Sashe 146
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Da gaske Aysha" ta gyaɗa kai tareda nuna ma sa inda su ke cin abinci. Ya ƙarisa wajen da gudu yana faɗin Daddy. Rungumeshi yai ta baya yana sauke ajiyar zuciya sai kuma hawaye su ka fara zubowa.
"First Son kai ne ka zama babban mutum haka? Jikokina nawa yanzu?"
"Daddy, ai har yanzu first Son É—in ka gauro ne"
"Maryam ya haka? Ya kuka bar min É—a yana rayuwa shi kaÉ—ai?"
Mommy ta ce "tunda ka zo yanzu kam shikenan sai ka ma sa aure"
Hashir ya ce "GrandPa, Anty Humairah zai aura fa. Ranan ma tana cewa 'idan na auri Hamm..." kafin ya ƙarisa Humairah ta buge bakin sa.
"Ah! Lallai abu yayi kyau" Humairah da Auwal su ka kalli juna, suna haÉ—a ido Humairah ta yi saurin sunkuyar da kai.
Ƙaddara da ta riga fata kenan. Bai taɓa kawowa ran sa Auwal ba zai auri 'yar sa Zaytoonah ba. Abu ne da yai sha'awar sa tun ma Zaytoonah na ƙarama dayaga irin shaƙuwar su da Auwal ɗin.
Tareda Auwal aka ƙarisa abincin kafin bayan sun nitsu T J ya ce zai je ya ga Iya tunda ya ji a bakin yaran cewa tana raye.
Zuga guda su ka fita daga gidan kowa baya son yin nisa da T J. Suna fita Mommy ta yi sujudish shukri tana ƙara miƙa godiya ga Allahu Akbar...
A gidan ma dai an yi koke-koke. Iya na kuka T J na yi. Muntari na ɗaki yana yin na sa. Yana ɗaki ya jiyo hayaniyar yaran dan su suka fara shigowa su ka gabatar da Daddy wa Iya da ke zaune a falo tana shan kunu. Tabbas dai ɗan uwan sa ne ya dawo, to da wani idon zai kalleshi? Wannan ya sa ya tuƙa keken sa ya je ya sawa ƙofar ɗakin sakata.
Shi ya cuci Hamma Tijjani, ya raba shi da gida shekaru shaÉ—aya.
Da ƙyar Iya ta haƙura ta dena kuka.
Ta waiwaya ba ta ga Muntari ba. "Ina Muntari ya ke? Ku je ku kirashi"
Junior ya ce sun je amma É—akin sa a kulle.
"Muntari na gidan nan?" T J ya tambaya da mamaki. A iya sanin sa Muntari na da gida, gidan ma da ya taka na shi a komai.
"Yana nan Shehu. Ka je ka same shi na san kunyar ka ya ke ji"
Ko da ya je ya buga ƙofar ƙin buɗewa yai hakan ya sa Auwal ya kawo ma sa spare keys ɗin ɗakunan gidan ya karɓa ya buɗe da shi.
Ganin Muntari akan wheelchair ya sa shi zaro ido.
"Mukhtar" ya kitɓra sunan sa a hankali.
"Kar ka ƙariso Hamma. Ban zanzanci ganin ka ba" yai maganar yana juya keken sa gefe.
Kishi da Hassada su suka kawo wannan rana.
T J ya ƙarisa wajen Muntari da ya rufe fiskar sa da tafukan hannunsa yana kuka.
"ÆŠan uwa Dan Allah ka bar kuka. Godiya za ka yiwa Allah"
"Ka barni na yi kuka Hamma. Ni ne sanadin komai, ni ne na rushe ma ka farin cikin ka, ni na rabaka da iyalin ka. Ni ne silar komai"
Bai gama gane mi Muntarin ke faɗi ba amma kuma koma minene shi ya yafewa ɗan uwan sa. Rayuwar sa ta ishe shi ishara cewa duniyar nan ba komai ba ne. Wanda ya riƙe Allah shine zai samu rabo. Yafiya yana ɗaya daga cikin abinda ke ɗaga darajar mutum a wajen Allah. Tun jiya da Malam Zulkiflu ya tabbatar ma sa Asiri aka ma sa ya ce ya yafe wa koma wanene.
"Maryam ba ta gaya ma ka ba ne?. Ni ne na sa aka ma ka kurciyya"
Abu ne da bai yi tunanin ji ba amma ya riga ya faru. Kuma nadaman daya gani a wajen Muntarin ya nuna ma sa cewa É—an uwan sa ya jima da tuba...
Ƙarfe tara na dare Auwal ya tattaro kan yaran su ka koma gidan Iya dan achan za su kwana. Duk cikin yaran ba wanda ya so haka sai dai abinda ya dace kenan. Mommy da Daddy su na buƙatan kaɗaici. Mommy ce ta fi dacewa ta bawa T J labarin komai, labarin abinda ya faru iya tsawon lokacin da yai baya nan.
Bayan tafiyan Yaran Mommy ta je ta kulle gida lokacin T J na banÉ—aki.
Shirin kwanciya ta yi amma T J ya ce bai san komai ba yana son sanin komai daya faru.
"Ka huta mana Barkindo"
Ya girgiza kai ya ce " ba zan iya ba Maryama tun É—azu ma daurewa kawai na ke yi"
Tiryan- Tiryan Mommy ta shiga bashi labarin rayuwar da su ka yi tun lokacin da aka neme shi aka rasa a Asibiti.
Irin faman da ta yi da Muntari har ta kai ta yiwa Zaytoonah aure da wuri. Tunda ta fara labarin bai katse ta ba, sai faman sauke ajiyar zuciya da ya ke yi musamman da ta gaya ma sa Goggo ta rasu. Labarin rayuwar Zaytoonah ya fi komai taɓa shi musamman lokacin da ta faɗa ma sa irin haukan da Zaytoonan ta yi immediately bayan rasuwan mijin ta.
"Yanzu ya saketa kenan?" Ya tambaya lokacin da ta faÉ—a ma sa dalilin dawowar Zaytoonah gida.
"Bai ce ya saketa ba ya dai ce ta zo gida zai neme ta"
"Idan ma baya sonta ni ina son ta ya sawwaƙa ma ta kawai"
"Ya sawwaƙa ma ta muna shirin shan suna nan da watanni ma su zuwa"
T J ya zaro ido. "Alinah ta yi wata shida kuwa?"
"Ni dai ba ruwana, ka tambayi 'yar ka" ta faÉ—a tana murmushi.
Bayan ta gama na ta labarin shima ya ba ta na shi wasu abubuwan ya iya tuna su wasu kuwa bai iya tunawa ba. Mommy kam sai da ta yi kuka da ƙyar ma ta bari ya kai ƙarshen labarin.
Mutum kenan. Akan Mace, akan dukiya da kuÉ—i, akan siyasa, akan kishiya, akan sarauta, akan soyayya ba abinda Mutum ba zai iya yi ba.
Lokacin da su ka kwanta ƙarfe huɗu saura na Asuba. Mommyn ce ma ta kwanta shi kam Alwala yai ya fara sallah. Bayan sallar Asuba ne ya samu ya kwanta
Har za su kwanta ya ce " Maryam na ga hotunan sirikai na"
Mommy ta ɗau wayarta ta fara dubawa hoton Zuhayr ta fara nuna ma sa. Tareda Zaytoonah su ka ɗauka lokacin da su ka zo Nigeria. Ya fi minti biyu yana kallo kafin ya ma sa addu'a sannan ya ce ta nuna ma sa hoton Galadima. Ya dai taɓa ganin sa tun ma ba a bashi sarautan Galadiman Zazzau ba amma gaskiya ba zai iya tuno kamannin sa ba yanzu.
Recent hotunan da su ka yi da Zaytoonah lokacin da su ka kai mu su ziyara a Las Vegas ta nuna ma sa.
"Allah mai sarrafa al'amura"
"Ka san shi ne?"
"Shine Alkalin da na ce mi ki na yi aikin gadi a gidan sa na shekaru biyu"
T J na aiki a gidan Justice Yunus lafiya-lafiya, kwatsam watarana Justice yayi wani baƙo daga Kano. Justice ya zo raka shi airport suna cikin mota mutumin ya ƙyalla ido ya ga T J da ya buɗe mu su gate. Ai kuwa ya ce Dreba ya tsaya.
"Justice kaman Dr Tijjani na ke gani"
"Dr Tijjani?"
Abokin sa ya ce "Malamin mu ne lokacin ina yin Masters É—ina a ABU"
Fitowa dukkan su biyu su ka yi daga cikin mota dan abokin ya tabbatar cause Justice dai ya san Maigadin sa sunan sa Malam Shehu ba Dr Tijjani ba.
"Dr Tijjani Abubakar Modibbo" abokin ya kira yana tsurawa Malam Shehu ido. Sai dai Malam Shehu ya ƙeƙasa ƙasa ya ce ba shi ba ne, bai ma taɓa jin sunan ba. Abun ya bawa abokin Justice mamaki, ya dai haƙura ya tafi akan ƙila kamanni ne kawai.
Sai dai bayan tafiyar sa washegari Malam Shehu ya ajiye aiki a gidan Justice ya ƙara gaba.
"Mommy ta ce what a coincidence. Kai ba abunda za mu ce sai dai Alhamdulillah"
2/11/21, 10:04 PM - ****: 72
Bismillahir Rahmanir Rahim
*The truth*
Tun da sassafe Zaytoonah da Humairah su ka shiga kitchen inda su ke haɗa special breakfast wa Daddyn su. Ƙarfe bakwai ta wuce kaɗan su ka gama komai.
Bayan ta shirya Alinah ta wuce ɗakin da 'yan biyu su ka kwana dan ta ba su kayan da za su saka. Daga bakin ƙofa ta ke jin kaman yaran na waya, ta tura ƙofan a hankali ta shiga.
Salman na zaune a bakin gado yana danna laptop yaran na ta kuma Hadid na riƙe da waya a ta kunnen sa shima kuma Hashir ya sa kunnen sa a wajen wayan duk da kuwa a handsfree wayar ta ke.
"Daddy ina za ka zo ka ga GrandPa É—in mu ko?"
"Ofcourse dear, zan zo yau ba ma gobe ba"
Hashir ya ce "Daddy yaushe za mu koma wajen ka Mom ba ta son mu..."
Zaytoonah ta fincike wayar ta kashe.
"Salman what's the meaning of this?"
Sai a lokacin Salman ya É—ago saboda tuntuni hankalin sa na kan project É—in sa da ya ke gyarawa.
"Ba magana na ke ma ka ba"
"Miye kenan?"
"Really! Bayan ka san bama tare amma shine ka ke kira mu su Daddyn Raziya a waya"
"Adaeze matsalar ki da shi daban. Yaran nan ba ruwan su"
"Eh lallai. To daga yau ba na so, Thank God 'ya'yana ne ba na shi ba, kar ka ƙara bari su yi magana da shi"
"Kun fi kusa. Lokacin da za ki zo kina rarrashi ta cikin bargo ba na nan ai, ina chan ina fama da rungume filo"
"Ka fara min rashin kunyar da ka saba ko. Wallahi zan haÉ—a ka da Daddy"
Jefa kayan yaran ta yi a kan gado ta ce "ku saka da kan ku. And, yau ni da ku a gidan nan" ta snapping hannunta kafin ta fice a ɗakin ranta a ɓace...
***
"Hajiya Ghazala manya. Na ji ance Galadima ya tafi wajen uwargidan ki... ?"
"Uwargida? Har kin sa ni jin amai wallahi. Ban taɓa ɗaukan Zaytoonah da wannan matsayi ba. Idan ba ƙaddara ba yaushe zan haɗa miji da wannan yarinyar"