko ya amince da aurenta da Patrict da ƙila duk waɗannan abubuwa ba su faru ba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata.
A gidan aka ba su masauki inda sauran 'yan uwa ke zuwa duba Mommy a matsayin ta na 'ya ga Caroline. Peter yana da 'ya'ya 'yan biyu mata kuma duka sun yi aure. Ɗaya na ƙasar Germany ɗayar kuma na zaune a Lagos da Mijin ta.
Shi kuma Paul 'yayan sa uku ne maza biyu mace É—aya. Baban É—an sa yayi aure yana America dan baturiya ma ya aura. Caroline wacce su ke kira da Carol itama ta yi aure tana Portharcourt sai autan sa Felix wanda ke Phd É—in sa a Yale University.
Chief James yayi alƙawarin duk yadda za ayi a hukunta Udodiri sai anyi dan ba zai taɓa yafe ma sa ba. Ba ƙaramin ja'in ja aka yi ba akan son ɗauke case ɗin daga hannun Zaytoonah da su ke son yi. Mommy ta yi biris akan ta yadda da 'yar ta ta kuma san Allah zai taimake ta. Daga ƙarshe dai haka su ka haƙura akan Zaytoonah za ta cigaba da case ɗin.
Kwanaki shatakwas ɗin nan a Calabar su ka yi shi ita da Mommy, Auwal ne ya koma saboda aikinsa, ba ƙaramin kulawa 'yan uwan Mommy na wajen Uwa su ke nuna mu su ba, duk da sun kasance Musulmai hakan bai rage soyayyar Mommy da 'yar ta a zukatan su ba, abinda su ka sani shine Mommy jinin su ce. Ance da sauran yaran ma sun yi hutu za a kawo su suma su ga 'yan uwan Mommy...
Kuka ta ke wiwi kamar wacce aka yiwa mutuwa. Tun da su ka fito daga court É—in ta ke hawaye.
Mommy ta nuna ma ta ba komai ba ne haka Allah ya rubuta amma ta kasa haƙura. Ji take yi da ta yi ƙoƙari fiye da haka da kotu ba ta yi watsi da ƙaran nan ba.