Sashe 97
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune ta ke wajen fountain inda ta ke zaune tana jin daɗin sanyin ruwan da ke ɓulɓulowa. Tun jiya ta kasa cin abinci, tun Mommy na lallashin har ta haƙura ta ƙyaleta. Ita safiyar nan ma tafiya ta so yi sai dai babu jirgin Kano ko Kaduna da zai tafi yau, na Abuja kuma tun ƙarfe huɗun Asuba ya tashi.
Idon ta da ya cika da hawaye ta sa hannu ta share. Ta cigaba da kallon ƙasa tana sheshsheƙar kuka.
Zama yai kusa da ita yana kallon yadda fiskarta ya koma saboda kuka. Yayi kusan minti biyu yana zaune a wajen amma ba ta san da zaman sa ba.
Yanayin Sallamar sa da ba za ta iya mantawa ba ta ji a kunnen ta. Ta É—an yi shiru kaÉ—an da kukan ko dai kunnen ta ne ya ji ba dai-dai ba. A karo na biyu ya sake sallama wanda ya sa Zaytoonah ta juya gefen ta da sauri. Ta zaro ido ganin Justice zaune a wajen yana murmushi.
Maimakon ta amsa sallamar sai ta ce " Sir an kori ƙaran da mu ka yi. I failed Mommy, I failed You. Gaskiyar Barr. Batula ne da ta ce ni daƙiƙiya ce"
"Ssshhhhh" ya sa yatsa a daidai bakin sa alamar ta yi shiru.
"Waya gaya miki kuka ake yi idan an kori ƙara?"
"Sir..."
"Ki dena kuka, kin yi ƙoƙari sosai and i'm proud of you, kuma na san Mommy na ta alfahari da ke. Ka da ki damu da cewa wai an kori ƙara. This is just the begining.
"Ni Yunus Muhammad Abbas zan tsaya miki har sai mun kai kankat ɗin shari'a a Nigeria. Zamu cigaba da ɗaukaka ƙara har sai mun ci nasara. Idan kuma ba mu da nasara a nan, za mu bar wa Alƙalin Alƙalai wanda ba ya zalunci, Alƙalin da babu wanda ya isa ya yai ƙarya ko ya ba da shaidar ƙarya a gaban sa. Shin kin san wannan Alkali?"
Zaytoonah ta girgiza kai.
"Ba ki sani ba?" Yai maganar da É—an mamaki a fiskar sa.
Zaytoonah ta girgiza kai.
Yatsar sa É—aya ya É—aga yana nuna sama da shi.
"Alƙalin Alƙalai shi ne mai kallon duk abinda ke wakana a doron ƙasa"
Zaytoonah ta yi murmushi ta ce "Sir ai sai ka min gwari-gwari zan fi fahimta"
"To yanzu barin mi ki gwari-gwari. Kar ki sake yin kuka kin ji, domin ko da a nan duniya gaskiya ba ta fito ba, za mu haÉ—u gaban Allah a ranan da babu wani mai Mulki ko Isa bayan shi"
Bai san dalilin da ya sa yai haka ba amma abu ne da zuciyar sa ta riya ma sa gangan jikin sa kuma ta aiwatar. Hannun ta ɗaya ya kamo ya sarƙe da na sa. Tunda ya kama hannun Zaytoonah ta ji wani sanyi na ratsata. Sau ɗaya ta haɗa ido da shi sannan ta sunkuyar da kai tana jin ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
"Ki min alƙawari ba za ki yi kuka ba Zaytoon"
Ta kalle shi da sauri jin sunan tamkar a bakin Zuhayr.
"Zan taimaka mi ki ta kowanni fanni har mu kai ga nasara Insha Allah.
"Ina so ki bani haÉ—in kai har komai ya tafi dai-dai. Zaytoon a duk lokacin da ki ke tunanin kin gaza a wani abu to ina so ki tuna cewa Yunus yana kusa da ke kuma zai zame miki madogara. I'll stand by you Zaytoon ko da ba mu samu nasara ba"
Ba ta san ya za ta fassara yanayin da ta tsinci kan ta ajiki ba. Is like kamar Zuhayr ke tareda ita a wannan lokaci, idan da hali kwantawa za ta yi jikin sa ta samu nitsuwa. Sai dai kafin ta kai ga biyewa zuciyar ta wajen aiwatar da abinda zuciyar ta ke tunani Justice ya sake hannun ta yana faÉ—in " ki tashi ki shiga ciki akwai sanyi a nan".
Mommy da ke kallon abinda ke faruwa daga sama ta sauke ajiyar zuciya ganin wannan dramar mai kama da almara, duk da ba ta ji mi su ke faÉ—a ba amma abinda idon ta ya gani ta fahimta sosai.
Tun jiya Justice ya sanar da Mommy zai zo bayan ta sanar da shi hukuncin da aka zartar a kotu. Jirgin su tsakar dare ya sauka shiyasa ma ya kwana a hotel sai yau da safe Mommy ta aika dreba ya je ya ɗauko shi. Hiran minti goma su ka yi da Mommyn ne ya tambayi Zaytoonah shi ne ta sa wani mai aiki ya kai shi wajen ta dan ɗazu da ta leƙo ta balcony ta hangota zaune a wajen fountain na gidan..
2/11/21, 10:04 PM - ****: 46
Bismillahir Rahmanir Rahim
*engaged*
"Ranka shi daɗe babu wanda ya ke goyon bayana cikin su, Ƙyamatata su ke saboda na zama Musulma. I think Uncle Udodiri ya riga ya poisining mind ɗin su, nobody is ready to testify"
Justice ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya ya ce "wannan mata da ki ka ce ta taimake ki kin gudu lokacin, tana raye?"
"An ce ta mutu shekaru biyu da su ka wuce"
Justice yai shiru na ɗan daƙiƙai kafin ya ce " za a iya samun wanda za su yi magana idan an tunzura su"
Cike da mamaki Mommy ta ce "Ranka shi daÉ—e kana nufin a bribing na su?"
"A cikin kowani Family ana samun rashin jituwa tsakanin 'yan uwa. Maƙiyan Chief Udodiri su za su ba mu haske har mu samu shaidar da mu ke so. If we ask the right question the right way, we'll get the answers we needed"...
Tun maganar su da Justice ta fara sake jikin ta. Lokacin da ta shiga gida wanka ta yi ta ci abinci sannan ta yi Sallah, daga wajen da ta yi sallar ne ma bacci ya sace ta.
Kusan ƙarfe biyar na yamma ta wuce su ka isa ƙauyen na Okwuohia. Asalin mafarin komai kenan.
Tun da su ka zo Owerri sau biyu su ka je ƙauyen. Rashin samun fiska daga 'yan uwanta ya sa ba su sake komawa ba.
Family house ɗin su na nan yadda ya ke duk kuɗin Udodiri bai gyara gidan ba, babban fili ya samu a ƙauyen na su ya gina ƙaton gida duk lokacin da ya shigo ƙauyen a nan ya ke sauka.
Gidan Mazi Nkem su ka je wanda shi ne Babba kaf gidan, ƙanin mahaifin su Udodiri ne.
Goro da palm wine aka kawo mu su a matsayin abun tarban baƙi, tunda sun samu Mazin shima na shan giyan ne.
Maryam ne ta fara bayani cikin harshen su na Igbo wanda bai zauna ba saboda sabo da yaren Hausa da kuma Turanci da ta yi.
A karo na biyu ta nemi ya sanar da ita abinda ya sani gameda mutuwar iyayen ta.
Wancan karan da su ka zo cewa yai bai san komai ba, shi baya ƙauyen sanda abin ya faru, lokacin da ya dawo ne ya tarar da mutuwar da kuma guduwar Maryam ɗin.
Duk tambayoyin da Mommy ke ma sa sai ya ce bai sani ba. Mommy ta kalli Justice da ke lura da yadda tsohon ke kwankwaÉ—ar giya a kofin silver.
"Ranka shi daɗe ya ƙi magana"
Justice ya miƙe tsaye yana faɗin "Hajiya taso mu tafi"
Ba mu su Mommy da Zaytoonah su ka miƙe su ka bi bayan sa da mamaki.
Sai da su ka yi nisa sannan ya tsaya ya ce "ba za mu samu komai a wajen sa ba a haka. Ina so mu je gidan Pastor na ƙauyen nan"
Ba mu su Mommy ta sa Eze wanda ya ke mu su rakiya akan ya kai su gidan Pastor. Ko da su ka isa Justice ya gabatar da kan sa wajen Pastor Emmanuel tareda ma sa bayanin abinda ya ke so. Pastor Emmanuel ya jinjina da lamarin tareda alƙawarin zai yi duk yadda Justice ɗin ya ce. Su ka ma sa godiya su ka tafi Mommy da Zaytoonah suna jinjina hikimar Justice...
Sun isa Owerri chan dare inda su ka kama hotel su ka kwana. Washegari bisa Umurnin Justice su ka ziyarci tsofaffin mai'aikatan Kamfanin Mahaifin Maryam wanda Udodiri ya ƙwace, wanɗanda su ke aiki tun lokacin da aka buɗe kamfanin. Da ke duk haɗin baki su ka yi duk tambayoyin da su ke mu su amsa ɗaya su ke samu, sai a wajen Mr Edet kawai su ka samu amsan da su ke so. Mr Edet yayi aiki a kamfanin na shekara ɗaya tun farkon buɗe kamfanin kafin daga baya ya ajiye aikin. Ya ba su vital information wanda za su taimaka.
A hanyar su ta dawowa ne wata number ta kira wayan Mommy. Da ke Mommy ta bada numbarta a wajaje dayawa shiyasa tana ganin baƙuwar numba sai ta ɗauka.
Matar da ke magana da yare ta ke magana inda ta nuna ta san wani abu gameda abinda ya faru shekaru talatin da su ka wuce...
Bayan sun yi wayar ne Mommy ta ce "Ranka shi daÉ—e trap É—in ka yayi aiki, Aunty Uloma is ready to confess"
"Mommy is she reliable?" Zaytoonah ta yi tambayar tana kallon Mommy.
"Ƙanwar Baba na ne itama, Uwar su ɗaya da Udodiri"
"Then ya kamata mu haÉ—u da ita a yau É—in"
Justice da ke gaba yana jin su bai ce komai ba.
Lokacin da su ka isa ƙauyen a gidan Aunty Uloma su ka tsaya. Mommy da Zaytoonah su ka shiga yayinda Justice ke jiran su a mota shi da Driver.
Tabbas wa'azin da Justice ya ce Pastor yai a church ya shiga zuciyar Aunty Uloma sosai. Kuka ta ke yi sosai lokacin da ta ke yiwa Mommy bayanin komai.
Mommy ma sai da ta yi hawaye jin yadda Udodiri ya kitsa komai. A lokacin da Udodiri ya faÉ—a mu su plan É—in sa na kashe Patrick ba ta supporting É—in sa ba amma da yai ta hura ma ta kunne sai ta amince ita ta kai abincin bayan Udodiri ya gama barbaÉ—a poision É—in a ciki.