Sashe 126
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da waƙar ta tsaya kafin Zaytoonah ta dena rawan. Ta yanko cake kaɗan ta ɗan rankwafa kaɗan ta miƙa wa Galadima cake ɗin tana faɗin " Yallaɓai ina ma ka addu'ar ƙarin lafiya, nisan kwana, Arziƙi, buɗi, rufin asiri, kwanciyar hankali, Albarkar 'ya'ya da ta jikoki da kuma farin ciki dawamamme. Happy birthday Sayyidi Zannoon"
Justice da tuni ya buge da murmushi ya amshi cake É—in ya fara taunawa yana faÉ—in "Amin ya Allah na gode"
"Happy birthday Daddy" Hadid da Hashir su ka faÉ—a a tare, suma yaran sai su ka faÉ—a.
"Come here my Boys" ya faÉ—a yana ware mu su hannun sa su ka zo da gudu su ka rungumeshi.
Ghazala dai zuciyar ta fashewa ne kawai bai yi ba a lokacin nan.
Itama Raziya abin ya burgeta amma haushin Zaytoonah ya sa ta joining Ghazala wajen haÉ—e rai.
Sai da ya bawa sauran yaran cake a baki harda Raziya kafin su ka je su ka wanke hannun su...
"Mu je ko" Galadima ya faÉ—a yayinda yai hanyar waje.
"Abu Razz inaga mu haƙura da fitan nan tunda na ga Zaytoonah ta riga ta gama komai" ta faɗa ranta na ƙuna. Zaytoonah na gefe tana nuna ma ta hips ɗinta tana dariya ƙasa-ƙasa. Da ke Justice ya ba ta baya bai ga abinda ta ke ba amma ita Ghazalar ta gani.
"Mum riga mun yi niyya mu je kawai" bai jira mi za ta ce ba ya fice daga falon yayinda dukka Yaran su ka take ma sa baya.
"Bariki ko? Wallahi ni da ke a gidan nan"
"Bariki iyawa ne Hajiya. Plz ki kula min da shi kin ji, dan Allah kar ki bari ƙura ya taɓa sweet gemun san nan"
Ghazala ta zaro ido tana mamakin Zaytoonah. Anya kuwa ita ce sokuwar yarinyar nan da ta shigo ta samu farkon zuwan ta?
*Nima dai na ce anya ita ce?*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 62
Bismillahir Rahmanir Rahim
*The Ghost*
"Abu Razz wannan ba adalci ba ne, É—azu da safe Zaytoonah ta yi abinda ranta ke so ba ka ma ta magana ba amma yanzu sai ka ce min ina abu kamar yarinya, a cikin kwanaki na fa ta min shishshigi"
"Ghazala inada gida a garin nan ba zan je na yi kwanan hotel ba, abinda Zaytoon ta yi iya cikin gida ne bai kai waje ba"
"Dama na jima da sanin cewa adalcin ka iya Zaytoonah ya tsaya bai kai waje na ba. Kullum idan ni ce sai dai ace ina abu kaman yarinya. Na yadda ni ba yarinya ba ce amma dai nima matar ka ce kuma ina buƙatar kulawa da tarairaya" ta yi maganar tana share hawayen ƙarya.
Ta san halin sa sarai, idan akwai abinda ke saurin birkita shi bai fi a tuhumeshi da rashin adalci ba.
"Shikenan, za mu fita amma ba za mu kwana ba. Zuwa ƙarfe goma ko shaɗaya za mu dawo, ba zan kwana a hotel bayan iyalina na nan gida ba"
"Dear mu kai dai ƙarfe shaɗayan"
Ficewa yai daga É—akin dan ya wuce masallaci, dama Alwala yai zai fita Ghazala ta tsare shi da maganar fitar da za su yi.
Bayan ya fita ta yi sauri ta faÉ—a banÉ—aki dan ta shirya kafin ya dawo.
Ɗakin Zaytoonah ya shiga amma ba ta ciki dan haka ya fito ya sauka ƙasa.
A nan ya sameta zaune a falo tana raba Shari'a. Jallabiya ta sakawa yaran na ta amma kowa na faÉ—in ba na sa ba ne.
"Idan ba ku min shiru ba sai na zane ku"
"Daddy" su ka faɗa a tare tareda ƙarasawa wajensa da gudu
"Daddy ta sa min Jallabiyar Hadid"
"Nima na Hashir ta samin"
"Kun san mi za ayi?" Dukkan su suka girgiza kai
"Mu je masallaci mu yi sallah idan mun dawo sai kowa a chanja ma sa kaya"
"Ok Daddy"su ka faÉ—a cikin gamsuwa
"Mun wuce masallaci"
"Allah ya dawo da ku lafiya Amin"
Amin ya furta tareda ficewa daga falon riƙe da hannun Yaran...
Zaytoonah na cikin gyara gado ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofa.
"Come in" ta faÉ—a ba tareda ta juya ba.
Ƙaran tsinin takalmin Ghazala ne ya sa ta yi saurin juyowa.
Sanye ta ke da wani Arabian gown golden colour, gaskiya gown É—in na da kyau sosai, sai dai da ya haÉ—u da jiki mai kyau da abin zai fi armashi.
"Mun fita dinner ni da Mahbubi na" ta faÉ—a tana murmushi.
Zaytoonah ma murmushin ta yi ta ƙarisa wajen dressing mirror ɗin ta ta ɗauki Robb ta ce "a dawo lafiya Hajiya na riga na tanadi kayan aiki dan gobe da safe akwai jinya"
Ghazala ta danne ɓacin ranta ta ce "ki yi bacci fa, kin san abin da cin rai"
"Sosai ma, dan na bar Sayyidi a hannun tsohuwa"
"Chan ta matse miki" ta faɗa tareda juyawa tana tafiyar ƙasaita.
"Hajiya ba sai kin ma sa ciko ba ya jima da sanin Fanteka ne"
Ba tareda ta juyo ba ta ma ta daƙuwa da hannu.
Sai da ta fita kuma Zaytoonah ta zauna kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Ko ba ta faÉ—a ba kishi ne ke cinta. Ta so a ce wannan rana na ta ne , da Justice ya ga tarairaya a wajen ta, ko da ya ke gobe zai shigo hannu.
Ghazala da Galadima kuwa da su ka fita Dreba bai sauke su a ko'ina ba sai katafaren hotel ɗin da Ghazala ta kama mu su. Suna zuwa aka miƙa mu su key yayinda ɗan jagora ya mu su jagora har zuwa suite ɗin.
Ghazala ce ta buɗe ƙofar dan haka tana rufewa ta cire baƙar after dress da ta ɗaura akan gown ɗinta. Da farko a haka ta fito za su tafi Justice ya korata akan bai yarda su fita haka ba saboda yadda gown ɗin ya kama jikinta shine da ta koma ɗaki ta ɗaura after dress a kai. Ta ji daɗi Zaytoonah ba ta falon da yau ta sha kunya da tsokala a wajenta.
Ɗakine Babba da ya sha ado da ƙyale-ƙyalen decoration na birthday.
"Mahbubi mu je ko" ta faÉ—a tana kama hannun sa.
Kai tsaye wani ƙayataccen waje ta kaishi inda aka setting dinner a wajen. Kan table ɗin an ƙawata shi da adon flowers da candles a tsakiyar kuma wani ƙaton cake ne wanda a ƙalla zai kai irin na 100k ɗin nan.
"Ghazala wannan almabazzaranci ne"
"Ni dai neman lada na ke, kuma na tabbata zan samu tunda komai na yi ne domin Miji na"
Girgiza kai kawai yai ya ja kujera ya zauna, itama zaman ta yi a wajen ...
Cake ta saka shi yankawa yanayi tana É—aukan shi video da waya. Da ya gama itama irin na Zaytoonah ta yanko cake ta ma sa addu'a kafin ta bashi a baki ya ci. Bayan wannan ta shiga buÉ—e abincin tana serving É—in sa.
"Ya isa Ghazala, a ƙoshe na ke"
Duk da ta san shi ba mai son cika cikin sa da dare ba ne amma wannan da ta zuba ma sa ko yaro albarka.
Ba ta bari ya riƙe sokalin ba ita ke bashi a baki har sai da ya ce ya isa kafin ta bari. Bayan sun gama cin abinci ta ce "Mahbubi na ce yau na taɓo ƙuruciya nima. I want to dance for you"
Ko kaÉ—an babu plan É—in rawa a cikin abinda ta shirya amma ganin rawan da Zaytoonah ta yi da safe ya sa itama ta sa a ranta dole sai ta yi.
Galadima dai ya zuba ma ta ido yana ganin ikon Allah yadda wannan mata ta shi ta dage da yin rawa. Idan ya ce ma ta ta bari ya san fushi za ta yi shiyasa kawai ya zuba ido yana É—an murmushi lokaci zuwa lokaci.
Ba wani jiki gareta ba amma da ke abune da ba ta saba ba zuwa minti bakwai da ta yi tana tiƙar rawa sai gashi cikinta ya ƙulle musamman saboda ba ta jima da cin abinci ba, gashi dagewa ta yi da gaske tana girgiza kwankwaso, Zaytoonah ta yi gaskiya dan bum short biyu ta saka saboda ta yi ciko.
"Masha Allah! Kin yi ƙoƙari sosai. Na gode da kulawa Gimbiya Ghazala"
Kalmomine da ya faɗa dan ya yaba ma ta kar a samu matsala. A yadda ta dage da yin rawan da wani kalar rawan ta yi wanda zai dace da shekarunta da kuma yanayin jikinta da abin ya fi ba da kala amma wannan ƙuruciyar dolen da ta yaɓawa kanta sai a hankali...
Kamar da wasa da za su kwanta Justice ya fara ɗan jin cikinsa na murɗawa. Banɗaki ya shiga dan yai wanka tareda rage nauyin cikin sa dan yana ganin ciye-ciyen da yai ne ke son ja ma sa ciwon ciki. Daga hawa seat ɗin toilet sai ga gudawa ya taho da gudu, hatta Ghazala da ke ɗaki sai da ta ji ƙaran.
"Sorry Mahbubi, kuma abincin na su bai yi yaji ba. Barin sa a kawo ma ka flagyl"
Abu kaman wasa bayan Galadima ya fito daga wanka sai da ya sake komawa saboda da gasken dai cikin sa ne ya ɓace. To da safe da yara sun je shan ice cream ya sha, ya ci abinci da rana nan ma abubuwa dayawa Ghazala ta tanada ma sa ciki kuwa harda favourite ɗin sa kwaɗon zogale. Yanzu ma wani abincin ya ci ga cake da ya ɗan taɓa shima kuma kayan zaƙi ne.
Bayan ya sha maganin da aka kawo ma sa ya ce Ghazala ta tattare su koma gida. Makeken gadon da aka jiƙe shi da roses da ta ke shirin karɓan saƙo a wajen Galadima sai ga shi ko zama a kai bai yi ba balle ayi wani abu. A yadda su ka bar hotel ɗin Ghazala sai da ta tsorata dan Justice ko links ɗin hannun sa bai sa ba, hular sa ma Ghazala ce ta riƙo a hannu.
Gudu sosai ya ce Dreban na sa yai dan ba abinda ya ke son ya gani irin ya gan shi a gidan sa.
Bayan sun isa gidan ma dai sai da ya ƙara shan wani magani amma still abin ba sauƙi.