← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 161

Sashe 45

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun samu yayi bacci amma hayaniyar su Zaytoonah ya tada shi. Yana ƙyalla ido ya ga Maryam ya ji wani farin ciki ya mamayeshi. Yaran duk su ka yanyameshi da shagwaɓa Zaytoonah har da kukan sakalci. Maryam dai zama ta yi a kujera tana bin su da kallo cike da tausayin mijin na ta har lokacin akwai nasal canula a hancin sa wanda ke daidaita numfashin sa maganar sa ma a hankali a hankali ya ke fita. Shima ɗin lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta, idan su ka haɗa ido sai yai saurin kau da kai.

Bayan maghrib Auwal ya tattari yaran zai mai da su gida su ka ƙi Zaytoonah har da kuka wai a wajen Daddyn ta za ta kwana. Maryam ta zare ma ta ido dole ta bi bayan Salman su ka tafi. Auwal ne zai kai su da Motar Maryam dan shima ba laifi ya iya, a ƙiriniya ya koyi mota a wajen wani abokinsa da ke sato motan Babansa yana fitowa da shi idan baya nan.

Ɗakin yai tsit bayan fitan yaran. Kusan minti biyu ya wuce kafin TJ ya ɗago ido ya kalli Maryam wacce itama shi ta ke kallo ya ce " ki yafe min, ban san da maganar Mukhtari ba, ban san komai ba. Ki yi haƙuri na kasa ba ki farincikin da na miki alkawari a farkon auren mu, ki yafe min"

Tasowa ta yi a hankali ta rungumeshi. Tana tsaye yana zaune ya kwantar da kan sa a cikinta ya ƙanƙameta.

"Na yafe ma ka"

"Da gaske Maryam?"

Ta gyaÉ—a ma sa kai.

Cikin i'ii'ina ya ce " kin janye maganar rabuwa da ni?"

"Ina da wajen da zan je ne idan na rabu da kai?"

"Na gode Maryam" ya faÉ—a sai ga hawaye na zubo ma sa. Maimakon ta yi magana sai ta manna ma sa light kiss a bakin sa.
"Ka ga ka kwantar da hankalin ka. Likita ya ce ban da kuka, ban da sa damuwa a rai"

"Ke ce likita na Maryam and you know it. Tunda kika shigo ɗakin nan duk ciwon da na ke ji ya yi sauƙi"

"Allah ya baka lafiya"

"Janbakin ya mi ki kyau idan da hali a bani na shanye"

"Naughty Man" ta faÉ—a tana murmushi kafin ta rankwafo ta haÉ—e bakin su...

Ita ta kwana da shi su ka wuni suna nunawa juna kulawa. Duk yadda ya so su tattauna abin da ya faru tsakaninta da Muntari ta ƙi ta ce sai an sallameshi tukunna. Ta yi hakanne dan ba ta so ya ji abinda zai ƙara ɗaga ciwon sa.

Washegari da safe da likita ya zo ya dubashi aka cire ma sa nasal canula ya kuma yiwa Maryam bayanin yadda za a dinga kiyayewa da duk abinda zai ɗaga ma sa hankali. Sun ce idan sun ƙara ganin yanayin yadda ya samu sauƙin ciwon ƙirji za su sallameshi dan har yanzu any shock ko wani extreme excitement zai iya sa shi a risk ɗin wani heart attack ɗin. Shi kuwa T J tunda ya farka dama ya lazimci addu'o'in saboda ya samu sauƙin raɗaɗi da zafin da ya ke ji a zuciyar sa.

Ba ta so tafiya office ba dan yadda T J ke narke ma ta hadda cewa ta ma sa rawan Atilogwu ta yi dariya ta ce za ta ma sa idan ya koma gida. Su Zaytoonah ma kafin su je makaranta sai da su ka zo su ka gaida mahaifin su.

Ƙarfe tara na safe Hajjo ta zo ta karɓeta hakan ya sa Maryam ta koma gida ta shirya ta wuce office. Ƙarfe shabiyu kuwa ta koma gida ta yi wanka ta shiga haɗa abincin da za ta kaiwa T J a asibiti.

Tana cikin juya abincin a food warmer wayarta yai ringing. Numbar T J ne dan haka da sauri ta ɗauka. Ɗazu tana office ya kirata sun fi minti shabiyar su na hira inda ya ke ƙara jaddada ma ta soyayyar shi gareta.

"Hello Mommy ba a ga Daddy ba. Daddy ya ɓata" Auwal ya faɗa cikin kuka.

"Ban gane ba a ga Daddy ba, ina ya je?"

Kukan Hajjo da ta ke ji ne ya sa jikinta ya hau ɓari ta yi saurin kashe wayar ta je ta rarumi gyalenta ta fita da sauri. Tare za su tafi asibitin da Goggo amma ko ta kan ta ba ta bi ba...

Zuwanta Asibitin ta tarar da mummunan labari. Lokacin da T J ya gama waya da Maryam ya kwanta bacci yana bacci Hajjo da ta je ɗauko ma sa kaya ta shigo. Ganin yana bacci ya sa itama ta kwanta a kan tabarma a ƙasa a haka Auwal ya shigo ya sameta, ganin T J ba ya kan gado ya sa ya tashi Hajjo yana tambayarta ina T J tunda ya leƙa banɗaki baya nan.
Wasa- wasa sai ga shi sun duba ko ina a asibitin babu T J ba dalilin sa. Maryam zama ta yi daɓas a ƙasa tana hawaye lokacin da wata mai shara ta ce ta ga lokacin da T J ya fita a ɗakin sa har tana ma sa ya jiki amma ko juyowa bai yi ba balle ya kulata. Mutane biyu ma su ka kuma jaddada cewa sun ga fitan T J daga asibitin.
Da farko Maryam ta É—auka Muntari zai je nema saboda abinda ya faru amma ai ya san Muntari baya gari.

Ranan dai tashin hankalin da Maryam ta shiga ba a magana. Kuka ma kasa yi ta yi, bacci kam kasa yi ta yi dan duk inda ake tunanin T J zai je an nema ba a same shi ba ba akuma samu wanda ya gan shi ba bayan fitan sa daga asibitin.
Washegari da safe aka je police station aka ba da report na ɓatan T J.
Wasa-wasa kwana biyu su ka shige ba a ga T J ba ba a san inda ya je ba. A rana na uku Muntari ya dawo gida ya tarar da ɓatan T J yadda ya ke salati yana salallami ka ɗauka bai san mi ke faruwa ba, ka ɗauka ya fi kowa damuwa da ɓatan T J. Har Kaduna ya raka Maryam aka kai cigiya gidan talabijin da gidan radio. Tun ana cewa kwanan sa biyu da ba a gan shi ba har aka fara irga sati ɗaya sati biyu sati uku kenan yanzu. Zuwa lokacin Maryam tamkar mahaukaciya ta koma, ita ne nan itane chan ko bacci ba ta iya yi. Koyaushe ɗaurawa kan ta laifi ta ke yi a ɓatan T J musamman da Likitan T J ya ce ƙila damuwa ce ta sa shi samun taɓin hankali...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*18-Baby Boy*

Bismillahir Rahmanir Rahim

A cikin wannan yanayi na tashin hankali ne ciwon Sadiq ya tash, Hajjo abu ya zama ma ta goma da ishirin.
Lokacin da Auwal ya zo ya gayawa Maryam haka ta ɗebi jiki ta je Asibitin. Itama na fama da Zaytoonah da tun da ta ji labarin Baban su ta ke cikin halin yau lafiya gobe babu. Ta yi sati ba ta zuwa makaranta, a sati na biyu da Maryam ta takurata ta je kuwa kullum da kuka ta ke zuwa da shi ta ke dawowa. Sai ga shi wai ƙanin ta Salman ne ke zama ya bata haƙuri idan tana kuka dan Maryam ta fita harkanta, itama fama ta ke da kanta, tun ɓatan T J za ta iya cewa ba ta samu nitsuwa ba, ba ta da lafiya amma babu halin nunawa dan abinda ke damunta ya fi ƙarfinta.

Wannan karan Auwal ne ya bayar da jini aka sawa Sadiq. Maryam na zaune kusa da Hajjo da ke ta matsar ƙwalla sai ga kiran Muntari. Hajjo ya ci ace ta saba da ciwon Sadiq amma tsoron rasashi ta ke yi kamar yadda ta rasa Sadiq ɗin ta na farko. Shi bai ma yi wahalar da wannan ke yi ba, wannan sai ya ja lokaci kafin ciwon ya tashi amma idan ya tashi kam hankalin kowa sai ya tashi ga uwa uba kuɗi da ake kashewa wajen jinyar sa.

Maryam na É—aga wayan ya tambayeta tana ina dan dawowar sa kenan daga Abuja inda ya kai cigiya abinda ya faÉ—a mu su kenan amma maganar gaskiya shine Lagos ya je ya dubo wasu kayansa da aka ce sun iso.

Ta sanar da shi su na Asibiti Sadiq ba lafiya. Ya ce gashi nan zuwa.
Minti Talatin da biyar sai gashi ya iso ya kuma kiranta yana tambayar ina ne É—akin ta ce bari ta fito ta shigo da shi dan bayan ita da Hajjo ba kowa a É—akin ba ta kuma da nitsuwar yi ma sa kwatance.

Lokacin da ta fito tundaga nesa ya ƙare ma ta kallo, ta rame ta yi baƙi kana ganinta ka san ba ta da kwanciyar hankali. A ƙasan ran sa ya ce "zuwa lokaci kaɗan za ki haƙura ki manta da shi"

Jerawa su ka yi su na tahowa amma ba su yi nisa da shiga Asibitin ba Maryam ta yanki jiki ta faÉ—i. Tunda ta fito dama ta ke É—an jin jiri amma ta daure ta cigaba da tafiya.
Muntari ya fara Salati yana ƙoƙarin tallafota gamida ƙwalawa likita kira. Shi da wata nurse su ka ɗauketa su ka ɗaura ta akan gadon da ke gefen wajen aka turata zuwa ɗaki.
Chapter 45 · 0% Book details