← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 161

Sashe 73

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni an riga an karɓo result daga Lab ga kuma report da aka gama haɗawa na crime scene ɗin.
An jima ana bayani kafin daga baya aka ba wa Zaytoonah takarda ta sa hannu wanda ke wanketa daga duk wani laifi da ake tuhumarta.
Bisa report da aka haɗa, wanda yai kisan facts da aka haɗa ya nuna namiji ne dan har tsayin sa sai da aka ƙiyasta. Sannan lokacin da Linda ta mutu da lokacin da Zaytoonah ta zo gidan akwai tazaran kusan minti shatakwas. Sannan text ɗin da aka tura da wayar Linda an goge shi amma kuma text ɗin na wayar Zaytoonah kuma an yi bincike an gane cewa text ɗin ya shigo ne mintuna kaɗan bayan Linda ta mutu.

Duk da an wanke Zaytoonah daga zargin da ake ciki ba a rufe case É—in ba saboda za a cigaba da bincike wajen gano wanda yai kisan dan wanda yai kisan wanda ya san Linda da kuma Zaytoonah ne.

Duk maganar da akeyi hannunta na cikin na Zuhayr yana matsasu a hankali. Duk yadda ya ba ta baki a gida akan kar ta yi kuka sai da ta yi lokacin da aka ba ta takardar dan ta yi signing. Duk da tana da yaƙinin Allah zai taimaketa amma ba ta san taimako da wuri haka zai zo ba, har ta fara tunanin ga ta nan an gurfanar da ita gaban kotu tana ba da bahasi.

Allah kenan, wani lokaci ka ga taimakon sa cikin gaggawa wani lokaci ya jinkirta taimakon zuwa wani lokaci saboda dalilin da ya barwa kan sa sani. Daga ƙarshe idan ka yi addu'a ka yi haƙuri sai kaga duk lokacin da ka samu taimakon Ubangiji to lokacin ne ya ke daidai a gareka, lokacin ne ya fi dacewa da kai.

Ben fakewa yai da zai je office amma a zahiri bin su yai ya bibiyi sakamakon report ɗin dan ya tabbatar da cewa Mr John ya yi abinda ya sa shi sai kuma ya riski komai ya juye. Kiran Mr John yai sai matar sa ta ɗauka inda ta ke ce ma sa yana kwance an ma sa allurar bacci. Ya daki steering motar sa da ƙarfi yana faɗin shit. Sai da ya jima a wajen kafin daga baya yai reverse da motar sa ya tafi.

***

Tana shiga É—akin abinda ta farayi shine sujudush shukri. Lokacin da ta É—ago kuma sai ta faÉ—a jikin Zuhayr da ke tsaye.
"Thank you, Thank you Zuhayr"

Ya sa hannu ya rungumeta sosai.

"Daga yanzu zan dinga kula da ke fiye da da, duk inda za ki je ki gaya min kin ji?"

Ta gyaÉ—a ma sa kai.

"Ki faÉ—a min mi ki ke so?"

"Ka kaini Nigeria, ina son ganin Mommy da ƙannena"

"Done, kina gama exams za mu tafi. FaÉ—a min sai me?"

"Za ka dena cemin Baby girl, i'm not a Baby" ta faɗa tana ɗan turo baki duk da wai ganin fiskarta ya ke ba dan har lokacin tana ƙirjinsa.

Yai murmushi ya ce " Baby kam ta girma tunda akwai tiny Baby a cikinta"

Jin maganar ya sa ta sake shigewa jikin sa dan kunyar sa ta ji.

"Ni kam ki bani dama na baki maganin kunyan nan, kema za ki huta Allah"

"Hu'uum, ba na so"

"To mi ki ke so?"

"Shikenan"

"Ban yarda ba. Ki faÉ—i duk abinda ki ke so da wanda ba kya so. Ko ni ne ba kya so ki faÉ—a"

Maganar ƙarshe sai ya sa ta ji gwiwar ta yayi sanyi. Ba za ta iya cewa kai tsaye tana son Zuhayr ba amma kuma compared to farkon zuwanta yanzu ya samu matsayi sosai a zuciyarta, tun ma kafin wannan abu ya faru da ita. Ko yaushe tana nutsar da zuciyarta da cewa Zuhayr ya fi ƙarfinta, ba ta kai Zuhayr ya so ta ba balle har ya janye yarjejeniyar su na farko ya fara ganinta a matsayin matar sa. Sai dai kuma ga wani baƙon al'amari da ya faru wanda gashi wai har cikin sa ke jikinta. Ta sani abunda ya faru da kuma cikin ne ya sa Zuhayr ke ba ta wannan lovey-dovey care ɗin.

"Tell me sai me ki ke so"
Tambayarsa ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

"Ka kaini Gidan gona kuma ka koya min hawa doki"

"Ok amma bayan sai kin haihu ko"

"A'a idan mu ka dawo daga Nigeria" ta faɗa da ɗan ƙarfi.

"Ok we'll see about that. Sai me kuma"

Wannan karan sai da ta janye jikinta daga na shi sannan ta ce "idan na tambaya za ka min?"

"Ofcourse My Dear" ya faÉ—a yana sa hannu a hips É—in ta.

"Dan Allah ka raba gida da Ben, idan ina kallon sa tsoro na ke ji. Idan ma wani gidan za ka nema mana mu koma ba matsala sai ka bar ma sa wannan, amma plz ka raba gida da shi ba zan iya juran ganin sa a gidan nan ba"

Kallon ta ya ke yi har ta ƙare maganar ta bai ce komai ba. Although shi ya siyi gidan nan da kuɗin sa but tare su ke zaune da Ben for years ko lokacin da ya ke shirin auren Alinah ma bai yi tunanin zai ce Ben ya bar ma sa gida ba.
Sai dai Zaytoonah is carrying his child, idan zaman Ben tareda su is threatening to her to dole ne ya nemawa Ben wani gida ko shi ya nemi wani gidan ba, ba zai affording ya rasa babyn sa ba especially at a time where he's battling a disease.

"Ni kam idan ba za ka ce ya tafi ba to ka nema min wani gida ko da É—aki É—aya ne zan zauna amma ba zan zauna gida É—aya da Ben ba"

Maganarta ya dawo da shi daga tunanin da ya ke.

Fiskarta ya tallafo da hannun sa ya ce "dont worry Dear your wish is my command, zan nema mana wani gidan kin ji ko kin fi son wannan?"

"Duk wanda ka ke so ina so"

"Zan bar ma sa wannan saboda kar ya ji haushi a ran sa, i'll buy another house"

***

Cikin kwana uku aka sama ma sa irin gidan da ya ke so, gida ne shima a chan gefen gari dan shi baya son hayaniya. Gidan bai kai wanda su ke ciki girma ba amma shima Babba ne, shi kuma gidan yana kusa da wajen ruwa ne dan daga balcony ɗin gidan kana ganin ƙaton ruwan da ke ta gaban gidan. Ga kuma garden da ya ke ta bayan gidan wanda ya ke da girma sosai.
Within four days aka je aka gyara komai na gidan, furnitures É—in da aka bari a gidan wanda baya so duk an cire an sa sabbi.

Sai da komai ya kammala sannan ya tunkari Ben da maganar komawa sabon gidan tareda miƙa ma sa takardun tsohon gidan inda ya ce ya bar ma sa shi kyauta.

"Are you avoiding me Zuhayr?, did you believe what Zaytoonah is saying about me, did you believe i can harm anyone?. We're brothers, we're best friends, i love you more than anyone in this world, do you hate me Zuhayr?"

"No Ben, you're my friend, my family, i dont hate you"

"Then why?" Ben yai maganar da ƙarfi yana miƙewa tsaye.

Zuhayr ya miƙe ya je wajen sa ya dafa kafaɗar sa yana bashi haƙuri tareda nuna ma sa ba komai ya sa shi son raba gida da Zaytoon ba sai dan kwanciyar hankalinta, baya son abinda zai tada hankalinta ya jawowa babyn sa matsala.
Ben sai huci ya ke yi idon sa ya kaɗa yayi ja. Amma yadda Zuhayr ya kwantar da murya yana bashi haƙuri ya sa ya sauko daga fushin da ya ke yi har ya nunawa Zuhayr ba komai zai bar mu su gidan. Zuhayr ya ce ya zauna su za su tashi saboda gidan da ya samu ɗin ya burgeshi saboda yana ta kusa da teku and he loved nature.

Bayan kwana biyu da maganar su ka koma sabon gida, sun tafi da Chef Green da masu aikin Zaytoonah guda biyu wanda za su dinga shifting É—in aiki tsakanin su. Akwai security guda biyu sai kuma Driver.

Wannan gidan nisan shi da school É—in su har yayi yawa dan haka dole awa É—aya kafin aji ta ke fitowa Mr Dawson ya kaita makaranta. Shi ma kaman wancan ba gidaje kusa da shi, wannan kan ma kafin ka ga gida sai ka sha dogon tafiya ba tareda ka ga alamar gida ko mutane ba kafin ka fara tsinkayar gidajen mutane jefi-jefi.

Hankalinta kwance ta ci ta sha ta kwanta sai karatu wanda yanzu abubuwa sun ma ta yawa dan an barta a baya sosai...

*Nobody takes you away from me My Love, not even the fat girl*

Ben ne yai maganar a lokacin da ya ke kallon ƙaton hoton Zuhayr da ke bangon ɗakin sa. Yai murmushi kafin ya fita daga ɗakin.

Zuhayr na Asibiti inda ake ma sa gwaji sai ga kiran Sheikh Hassan ya shigo wayar sa. Bai É—auka ba sai da nurse É—in ta gama É—eban jinin sa kafin ya É—au waya ya kira Sheikh Hassan É—in.
Maganar da su ka yi ne ya sa shi washe baki yana murmushi. Daga Asibiti kai tsaye gidan Sheikh Hassan ya wuce inda ya ƙara tabbatarwa idon sa abinda Shiekh ɗin ya faɗa.

Ya rungumi Ben yana murmushi.
Sun jima suna tattaunawa kafin su ka É—unguma masallaci saboda sallar la'asar ya yi.
A masallacin ne aka shaidawa mutane Mr Benedict Vincent Haddish ya karɓi kalmar shahada. Nan da nan 'yan uwa musulmai aka fara murna ana rungume Ben ana taya shi murna, shi kuma sai yaƙe haƙora ya ke yi.

Sai bayan sallar Isha su ka dawo gida tare inda Zuhayr ya ce ya zo su gaisa da Zaytoonah saboda ya sani yanzu kam za ta dena jin tsoron sa.

Da ke tana falo lokacin da aka buga ƙararrawar shiga gidan ita ta tashi ta je dan ta buɗe dan ta ji alamar tsayuwar motar sa. Tuntuni ta ke jiran sa ya dawo saboda ta gaya ma sa abinda ta gano.
Chapter 73 · 0% Book details