← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 161

Sashe 153

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunan ta a group Mrs Galadima. Wata rana wata 'yar ajin su da su ka yi JSS 1 zuwa SS 1 tare ta ga sunan sai ta ke tambayar wai waye Mrs Galadiman nan ne. 'Yan neman tsokala kuwa tuni aka samu wata ta turo hoto lokacin su na JSS 3, ga su nan 'yan É—agwas-É—agwas, ta tsakiyar cikin su kuma Zaytoonah da ta fi kowa jiki ta haÉ—e rai saboda ba ta so aka sakata É—aukan hoton dole.

Wacce ta tura hoton ta highlighing fiskar Zaytoonah a ƙasa ta rubuta ga Mrs Galadima nan.
Wacce ta yi tambayar ta turo da sticker É—in dariya tana faÉ—in wai dama Antyn aji ne Mrs Galadima. Wata kuma ta ce tukunna Galadiman suna ta ke aure ko Galadiman gaskiya na sarauta.

Caraf wata da ke son ɗaukan gulman to the next level ta yi saurin turo hoton Zaytoonah da Galadima, dukkan su tsaye, Zaytoonah ta ɗan kwanto da kanta a kafaɗar sa, shi yana sanye da Alkyabba kalar baƙi da aikin fari ita kuma Lifaya ta saka kalar baby pink.

"Ga ta nan kun ganta, matar Galadiman Zaria ce"

Ma su Hmmm na yi, ma su sa Albarka na yi, ma su cewa bai kamata ta turo hoton group ba na yi, ma su mamakin chanjawar Zaytoonah daga Antyn Aji, BuskuÉ—a, Maman Bola... zuwa classy and elegant lady kamar wannan su ma na yi.
But one thing is for sure. Allah ya riga ya ɗaga Zaytoonah. Ko su ma ta murna ko su yi baƙin ciki ta riga ta mu su fintinkau.
It doesnt matter ta ina ka fara rayuwar ka, it doesnt matter ya rayuwar ka ta kasance a baya. It doesnt matter ko kai ne ka fi kowa kyau ko muni a cikin ƙawaye ko 'yan uwan ka, it doesnt matter ko ke ce jaka ko wawuyar cikin sa'annin ki. Lokaci ɗaya idan Allah ya ɗaga darajar ka duk wani abu a baya ya zama tarihi. Ya wuce har abada kenan.

Bayan an gama gulma a group wasu su ka koma gefe suna bawa Zaytoonah haƙuri. Wasu kuma na neman shiga jikin ta ana so ayi ƙawancen da ba a yi ba a baya.
Zaytoonah da ta zo ta ga chats É—in ba ta tanka mu su ba, ba ta da lokacin tsaya biyewa wannan silly chats É—in.

Washegari da safe Zaytoonah ta zari jiki akan za ta je gidan Iya, dan kunyan ta gayawa Mommy za ta je saloon ta ke kar ta dinga tsokanar ta irin na jiya. Ita da Humairah su ka fita, su ka je aka ma ta gyaran kai sannan aka ma ta ƙananun kitso. Humairah ta ce ta bari a ma ta Lalle bayan an ma ta pedicure da manicure. Lallen ba mai yawa ba ne amma ya haska ma ta hannu da ƙafar ta.

Lokacin da su ka koma gida da ta ga Mommy sai ta haÉ—e rai dan kar ma ta tambayeta ina su ka je su ka daÉ—e.
Mommyn ma sai ta manna ma ta hauka ta shareta ba ta ce komai ba.

Bayan sallar Isha Daddy ya kirata É—akin su. Mommy na haÉ—a kayan su, Daddy ya ce ta ba su waje.

"Ikon Allah. Ko yau za a kaita É—akinta na farko albarka"

"Tunda Allah bai bani dama ba wancan lokacin, zan yi amfani da wannan na yiwa Princess nasihar da Uba ya kamata yai wa 'yar sa a lokacin da ya aurar da ita"

"Hmmm, Allah ya ba da sa'a Daddyn Zaytoonah"

Bayan fitan Mommy Daddy yai Bismillah sannan ya karanta suratul Fatiha tareda yiwa Annabi salati.

"Adaeze, i'm proud of you. Ba ki san irin daɗin da na ji ba lokacin da Mijin ki yai ta faɗa min kyawawan halayyan ki. Na ji daɗi sosai, na san duk abinda ki ka zama a yau yanada nasaba da irin tarbiyyan da Mommyn ki ta mi ki. Kinga yadda Mommy ta riƙe gidan nan ita kaɗai lokacin da bana nan, ina so ki riƙe gidan mijin ki fiye da haka. Irin tarbiyyan da aka miki shi na ke so ki yiwa 'ya'yan Mijin ki and even more, ki riƙe 'ya'yan mijin ki fiye da yadda za ki riƙe Alinah da twins ɗin ki. Ki rage fushi Zaytoonah, ki cigaba da haƙuri and most importantly addu'a Zaytoonah. Ki riƙe addu'a sosai. Na san Allah ya buɗewa mijin ki sannan kema Allah ya baki dukiya. Ka da ki taɓa bari wannan ya ruɗa ki har ya mantar da ke ibada da addu'a. Duk wannan ƙyale-ƙyalen a duniya kawai ya tsaya, ranan da za a saka ki a kabari waɗannan abubuwa ba za su bi ki ba, ibadar ki da kyawawan halayen ki su ne za su biki cikin kabarin ki. Ki duba tsohon mijin ki Allah ya jiƙan rai. Duk abinda ya tara a duniya lokacin da ciwo ya sameshi ba abinda su ka ma sa, lokacin da aka cusa shi cikin kabarin sa babu ko abu ɗaya da aka haɗa ma sa da shi. Haka ya tafi ya bar komai a nan duniya.
Zaytoonah idan har duniyan nan ba matabbata ba ce, ina roƙon ki da ki dinga tunawa da mutuwar ki, ina roƙon ki da ki dinga ƙoƙarin kusanta kan ki ga Ubangijin ki. Hakan zai sa Shaiɗan ba zai taɓa samun galaba a kan ki ba. Idan abu ya shige miki duhu a gidan Mijin ki ba kuka za ki yi ba, ba fushi za ki yi ba, ko ki dinga yiwa mijin ki rashin kunya. Alwala za ki yi, ki yi sallah ki gayawa Allah matsalolin ki. Idan zuciyar ki ta cunkushe ki ka rasa jin daɗi, ki ka rasa samun sukuni, ki ka rasa mafita kinga wannan"
Ta ɗago idonta da tuni su ka cika da hawaye ta kalli Daddyn ta. Ƙur'ani ne a hannun sa.
Daddy ya miƙa ma ta ƙur'anin ya ce "ki dinga karanta shi safe da yamma, ki dinga karanta shi a lokacin da ki ke cikin matsala, ki dinga karanta shi a lokacin da ku ka samu saɓani da mijin ki. A lokacin da mijin ki ya ɓata miki rai ki karanta shi. Ki karanta shi a lokutan da kike cikin farinciki, ki kiyaye raya ranakun farincikin ki da abubuwan da ba su da amfani. Idan kina farin ciki ki tuna Allah, idan kina cikin ƙunci ki tuna Allah wannan zai sama miki matsayi a wajen Allahu. Daga ƙarshe ina so ki sani cewa ƙofa ta a buɗe ta ke gareki, idan abu ya shige miki duhu kina buƙatar shawara ko ƙarin fahimta ina tare da ke. Ki sani kasancewar ki matar Galadima bai yanke cewa ni ɗin mahaifin ki ba ne. Kada ki manta cewa you'll always be Zaytoonah Tijjani Abubakar. ba za a kiraki da sunan wani ba sai sunana ko da kuwa ba na raye. Just know that idan ina raye i'll always be there for you my princess"...

Ƙarfe tara da minti shida kiran Galadima ya shigo wayarta. Humairah da ke gefe ta miƙa ma ta wayar.
Zaytoonah ta karɓa ta sa a kunne.

"Ranki shi daÉ—e na iso"

Muryanta ƙasa-ƙasa ta ce " ka shigo Daddy na son ganin ka"

"Duk yadda ki ka ce Gimbiya. Gani nan zuwa"

Minti biyu bai cika ba ya shigo, inda ya samu Daddy a falo. Bayan sun gaisa ya cewa Junior da ke zaune gefen sa akan ya je ya kira ma sa Zaytoonah.

Ko da junior ya faɗi saƙo ya tafi kasa miƙewa ta yi sai da Humairah ta yi ta ba ta baki kafin ta tashi da ƙyar.
Humairan ta raka ta falon kafin ta juya ta koma ɗaki bayan sun gaisa da Galadima. Duk yadda Galadima ya so ya iya haƙurin rashin kallon Zaytoonah bai iya ba, lokacin da ta shigo da sallama da ya ji muryanta ɗagowa yai ya zuba ma ta na mujiya har sai da ta samu waje ta zauna gefen Daddy kafin ya iya sauke idon sa da sauri saboda lura da yai da idon Daddy akan sa ya ke.

Addu'a Daddy ya mu su sannan ya damƙawa Galadima amanar 'yar sa.

"Ka san dai Princess ce a wajena dan haka ka kula min da ita da kyau" Galadima ya ce Insha Allahu.

Humairah, Junior da Daddy ne su ka raka Zaytoonah wajen Mota. Mommy kam ƙin fitowa ta yi tun bayan da su ka gaisa da Galadima.

Suna barin anguwar Zaytoonah ta saka kuka. Galadima ya jawota jikin sa yana lallashi. Bai ji haushin kukan da ta ke ba dan ya san rabuwa da Mahaifinta ne ya jawo haka. Duk da dai ba su da nisa amma ba za ta sake zama da shi kamar da ba, ganin sa ma kuma ya zama sai lokaci zuwa lokaci. Kafin su ƙarisa gidan ta dena kuka, ta dai yi lamo a jikinsa tana shaƙan daddaɗan turaren sa. It was as if yau ta fara jin ƙanshin, ya ma ta daɗi sosai.

Koda su ka isa gidan kai tsaye falon sa su ka wuce. Sai a lokacin Galadima ya sami damar rungume abar sa da kyau. Itama ta lafe jikin sa tanajin wani sabon son shi na shigar ta.

"Allah ya miki albarka Zaytoon"
Ta amsa da Amin. Sun jima tsaye kafin daga baya Zaytoonah ta janye jiki ta tambayeshi mi za ta dafa ma sa amma ya ce ba yau ba Baba Nafi ta riga ta mu su girki amma bai ci ba dan yana jiran ta zo ta ba shi a baki.

Da suka fara cin abinci ne ya ce ma ta "kinga Mijin ki hankalin ki ya kwanta, ina kuma aka bar min 'ya?"

"Na sayar da ita"

"Lallai za ki haifi wata yanzu-yanzun nan kenan"

Zaytoonah ta yi murmushi.
Chapter 153 · 0% Book details