Sashe 62
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiya su ke a hankali suna tafiya lokaci zuwa lokaci Zaytoonah na ma sa tambayoyi gameda gidan da su ke wanda ya ke nesa da mutane dan idan za ta tafi school Mr Smith ya É—auketa a mota sai sun yi tafiyar kusan minti goma kafin su fara ganin gidaje suma kuma tsilla-tsilla haka, its like anguwar dai na wanda ba sa son takuri ne.
Sai da su ka yi tafiya mai nisa kafin Zuhayr ya nuna ma ta iya inda filin gidan sa ya ƙare wanda ya sa ta mamakin girman filin gidan sa.
Sun yi tafiya mai nisa sosai dan sun fi awa É—aya suna tafiya amma da ke ana tafiya ana taÉ—i ne sai Zaytoonah ba ta ga nisan da su ka yi ba, tafiya da ta yi nisa kam yunwa da ishirwa ne ya sa ta fara gajiya.
"Amma idan za mu koma ba da ƙafa za mu tafi ba ko? Na ga tafiyar ta ƙi ƙarewa"
"Ke dai ki ce kin gaji da tafiya, dan haka na ci galaba yau"
"Ba wai na gaji ba ne fa tambaya ce kawai"
"Zaytoon ki yarda kawai, i won"
Da suna dawowa kuwa sai ta ga tafiyar ta ma ta nisa saboda yunwa da ta ke ji amma a haka dai suka dawo da ƙafan dan ya ce ba zai kira Driver ba.
Suna zuwa kuwa dining ta nufa Zuhayr ya bita da sauri.
"No no no no" ya riƙe hannun ta da ke shirin buɗe wani bowl
"Ba ci zan yi ba dubawa kawai zan yi"
"Ki je ki yi wanka Baby"
Haka ta kumbura fiska tana tura baki ta haura sama.
Da ta yi wanka ta sauko ma shi ya tsara abincin da za ta ci.
"ÆŠan wannan abun zan ci?"
"Is not about the quantity but quality Baby girl"
"Allah cin zali ne wannan, cin zali of the highest order"
"Mi na gaya miki jiya?"
Ta juya ido ta ce " abu biyar da za su sa na ji daÉ—in jikina amma in ji Zuhayr"
"Ba in ji ni ba Zaytoon, its the truth, abincin da ki ke ci dole ya zama mai lafiya"
"Whatever"
Ranan dai gaba ɗaya abincin da ta ci ƙarƙashin kulawar sa ce.
Ben kam wuni yai a ɗaki yana nazarin yadda zai yi da wannan sabon salon shaƙuwa tsakanin Zuhayr da Zaytoonah. Idan aka tafi a haka Zaytoonah za ta samu dama akan Zuhayr. A da ya renata saboda ƙarancin shekarunta da kuma gani da yai kaman ba ta da abinda za ta iya jan ra'ayin Zuhayr da shi amma kuma yanzu dole ne ya raba tsakanin wannan shaƙuwa.
Cikin kwana goman nan ba ta da sukuni, Zuhayr ya ma ta kane-kane. Abincin da ta ke ci duk under strick supervision ɗin sa ne ga shi ta ɗauka excercise ɗin su kaman na ranan farko ne ashe ba haka ba ne, ranan farko sharan fage ne. Washegari gudu su ka yi a cikin gida da zagaye gidan su ka yi sau goma, sun yi biyar su ka zauna su ka huta kafin su ka sake yin biyar. Rana na uku ma gudu su ka yi, a rana ta huɗu kuma suna fitowa waje ya miƙa ma ta jump rope ya ba ta.
Ta bishi da harara bayan ta karɓa igiyar.
Da sauri ya ke tsallen amma ita a hankali ta ke yi tana yi ma tana harɗewa, minti goma su ka yi ya ce a huta akayi hutun minti biyar sannan aka sake yin wani minti goman ana tsallen aka sake yin hutun minti biyar kafin su ka yi na wani minti goman wanda da ƙyar Zaytoonah ta kai.
Kwantawa ta yi laƙwas akan grass carpet tana maida numfashi Zuhayr ya kwanta gefenta yana maida numfashi shima.
"Ya ki ka ji?"
"Ni dai daga wannan kwana goman ba zan ƙara yin komai ba"
Yai dariya.
Sauran kwanakin kuma a gym room aka ƙarisa wanda da tsiya-tsiya aka ƙareta.
Day 11 ta tashi da ɗoki yau kan babu wani excercise babu cin abubuwan da Zuhayr ke tursasa ma ta ci. A ƙasa ta sameshi har ya shirya cikin suit shi da Ben da alama fita zai yi.
"Yau kam angama" ta faÉ—a tana murmushi
"Saura abu É—aya"
"Babu, ai kwana goma ka ce"
Ya zaro wani takarda a Aljihun sa ya miƙa ma ta sannan ya ce " zai yi tafiya sai bayan kwana huɗu zai dawo"
Bayan ya tafi ne ta buÉ—e takardan.
*ki je gaban madubi ki duba kan ki, ki ɗau lokaci kina kallon kan ki. Sannan bayan kin gama ki yi shawara da kan ki, ki zaɓa self love or weight loss*
Ta jima tana sake karanta takardar amma ba ta gama gane manufar takardar ba...
Da ke da Ben su ka tafi ita É—aya ce a gidan kamar yadda ya faÉ—a É—in ta jima tana kallon kan ta a jikin madubi amma ba ta ga komai da ya chanja ba hakan ya sa ta watsar da maganar zuwa yamma kuma ta je gym room ta gwada nauyin ta. To her shock daga 95kg sai ta ga ta sauka zuwa 91kg.
Ta yi murmushi dan ta fahimci mi Zuhayr ke nufi. Maimakon ta dena excercise kamar yadda ta yi niyya da farko sai ta cigaba kamar yadda su ke yi da Zuhayr. Abinci ma irin yadda ya tsara ma ta takeci sai dai ta ɗan ƙara yawan sa. Eat more protein Zaytoon saboda calorie ɗin sa na saurin ƙonewa ba kaman na carbohydrate ba.
Ba ta taɓa yiwa Zuhayr waya ba amma a rana ta biyu sai ta kira numbar sa, ba a ɗauka ba dan haka ta tura ma sa da text kamar haka *i choose self love*
Bayan minti talatin sai ya kirata ya ba ta haƙuri na rashin ɗaukar wayarta da bai yi ba saboda meeting da su ke yi.
Sun ɗan taɓa hira kafin ta kashe wayar...
***
Dawowar Zuhayr daga tafiya da kwana biyar aka fara Azumi.
Kwanakin farko duk sai da ta makara saboda bacci sai wucal ta ke yi. Hakan ya sa ta sa Zuhayr ya dinga tashin ta, ita ko a gida Mommy ce ke tashinta dan idan ta sa Alarm ma idan ya buga a banza, ko ta tashi kashewa ta ke yi ta cigaba da bacci.
Zuhayr baya suhur amma haka zai zo ya tasheta wani lokaci sai ya zo har sau biyu kafin ta tashi ta fita ta nemi abincin da za ta yi suhur da shi.
Ranan tana bacci sai ga kiran Chef Green wai ta zo tanada baƙi a ƙasa.
Ta yi mamaki dan ita ba ta san kowa ba balle har a zo neman ta, ta dai fita dan tana tunanin ko baƙin Zuhayr ne.
Mata da miji ta gani da 'ya'yan su biyu mace da namiji, da ka gan su ka san ba za su wuce 'yan India ko Pakistan ko Malaysia ba.
Bayan sun gaisa matar ta yi ma ta bayanin ko su ɗin su waye ne. Namijin ya gabatar da kan sa da suna Faisal Khan ita kuma matar Zahra Ayyub wanda hasashenta ya zo kusan dai-dai dan Faisal khan ɗan Asalin ƙasar India ne matar sa kuma 'yar Malaysia.
Yaran su kuma Macen wacce ita ce Babba, sunan ta Alinah sai namijin Fareed.
Cewa su ka yi ba su san Zuhayr yayi aure ba sai a wajen Chef Green, sun kawo wa Zuhayr ziyara ne ya ce baya nan amma matar sa na nan shine su ka nemi ganin Zaytoonah. Sun yi murna tareda yiwa Zaytoonah addu'ar fatan samun zaman lafiya. Da za su tafi su ka roƙi Zaytoonah akan ta taimaka ta jawo Zuhayr ya koma yin Ibadah kamar yadda ya ke yi kafin mutuwan Alinah. Tunda Alinah ta mutu bai sake zuwa masallaci ba haka nan ya dena shiga harkan kowa musamman wa'yanda su ka haɗa alaƙa da Alinar.
Da maghrib su na buɗe baki ta gaya ma sa yayi baƙi da rana. Tana faɗin Faisal Khan ta ga ya haɗe rai.
"Shikenan dan Alinah ta rasu sai ka dena mu'amala da kowa na ta?, shikenan dan Alinah ta rasu sai ka dena zuwa masallaci? Kenan dan Alinah ka ke ibadah ba dan Allah ba?"
"Ba ki san komai ba, ki ajiye maganar nan a haka"
"Anya kana sallah ma?" Ta yi tambayar kai tsaye. Idan akwai abinda za ta ma sa ya ji daÉ—i kafin ranan rabuwar su bai fi ta taimaka ma sa wajen gyara tsakanin sa da Allah ba. And for that she has to be brave.
"Idan masallaci ki ke son zuwa ki gayawa Mr Smith zai dinga kai ki"
"Ni kai na ke so ka kai ni, bai kamata ace"
"Enough Zaytoon" ya faɗa da ɗan ƙarfi sannan ya miƙe ya bar wajen yana jin haushin kan sa da ya bari yai sakewar da Zaytoonah ta raina shi.
Daga ranan kuma ya dena ma ta magana ko ta gaishe shi haka zai amsa sama-sama ko idon ta ba zai kalla ba. BuÉ—e baki da su ke yi tare kuma ya dena hakan kuma shi ya fi damun Zaytoonah...
Yau suna dawowa daga masallaci tana cikin mota tana amsawa Mr Smith tambayoyi gameda Azumin da musulmai ke yi a watan Ramadan kamar daga sama wata babbar mota ta zo ta buge su, sai da motar ta su ta je ta bugi wasu bishiyoyi da ke kusa da titin tukunna ta tsaya. Ben yai sauri yai reverse da babbar motar sa ya ƙara gaba da gudu.
Ya lura ta fara zuwa masallaci dan idan Mr Smith ya fita da ita bayan magariba sai chan dare ta ke dawowa. Ba damuwar sa ba ne tunda abin da ta ke so kenan.
Yana zaune akan gado yana duba laptop ɗin sa yana ɗan kurɓan coffee sai ga wayar sa ta hau ruri, ya jawota a hankali ya sa a kunne yana faɗin "Hello"
Abinda aka faɗa ma sa ne ya sa shi miƙewa zumɓur yana faɗin gashi nan zuwa. Yana fita ya fara ƙwalawa Ben kira amma babu shi babu dalilinsa. Dan haka a rikice ya fita ya samu dreban sa ya wuce da shi Asibiti.