← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 161

Sashe 100

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani raɗaɗi ya ke ji a zuciyar sa. Ba yau ba ne ta fara furta irin maganan nan amma na yau ya taɓa shi sosai. Idan har ya cigaba da maganar auren nan to tabbas ya zama azzalumi.

Kusan minti bakwai babu wanda yai magana a cikin su, kowa da abinda ya ke tunani a ran sa.

Kaman daga sama ta ji ya ce " shikenan, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi"

Ta juyo ta kalleshi sai taga ya É—ara wayar sa a kunne yana yiwa dreban sa magana akan ya dawo ya maida shi gida.

A hankali ta tura ƙofan bayan ta ji ƙaran cire lock ɗin da yai. A sanyaye ta fara tafiya har ta kai cikin Asibitin. Sai da ta share fiskarta sosai kafin ta shiga ɗakin fiskarta ɗauke da murmushin dole...

***

Zaune ya ke a study room ɗin sa litattafai ne a gaban sa amma ya kasa karantawa. Maganar Zaytoonah ne ke ma sa yawo a ka. Yayi Istikhara akan maganar Zaytoonah kuma yana ji a jikin sa Alkhairi ne, sai dai dole ne ya haƙura da ita tunda ta ce ba ta so. Abu ne da ba zai taɓa yiwa 'ya'yan sa ba, Auren Dole. Dan haka gara ya haƙura kawai kar ya zama Azzalumi.

At first ya É—auka Zaytoonah za ta fahimce shi amma bayan maganan su ta yau, ba shi da wani hope akan ta.

Chan ya jawo wayar sa ya binciko hoton mijin Zaytoonah. Hoto ne da ta saka kusan watanni uku da su ka wuce.
*Gone too soon. I miss you my love* abinda ta saka kenan a ƙasan hoton ranan da ta ɗaura shi a status ɗin ta.

Hoto ne da aka É—auka yana zaune akan wheelchair a masallacin Ka'abah yana zaune yana murmushi. A hoton sa na gaba ne ta rubuta * 4 years, 3 months, 3 days without you D*.
Tausayinta ya ke ji sosai tun lokacin da ya san cewa Mijinta ya jima da rasuwa.
Bayan tausayi akwai wani abu a ƙasan ran sa gameda ita wanda ya kasa gane ainihin minene...

Sai da ta gyara zaman ta da kyau ta jawo laptop É—in kusa da ita kafin ta kunna video É—in.

"I love you D" muryan ta ya fito raÉ—au daga video É—in. Zuhayr ya manna ma ta kiss a goshi yana faÉ—in i love you more.
Ta cigaba da kallon videos É—in tanayi tana hawaye. Kusan ta haddace komai na videos É—in tsabar yawan maimaita kallon su da ta ke yi. Video É—aya ne ba ta cika kallo ba saboda video ce ta wasici da yai, kusan ma sau biyu kawai ta kalle shi.
Ta kunna video ɗin ta ƙurawa screen ɗin laptop ɗin ido tana kallon facial movement na Zuhayr har ya kai wajen da ya ke cewa.

*ina addu'ar Allah ya haɗa ki da masoyi na gaskiya, wanda zai so ki tsakani da Allah ya kuma ƙaunaci 'ya'ya na tamkar 'ya'yan cikin sa. Ina ji ajikina akwai mai share mi ki hawaye idan ba na nan, ina ji a jikina 'ya'ya na ba za su yi kukan rashin uba ba idan suna tare da shi...*

Ta yi saurin rufe Laptop ɗin saboda yadda maganganun sa ke tasiri a jikin ta kamar dai yanzu ne ya ke yin su. Ta ɗago rinannun idanun ta ta kalli agogon da ke jikin bango wanda ya nuna ƙarfe biyun dare har ta gota. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗauke Laptop ɗin da ke gabanta ta kai shi kan kujera.
Tana miƙewa akan gado ko minti biyar ba ta cika ba bacci mai nauyi yai gaba da ita.

Washegari ba ta tashi da wuri ba dan har sai da Azma ta shigo ta tasheta lokacin ƙarfe takwas na safe ta gota. Ta yi wanka tareda ɗauro alwala ta yi sallah. Tana zaune akan sallaya tana Azkar sai ga Mommy ta shigo da sallama. A bakin gado ta zauna ta jirata har ta idar da addu'o'in na ta.

"Good morning Mommy"

"Morning Adaeze"

"Na É—auka ma kin wuce Asibiti ai" ta yi maganar tana naÉ—e sallaya.

Maimakon ta amsa ma ta sai ta ce " mi kika faÉ—awa Justice jiya?"

"Ba komai" ta faÉ—a kan ta tsaye

"Ba komai? Zaytoonah ba komai?"

"Mommy what did you want me to say? Ni ba abinda na faÉ—a ma sa, idan ma shi ya ce na faÉ—i wani abu to sai ya gaya miki ai tunda dama munafuki..."

"I forbid you from ever calling him names, kina ji na ko?" Ta faÉ—a da tsawa.

"Hajia Ni'ima ta kirani yau da sassafe tana maganar Justice ya janye maganar auren ku. Infact yau za a sanar da su a Ringim.

"Adaeze addu'a na ce kiyi a kai kuma ki bani sincere feedback amma ba ki yi ba sai kawai ki ce ma sa ya janye maganar auren"

"Mommy you dont expect me to marry him right?" Ta yi maganan tana nuna kan ta.

"Kin yi addu'ar da na ce ki yi? Kin nemi zaɓin Allah kamar yadda na ce ki yi? Ko dai son zuciyar ki kawai ki ka yi amfani da shi?"

Da mamaki ta kalli Mommy idon ta fal da hawaye ta ce "Mommy ba dai abinda na ke tunani kike shirin yi ba? Mommy i didnt choose my first husband, infact aure ne aka min wanda ba ni da zaɓi akai. Shin yanzu ma ba zan zaɓi mijin da zan aura ba kenan? Yanzu ma ba ni da zaɓi kenan?, is it because he's from a royal family?.

"Mommy idan a lokacin ni yarinya ce yanzu fah? I'm an adult, zan yi aure a lokacin da na ga dama ga wanda na ga dama, kuma ba zan auri Justice ba. Infact da na aure shi gara na auri Yaya Auwal"

Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "duk abinda ki ka ga za ki iya ki yi shi Zaytoonah, kamar yadda ki ka faɗa you are an adult, Yes you are. Sai dai ki sani idan ba za ki auri Justice ba banida matsala da hakan amma maganar Auwal ki ajiye shi gefe dan matuƙar ina raye ba zan sa mi ki hannu a ciki ba"

"But why?"

"Ƙiyayyar Tijjani da Muntari ya samo asali ne akan soyayyar Maryam, kuma yau ga inda gabar ta kawo mu. Idan ba ki sani ba to ki sani, 'yar uwar ki Humairah tana son Auwal kuma ta yi iƙirarin ɗaukan mataki idan har Auwal ya aure ki. Ba zan taɓa bari gaba ta shiga tsakanin ku ba bayan dukkan ku jini ɗaya ne"

Ta miƙe tsaye tana kallon Zaytoonah ido cikin ido ta ce " kuɗi ko sarauta da Justice ke da shi ba su isa na bashi 'ya ta ba. Sai dai kyakyawan zato da na ke ma sa da wanda jama'a ke ma sa shiyasa na ji a raina zai kula min da 'ya tsakani da Allah da kuma jikoki na. Na yi addu'a kuma na nemi shawara a wajen mutane kuma still har yanzu tunanin alkhairi na ke yiwa auren nan shiyasa na amince.

"Amma tunda ke kallon uwa mai kwaÉ—ayi ki ke mini. Na cire hannuna a maganar, tunda kin ce ba kya so shima kuma ya fasa Allah ya bawa kowa rabon sa"

"Mommy ba haka..."
Ko sauraron ta ba ta yi ba ta fice daga É—akin.

Zaytoonah ta kifa kan ta a kan gado ta fashe da kuka...

***

"Allah dai ya wadaran naka ya lalace. Yanzu Maryam ɗin tana ji tana gani za ta biyewa 'yar ta. Wani irin rashin mutunci ne wannan, gidan sarauta fa! Yanzu ace jikata na auren Ɗan Sarki ai wani ƙarin daraja ne "

Auwal yai dariya ya ce " Iya kenan, kina da abin dariya wallahi. Ina ce Zaytoonan ce dai 'yar da ki ka ƙyamaceta lokacin haihuwar ta, ki ka shegantata kika ƙi ma a saka ma ta sunan ki saboda ba ki ɗauketa jinin ki ba. Yau kuma dan ta ce ba za ta auri ɗan Sarki ba har da kiran ta jikar ki"

"Auwalu!" Iya ta faÉ—a baki na rawa. Sai dai gaskiya ce ya faÉ—a. Yarinyar dai da ko kallo ba ta isheta ba ita ce yanzu hasken gidan na su, ita ce tauraruwan gidan na su.

"Ayi tsohuwa da kwaɗayi kamar ba za ta mutu ba. Miye ne a cikin auren Ɗan Sarki" ya ƙarisa maganar da tsaki sannan ya miƙe ya cire suit ɗin sa ya shige ɗaki. Dama ya dawo daga office ne Iya ta tareshi da maganar wai an bugo ma ta waya daga Ringim kan Zaytoonah ta fasa auren Galadima kuma suma sun janye maganar auren amma sun ce duk abinda aka kai an yafe.
Shi kan daɗin sa dan dama tun kiss scene ɗin nan da ya gani hankalin sa ya matuƙar tashi, ba shiri ma washegari ya dawo Zaria ya tura wani ƙanin sa Yakubu da su ke Uba ɗaya zai cigaba da jinyar Salman dan dama Yakubun ma admission da ya samu a ABU ya sa ya dawo gidan su da zama, to kuma suna hutun ƙarshen zango.

Gobe-gobe zai je Ringim ya gabatar da maganar sa da Zaytoonah. Idan sun amince ma a take ya ke so a ɗaura auren kar ya zo ya rasata kuma du. Ya sani Mommy ta hana shi Zaytoonah ne saboda Humairah ne amma ba zai iya haƙura ba, soyayyar Humairah duk shirme ne tunda yarinyar da ta ke iƙirarin tana son shi amma hakan bai hanata kula wasu samarin ba. Tun da ya mallaki hankalin sa ya fahimci yana son Zaytoonah bai ƙara kallon wata mace da sunan so ba. Ko lokacin da aka yi auren ta da Zuhayr bai iya son wata ba...
Chapter 100 · 0% Book details