Sashe 106
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raziya ta yi shiru.
Hajiya Ghazala ta cigaba da kitsa ma ta abinda za ta faÉ—a tana nuna ma ta indai ta yi hakan to Daddyn su zai saki Zaytoonah ta bar mu su gidan gaba É—aya.
Wannan karan bayan ya ji abinda ya faru daga ɓangaren Hajia Abu, Ghazala da ma Raziyan bai yanke mataki ba duk da dai ransa ya sosu da abinda ya faru. Kiran Zaytoonah yai ya tambayeta miya faru a gidan sanda baya nan. Da ke ranta a kufule ya ke sai ta ce ma sa "na san ka kira ne dan ka ji dalilin da ya sa na yiwa Raziya haka. To dalili ɗaya ne, ba zan cigaba da ɗaukan rashin kunyarta ba. na san ban haifeta ba amma atleast na girmeta kuma ko gaba ta sake shiga hurumina zan hukuntata"
Yai shiru bai ce komai ba sai chan ta ji ya ce " Allah ya kyauta"
Yana katse kiran ta ja tsaki ta fara kwarwa " haka kawai yarinya za ta mai da ni shashasha. Ta kirani buskuɗa, inyamura, Mama ɗuwawu duk ban tanka ba still dan tsabar rashin kunya sai ta shigo min ɗaki ta min ɓarna saboda ni baiwar gidan su ne".
Ɗazu su ka gama baran-baran da Hajia Ghazala, ta gama karantar ta, matar babbar munafuka ce ta ƙarshe kuma da alama akwai wata agenda da ta ke da shi a ƙasa. Ko waye ya kirata ma ta zo oho...
***
"Daddyn Raziya ina son zuwa gidan Muhsina gobe"
Sai da ya kurɓi tea kaɗan kafin ya ce "Allah ya kaimu"
Su biyu ne zaune a dinning É—in suna karyawa. Wannan weekend É—in yaran sun tafi Zaria tareda Hajiya Ghazala. Itama ta so yaranta su zo wannan weekend É—in amma Mommy ta tafi da su Ringim.
Har su ka gama cin abinci ba wanda ya ƙara cewa komai. Tun ranan da ya dawo ta ke jira ya ma ta magana akan aikin da ta saka Raziya amma bai yi ba itama sai ta biye shi aka cigaba da zaman shiru.
Ko da ya tada maganar ma tanada befitting amsa da za ta bashi. Dan ta ga take-taken sa yana nuna bayason abinda zai taɓa ma sa Yara...
"Faɗamin gaskiya 'yar uwa, kina bashi haƙƙin sa yadda ya kamata?"
"Ni kam..."
"Seriously Zaytoonah, ke fa ba yarinya ba ce, in har babu wannan intimacy tsakanin ki da mijin ki akwai matsala. To ni in tambayeki zaman mi ki ke yi a gidan sa?"
"Zaman aure mana" Zaytoonah ta amsa da sauri.
"Haka ake auren a garin ku? For good 3months kina zaune a gidan sa zaman kashe wando"
"Malama wata biyu da sati uku ne"
"I'm dissappointed in you Allah. So ki ke ya nemi matan banza a waje? Ko so ki ke ya ƙaro wata matar a kan ki?. In ba dan Galadima ma ba yaro ba ne ta ina zai biyewa shirmen ki har ya bari kuna zaune gida ɗaya iya wannan lokacin yana jira ki kawo kan ki"
"Muhsina ba za ki gane ba, its just complicated ne"
"Really!. Mutum mai daraja kamar sa kin mai da shi wawa ki ce its complicated. Haba Zaytoonah, haba"
Hawaye ne ya gangarowa Zaytoonah ta yi saurin gogewa tana faÉ—in " ba zan iya mantawa da Zuhayr ba. Nobody can take his place..."
"Subhanallahi! Zaytoonah wani irin gurɓaceccen tunani ne wannan"
Ina buƙatan lokaci a halin yanzu i just cant..."
"Cant or wont" Muhsina ta katse ta rai a ɓace...
***
Ta sauke ajiyar zuciya ya fi sau bakwai, duk dan tana neman sauƙi a zuciyarta da ya cunkushe. Ga shi dai ta shirya a zahiri amma a baɗini ba ta shirya ba.
*" ba shi da muni, ba jahili ba ne, ba shi da nakasu a tattare da shi. So what's stopping you from embracing your husband?. Ta ya za ki hana shi, ki hana kan ki samun nitsuwa da Allah ya halarta mu ku. Ban ce ki bashi kan ki a matsayin dole ba, amma na rantse mi ki da Allah indai ki ka ba shi dama nan da lokaci kaÉ—an duk wani É—ari-É—ari da ki ke ji zai tafi and you'll accept him wholeheartedly"*
Maganganun Muhsina ya ba ta ƙwarin gwiwar miƙewa, ta taka zuwa gaban madubi ta kalli kan ta. Ba wani kwalliya ta yi ba amma ta yi kyau.
Rigan baccinta iya rabin cinya ne fara ƙal sai robe ɗin rigan wanda ya kai ma ta har ƙasa shi kuma baƙi, dai da ta nannaɗe gashinta into bun kafin ta saka baƙin bonnet a kan ta.
Ta fesa turare a jikin kayan sannan ta shafa turaren jiki a wuyan ta sauran ta murje shafukan hannunta da shi.
Har ta zo za ta fita ta ji wayar ta na ringing a kan gado. Ta je ta É—auka sai ta ka kiran Justice ne.
Da ta amsa wayan ya ce ta same shi a falon sa yana da magana da ita.
"Relax Zaytoonah" ta faɗa tana shaƙar iska sannan ta fizgar da shi.
"Ko da ya miki faÉ—a akan Raziya ne kar ki yi fushi kin ji. Ke ma idan ba ki manta ba Daddy har faÉ—a ya ke yiwa Mommy idan ta punishing É—in ki. Relax he's a father matsayin ki matar sa matsayin Raziya 'yar sa akwai banbanci kin ji"
Da wannan mantra É—in ta wuce falon Justice.
Baya rabuwa da karatu, yanzu ma wani ƙaton littafi ta gani a gaban sa yana karantawa da alama littafin abinda ya shafi Law ne.
Ƙaramin hijab ta saka akan kayan dan ta zo fitowa a haka ta fasa ta saka hijab ɗin.
Kusan minti biyar kafin ya rufe littafin ya ajiye gefe.
Ya yi salati tareda buÉ—e zaman da addu'a. Cikin zuciyar Zaytoonah tana tunanin ko dai yana duba ne, idan ba haka ba ya aka yi ya san ta zo ne domin su shirya.
Sai da ya gama addu'an kafin ya fara jawabin sa wanda ƙaramar nasiha ce akan ƙaddara da kuma falalar yadda da ƙaddara, wanda ke ɗaya daga cikin cika-ciken musulunci.
Sai da ya gama nasihar sa sannan ya faÉ—a ma ta dalilin kiran ta da yai.
"Princess zan ƙara aure"
Da sauri ta É—ago ido tana kallon sa ko dai kunnen ta ne bai ji dai-dai ba.
"Ba dan na nuna miki kin gaza ba, sai dan ina ga hakan zai kawo maslaha a tsakanin mu. Kula da su Raziya ba zai zama yana hannun ki ke kaÉ—ai ba, idan kin fara aiki kula da gida zai mi ki wahala ke kaÉ—ai..."
Sauran maganganun sa ya bi iska ne dan ba jin su ta yi ba.
Wani ciwon kai ne ya sauka ma ta lokaci guda. Ta ma rasa yadda za ta kwatanta abinda ta ke ji yanzu. Certainly ba haushin Justice ta ke ji ba tunda koma wani irin hukunci ya ɗauka harda laifin ta ciki. Amma why zuciyar ta ya cunkushe ta ke jin wani ƙunci a ciki?
"Ki yi haƙuri ban gaya mi ki ba sai yanzu, komai ya zo ne a ƙurarren lokaci"
Murmushi mai ciwo ta yi a ƙoƙarinta na danne abinda ta ke ji mai kama da kishi.
"Ranan Jumu'ah za a É—aura aure, tarewar ta zai iya kaiwa sati É—aya ko sati biyu bayan auren"
"Allah ya kaimu lokacin" Da ƙyar ta iya haɗa kalmomin da ta faɗa...
Tana shiga É—aki sai ga hawaye É—aya bayan É—aya na zubowa.
Ta ƙarisa kan gado ta kwanta. Wasa-wasa tun tana dannewa har ta kai ta kasa sai kawai ta fashe da kuka.
Ba abinda ya zo ma ta rai sai dana sanin auren Justice da ta yi tun farko. Mi ya sa ma ta bi shawaran Mommy? Mi ya sa ma ta biyewa nasihar Mommy?
Mi ya sa ba ta tuɓurewa Mommy ta auri Auwal ba. Auwal ba zai taɓa ma ta haka ba.
Its barely 3 months da auren su amma wai zai ƙara aure. Kenan dama tun farko ba ita kaɗai yai niyyar aura ba kenan.
Ire-iren waɗannan tunanin ta dinga yi har bacci ya sace ta bayan ta sha kuka ta ƙoshi...
Washegari haka ta tashi kamar ba abinda ya faru. Indai aure zai yi to yai abunsa tunda matar ba a kan ta za ta zauna ba. Idan ta ga zaman ba zai yiwuba kuwa dole ne ya sallameta. Abinda ta sawa ran ta kenan.
Ta dai ma sa breakfast amma ba ta zauna sun ci tare ba. Da dare kuwa da su ka zauna tare tambayarta yai ko akwai abinda ta ke buƙata amma ta ce ma sa ba komai. Haka ya dinga satan kallon ta. Yana so ya ga wata alama da za ta nuna ma sa Zaytoonah na kishin sa amma duk ta inda ya duba sai ya ga kamar yaudaran kan sa kawai zai yi dan bai ga alamun Zaytoonah na kishin sa ba...
Wayar Mommy ne ya tasheta daga bacci. Da ta san maganar auren Justice za ta ma ta da ma baccinta kawai ta yi.
Hajiya Ni'ima ce ta faÉ—a ma ta maganar auren da su ka haÉ—u a office. A faÉ—anta wai itama sai a lokacin ta ke jin maganar auren da ta je Fada, shi ne ta kira Galadima ta tabbatar da maganar a wajen sa.
"Adaeze kar ki bari wannan ya ɗaga miki hankali kin ji. Ibada ki ke yi kuma itama shi za ta zo yi, duk abinda za ki yi ki yi shi tsakani da Allah domin shi zai ba ki ladan haƙurin da ki ka yi kin ji"
"Adaeze i know it hurts, i felt the same way too lokacin da Daddyn ku ya auri Hajjo. It always hurts Princess.
"Rayuwar aure kowa da kalar ta shi jarrabawar. Idan ki ka ji na wani sai ki kama baki ki godewa Allah saboda nakin ya fi na su kwanciyar hankali da farin ciki.
"Ki lazimci addu'a sannan ka da ki yadda ki saka damuwar wata a ran ki, lafiyar ki da kwanciyar hankalin ki shine gaba da komai. Sai ki ga komai ya zo mi ki da sauƙi, kin ji"
"Na ji" ta faÉ—a kamar za ta yi kuka...
***
Tana zaune a ɗaki ita kaɗai sai ta ji sallamar Bahijje a bakin ƙofa.