Sashe 154
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun ci abinci ba ta yarda sun kwanta ba sai da ya gaya ma ta duk abinda Ghazala ta yi, ya nuna ma ta evidence ɗin da ya tara akan ta. Lokacin da ta saurari audio ɗin sai da ta yi hawaye. Nasihar Daddy ne ya ƙara faɗo ma ta a rai.
"Son zuciya da kwaɗayi su na kai mutum ga halaka, Zaytoonah ki guji son zuciya. Ke musulma ce, kin san Allah ya bawa namiji damar auren mata huɗu. Kar ki taɓa bari maganar kishiya ya sa ki saɓawa Allah"
Tana son Galadima ya zama na ta shi kaÉ—ai as if kasancewar sa ita kaÉ—ai a wajen sa shine zai ba ta guaranteed happiness. Wannan shine kuskuren Ghazala na farko.
***
"Muhsinah akwai baƙo a falon Daddyn ku, ki kai ma sa abinci Dan Allah"
"Mommy an haÉ—a abincin ne?"
"E, É—auka kawai za ki yi a kitchen"
Yau su ka baro family house su ka dawo gidan su bayan anyi sadakar bakwai É—in Alhaji Ilyasu.
Kitchen ta wuce ta É—auko abincin da aka jera akan tray ta wuce da shi falon Daddyn su. Ga mamakin ta sai ta ga Daddy ne kawai a falon yana waya.
Ta ajiye tray ɗin a ƙaramin dinning area da ke falon sannan ta ƙarasa wajen Daddyn tana jira ya gama waya dan dai baƙo aka ce ita kuma ba ta ga kowa ba.
Sai da ya gama wayar tukunna ya kalleta ya ce "Muhsinah zauna mana"
Ta zauna tana faɗin "Daddy baƙon bai iso ba ne?"
"Ya je sallah, zai shigo yanzu"
"Ok, barin wuce ciki, zan cirewa su Sadiq kayan baccin su"
"Muhsinah"
Bugun ƙirjinta ya ƙaru. Indai Daddy ya kirata da sigar jan hankali to maganar AbdulHameed zai ma ta.
"Yes, Daddy"
"Kafin Alhaji ya rasu, ya nuna min rashin dacewar zaman da ki ke a gida da aure a kan ki"
Ta san da cewa har yau AbdulHamid bai saketa ba, amma kuma itama har yau É—in ba ta ganin za ta iya komawa gidan shi.
"Muhsinah, na kira AbdulHameed ne saboda ku yi sulhu tsakanin ku. Idan hakan bai yiwu ba, na ce ma sa zai ajiye min takardar ki kafin ya tafi yau. Idan Allah ya sa kika gama idda sai ki fito da wanda ki ke so a miki aure"
"Daddy..." ta faÉ—a kaman za ta yi kuka
"Ke ba yarinya ba ce Muhsinah. Idan har iya tsawon lokacin nan ba ki iya yafewa AbdulHameed ba inaga gara kawai kowa yai hanyar sa ki dena ma sa wasa da aure a kai. A matsayina na mahaifin ki zan baki shawaran ki koma gidan mijin ki, ki koma ga 'ya'yan ki. Amma idan kin zaɓi sake sabon rayuwa a wani gidan daban wannan ba matsala ba ne, Fatana a gareki shine Allah ya sa albarka a duk inda za ki je"
Fashewa ta yi da kuka.
A da duk lokacin da AbdulHameed ya kirata ba abinda ta ke gaya ma sa illa ya saketa, wannan ne ma ya sa daga baya ya dena kiranta sai dai kawai ya tura ma ta saƙo. Yanzu da Daddy yai maganar saki kuma sai ta ji wani abu ya daki ranta.
AbdulHameed ne yai sallama ya shigo falon. Ƙananun kaya ne ajikin sa, light blue shirt da kuma blue jeans sun ma sa kyau sosai.
"Ka dawo"
"E" ya faÉ—a hankalin sa na kan Muhsinah da ke kuka.
"Allah ya karɓi ibada"
AbdulHameed ya amsa da Amin.
Daddyn Muhsinah ya miƙe ya bar mu su falon.
AbdulHameed ya ƙarisa gaban Muhsinah ya saka gwiwon sa ƙasa. Hannun ta biyu da ya kamo ne ya sa ta ɗan tsagaita kukan ta zuba ma sa ido tana zubda hawaye.
"Muhsinah, ba zan ce ki dawo gareni ba, ba zan ce ki yafe min ba, ba zan ce ki manta da abinda ya faru ba. Abu biyu kawai zan faÉ—a miki Muhsinah"
Ya ja dogon numfashi kafin ya cigaba
"Abu na farko shine, na yi nadama. ina neman gafara kullum, kuma ina ƙoƙarin nisanta kaina daga abinda zai kai ni ga faɗawa sharrin zina. Na biyu, shine, ina son ki Muhsinah, Wallahi ina son ki har yau, kuma zan so ki har gobe.
Ban faɗa sharrin zina ba dan bana son ki ko kuma dan kin gaza biya min buƙata ta, sai dai tarko ne da sheɗan ya ɗana min ni kuma son zuciya ya sa na faɗa ciki. Wannan shine abinda zan iya gaya miki. Na san Daddy ya gaya mi ki sharaɗin sa, ba zan tsane ki ba idan har kin zaɓi rabuwa da ni, dan na san i don't deserve you anymore. Kafin ki faɗi hukuncin da ki ka yanke, please ki bari na ci abinci tukunna, yunwa na ke ji, ban samu na sha ruwa ba tun ɗazu"
Hawayen da ke ƙoƙarin zubo ma sa yai saurin gogewa tareda miƙewa ya ce " ki turomin su Sadiq dan Allah, i miss them"
Kasa ƙwaƙwaran motsi ta yi tunda ya tashi, tana gani ya koma wajen dinning ya zauna.
Ba za ta ce babu soyayyar AbdulHameed a ranta ba. Ba za ta ce ba ta yi kewar mijin ta ba. Ba za ta ce ba ta jin haushin sa ba, ba za ta ce ta yafe ma sa ba, ba za kuma ta ce za ta koma gidan sa ba. But Zaytoonah was right. All this while wahala kawai ta ke bawa kan ta. The truth is, she yearn for him.
"Muhsinah kina bawa kan ki wahala ne fa. You still love him and you miss him, this is the truth. Abinda ya miki ba zai taɓa chanjawa ba, ba zai zamar da soyayyar da ki ke ma sa ƙiyayya ba, za dai ki yi ta cewa ran ki kin tsane shi, but zuciyar ki ba za ta karɓi hakan ba. Shin ba kya so ki koma gareshi ki cigaba da yi mi shi addu'a har Allah ya shiryar da shi gaba ɗaya, ki samu lada a wajen Allah. Kina tunanin akwai perfect namiji ko perfect aure yanzu a doron ƙasa?. You have to work with that imperfect marriage ki moulding na shi har sai ya zama miki yadda ki ke so may be not perfectly amma idan har akwai kwanciyar hankali a ciki shikenan"
"Wani kwanciyar hankali ne ga auren mazinaci?"
"Muhsinah kin fi kowa sanin mijin ki, kuma na san za ki ba da shaidar ya fara wannan abin ne lokacin da ba kwa tare kina Nigeria yana chan America. Ba wanda ya fi ƙarfin faɗawa tarkon Shaiɗan, i'm sure AbdulHameed yayi nadama yanzu"
"Ko da zan koma ba zai zama dan karan kaina ba Zaytoonah"
"Muhsinah ina so ki yi wani abu ɗaya. Idan har za ki koma gidan sa, to ki koma saboda kin shirya zama da mijin ki a yadda ya ke da raunin sa. Ka da ki koma saboda iyayen ki ko 'ya'yan ki. Saboda idan har zaman su za ki yi, har abada ba za ki sake samun farin ciki a auren ba. Go back because you wanted to embrace your husband's flaws and do your best to change him for the better. Ina son ki da AbdulHameed Muhsinah. Look at you, duk zaman ki a Americah ba abinda ki ka ƙara sai rama da koɗewa"
"A aurena da Galadima na koyi abu É—aya. If a man love and respect you then he's worth dying for. Tun kafin na fara son Galadima i know that he really respect me. Ki amsa wannan tambaya, truthfully banda son zuciya. Do you think a rayuwar auren ku, Abdulhameed loves and respect you?"
"Ikon Allah, Matar Galadima yaushe ki ka zama marriage counselor. The last time i remember cewa ki ka yi ba za ki sake komawa gidan sa ba"
"Lokacin da na ke da ƙarancin tunani kenan, yanzu kam mutu ka raba Insha Allah ni da Sayyadi na" ta faɗa tana fari da ido.
Muhsinah ta sa dariya.
Hiran da su ka yi kenan yau da Zaytoonah ta zo yi ma ta sallama akan za ta koma gidan Galadima, kuma gobe za su wuce Abuja.
May be itama lokaci yayi da za ta yafe wa AbdulHameed ta bashi chance na gyara kuskuren sa. Idan za ta amsa tambayar Zaytoonah to tabbas za ta ce Yes AbdulHameed love and respect her.
Sai da ta gama jujjuya komai a ranta kafin ta share hawayen ta ta je wajen dinning ɗin. Kankana da Ayaba kawai ya ci bai buɗe abincin ba balle ya taɓa.
"Sannu da shan ruwa" ta faÉ—a da dasashshiyar murya
"Na gode"
Buɗe food warmer ɗin ta yi ta fara ƙoƙarin zuba ma sa abinci. Tana yi kuma hawayen da ta yi ƙoƙarin tsayarwa ɗazu su ka fara saukowa. She missed cooking for him, she missed feeding him. She missed lokutan da su ke shan ruwa tare a lokacin Azumi.
"Muhsinah" ya kirata a hankali tareda riƙe hannun ta ɗaya.
Fashewa ta yi da kuka, hakan ya sa shi saurin miƙewa ya rungumeta.
"I'm sorry for everything, i'm sorry for hurting you. I'm sorry for cheating on you. I'm very sorry Baby" abinda ya ke ta faɗa kenan lokacin da ya ke ƙara ƙanƙame ta a jikin sa.
Sun jima a haka, dan tun tana kukan har ta zo ta yi shiru ta lafe jikinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Yaran da su ka shigo falon suna kiran Abba, Abba, shi ya sa Muhsinah ta janye jikin ta daga na shi.
Bar mu su wajen ta yi dan ya samu ya gana da 'ya'yan sa da kyau, duk da a wajen sa ya so a ce ta zauna ya ci abincin a gaban ta.
Kafin ya tafi da Daddy ya tambayeta abinda ta yanke cewa ta yi za ta koma gidan AbdulHameed. Ya haÉ—a su ya mu su nasiha.
Bayan AbdulHameed ya tafi ne Muhsinah ta samu daman tura ma sa text.
*na amince zan koma gidan ka, but kar ka É—auka komai zai koma dai-dai lokaci guda. I need time to heal*
Kusan minti bakwai sannan reply É—in sa ya shigo
*na gode Baby, zan ba ki duk lokacin da ki ke so*