← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 161

Sashe 84

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ciwon na sa abinda ke damun sa harda kaÉ—uwar abinda Ben ya ma sa ko ace ya jima yana ma sa. Wani irin so ne wannan? wani irin kishi ne wannan da zai sa shi kashe rayuka har uku ba tareda kuma ya damu da komai ba.
What if Mr Rogers baya gidan a ranan da sai dai Zaytoonah da yaran sa su bar duniya ba tareda sun yi laifin komai ba. Ire-iren waÉ—annan tunani su ke sa shi cikin damuwa.

Dawowar Zaytoonah kenan daga Asibiti ita da Dada sun bar Zuhayr yana bacci. Ba dan Dada ta takura ba da ba za ta dawo gida yanzu ba dan ko kaÉ—an ba ta son barin gefen Zuhayr.

Wanka ta shiga yayinda Dada ta shiga kitchen dan ta dafa mu su abinda za su ci tunda ta zo gidan ba ta yarda da wani ko wata ya musu girkin da za su ci ba musamman ma saboda abubuwan da su ka yi ta faruwa a gidan, daga baya ma sallamar su aka yi aka bar mace É—aya da za ta dinga kula da tsabtar gidan.
Tana banɗaki wayarta ya dinga ringing amma kuma ba ta fito ba dan ta riga ta tuɓe ta fara wanka. Sai da ta gama ta fito ta duba wayar sai taga miss calls ɗin Farha kusan guda huɗu da kuma na baƙin numbers da ba ta sani ba. Text ɗin Farhan ta karanta kamar haka:

*Zaytoonah kar ki yadda ki fito daga gida sai police sun zo Ben ya gudu daga psychiatric*

Jikinta ya fara rawa. Ashe ba su rabu da wannan baƙin Mugu ba har yanzu. Tunda aka kama shi aka rage securities na gidan na su sai guda biyu kacal.

"Sallallahu Alaihi Wa Sallam" Dada furta lokacin da ta gama jin bayanin da Uncle Aliyu ya ma ta. Ta yi sauri ta kashe cooker ɗin ta wuce ɗaki dan ta tabbatar da lafiyar Zaytoonah. Yanayinda ta sameta ne ya ruɗar da ita. Tana tsaye jikinta na ɓari tana maimaita kalmar "he's going to kill me, he's going to kill me"
Dada ta riƙo hannunta tana faɗin "kalleni Zaytoonah, ba abinda zai faru Insha Allahu. Allah zai karemu"

Suna tsaye suna jimamin wannan abun ne su ka ji ƙaran halbe-halbe daga waje. Zaytoonah ta ƙanƙame Dada tana kuka ko addu'ar ma ta kasa yi. Dada ma ta tsorata amma ta daure ta dinga jero addu'o'i a bakinta duk wanda ya zo ma ta.
Chan ta yi ta maza ta ɓanɓare jikinta daga na Zaytoonah ta je ta rufe ƙofar ɗakin da su ke. Sun dena jin ƙaran halbin yanzu.

"Zaytoooooooooonahhhh" Ben ya faɗa tareda ƙyalƙyalewa da dariya.

"You better come out now" yai maganar yana haurawa stairs É—in.

"Come out, come out now Fat girl"

Ya tsaya baƙin ƙofar ɗakin Zuhayr ya murɗa handle ɗin ƙofar amma kuma ya ji ta a garƙame.

Wani mahaukacin dariya yai sannan ya ce ma ta tafito ya kasheta cikin sauƙi ko kuma ta mutu cikin wahala.

"I'm going to burn down this house, so come out "

Tsabar tsoro sai da Zaytoonah ta saki fitsari daga inda ta ke zaune. Da ita da Dada kowa hawaye ya ke, sun ƙanƙame juna suna zaune a ƙasa a cikin banɗaki.

Bindiga ya sa ya fara harbin ƙofar ɗakin sai da ya ma ta kusan harbi bakwai kafin ya sa ƙafa ya ture ƙofar ɗakin sai ga ƙofar ta faɗi. Ya shigo ɗakin yana faɗin "I love him, but you took him away from me. I warned you to stay away from him but you refused to listen"

Bai gan ta a ɗakin ba dan haka ya san tana banɗaki. Ya saita bindiga dai-dai ƙofar banɗakin ya ce "for the last time come out"

Winwinwinwinwinwin... motocin 'yan sanda su ka iso gidan.

Ben yai murmushin takaici. Lokacin da Lawyer ɗin sa ya ma sa hanyar guduwa daga psychiatric ya shirya ma sa komai domin ya bar garin ba tareda an kama shi ba, daga ƙarshe kuma ya bar ƙasar gaba ɗaya. Sai dai abu ɗaya ya hanashi guduwa wato Zaytoonah. Ya rantse matuƙar bai kashe Zaytoonah ba bare bar garin ba.

Daga loudspeaker ake ma sa magana ana faÉ—in ya yi surrender saboda police sun zagaye gidan.

Ko zai mutu gara ya mutu da sanin cewa Zuhayr ba zai rayu da Zaytoonah ba.

Ƙaran bindigar da aka ji ne ya sa police su ka shigo gidan da gudu.

Kafaɗar da Ben ke riƙe da bindigar aka harba hakan ya sa bindigar ya faɗi ƙasa. Ɗaya daga cikin securities ɗin da Ben ya halbe a ƙofar gidan ne ashe bai mutu ba.

Security ɗin mai suna Micheal ya ƙariso wajen da Ben ke tsaye yana dafe da kafaɗar sa da ke fitar da jini. Ya nuna shi da bindiga yana faɗin ya ɗaga hannun sa sama. Ben ya ɗaga hannu ɗaya yana huci, Micheal ya ce "move" suna shirin fitowa daga ɗakin Ben ya juyo bazata ya make Micheal hakan ya sa bindigar hannun Micheal ta faɗi nan da nan su ka fara kokawa, daga ƙarshe dai Ben ne ya ɗau bindigar ya sa a ƙeyar Micheal su ka fito waje inda su ka yi kiciɓis da police a bakin stairs.
Ben ya nuna mu su idan ba su ja da baya ba zai halbi Micheal wannan ya sa su ka fara yin baya-baya.
Ko stairs ɗin ƙarshe ba su kai ba aka harbi Ben ta baya. Daga ƙeyar sa harsashin ya shiga ya fito ta wuya. Ben ya sa hannu a wuyan sa yana ƙoƙarin tare jinin da ke ta ɓulɓulowa amma ina ko seconds goma bai yi ba ya faɗi ƙasa ya mutu.
Sai da ya faɗi ƙasa ne police da Micheal su ka kai duban su ga wanda yai halbin.

Kevin Dawson ne tsaye da bindiga a hannun sa. Tun mutuwar mahaifinsa sakamakon Bomb É—in da Ben ya dasa a mota wa Zaytoonah ya ke bibiyar case É—in, yana son gano waye ya kashe ma sa uba. Lokacin da aka kama Ben aka kuma tabbatar da cewa shi ya kashe Alinah, ya kashe Linda sannan ya zo ya kashe Mr Dawson ya sa a ransa ko da ba a yankewa Ben hukuncin kisa ba shi sai ya kashe shi. Yana bibiyar labarin har sanda aka sanar akan guduwar Ben daga psychiatric, nan shima ya É—au aniyar indai ya ga Ben to ba makawa harbe shi zai yi. Tun farko Police Asibiti su ka fara zuwa saboda sun É—auka Zaytoonah na wajen Zuhayr dan sun tabbatar wajen Zaytoonah Ben zai fara zuwa. Sai dai shi Ben yana da masaniyar Zaytoonah ta bar Asibitin shiyasa ya wuce gidan su direct su kuma daga Asibitin ne su ka taho gidan.

Babu tsoro ko nadama a tattare da Kevin sai ma murmushi da ya ke yi saboda burinsa na É—aukar fansar kisan mahaifinsa ya cika.

Kafin minti ishirin gidan ya cika da police da ambulance da ma su bincike. An sawa Kevin ankwa an tafi da shi yayinda aka naɗe gawan Ben a cikin baƙin leather jacket da ake saka gawa a ciki aka wuce da shi mutuary...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 40

Bismillahir Rahmanir Rahim

*a new beginning*

"Karatu a Nigeria sucks Wallahi. Haka kawai ayita abu ba hutu"

Auwal da ke sauraron wayar yai ƙaramar dariya ya ce " a hakan ba gashi kin kusa gamawa ba"

"Ya Auwal ba za ka gane bane"

"Ki ji ki dai. Ni ma fa na yi Makarantar"

" ni kam ina ganin a lokacin na mu karatun ya fi wahala"

ya kwantar da kan sa a kujerar office ɗin yana cigaba da jin ƙorafin Zaytoonah. Tunda ta fara Law school na Abuja ba randa za ta zo gida weekend ko kuma su yi waya ba ta yi ƙorafin wahala ba. Da gaskiyarta dan karatun da ta yi a turai ya banbanta da nan Nigeria. Yayinda su suke ƙoƙarin sauƙaƙawa ɗaliban su ta inda karatun zai zo mu su da sauƙi a nan kam Karatu mai takuri ake yi wanda ke stressing mutum to the core.

Ƙarfe biyar ya shigo falon Mommy wanda tunda ya parker machine ɗin sa a compound ɗin gidan ya ke jin hayaniyar jikokin Mommyn.

Kokawa su ke a kan remote É—in TV wannan na faÉ—in ga inda za a kalla wannan ma na cewa bai yadda ba nashi tashar za a kalla. Suna jin sallamar sa su ka sake remote É—in su ka zo da gudu su ka rungume shi.
"Uncle Auwal Oyoyoooo"
Auwal ya tsugunna dai-dai tsayin su ya sa hannu ya rungume su. Yana son yaran sosai ji ya ke tamkar shi ya haife su balle dama 'yan biyu da su ke da shiga rai.
Fraternal twins ne dan ba za ka É—auke su 'yan biyu ba ma, tsayin su dai É—aya ne, kalar idanun su É—aya, sai muryoyin su ma É—aya, dukkan su sun É—auko blue eyes É—in Zuhayr. Shi Muhammad Hashir ya fi kamaceceniya da Zuhayr duk dama ya fi É—auko yanayin fiskar Lucile-Abigail wato mahaifiyar Zuhayr, amma Ahmad Hadid kamannin mahaifin Zuhayr ya É—auko wato ta sashen Alhaji Iliyasu dan da ka ganshi ka san jinin gidan ne.

"Uncle Auwal Chocolate" su ka haɗa baki su ka faɗa. Ta ɓangaren ciye-ciye kam Maman su Zaytoonah su ka ɗauko.

Ya fito da chocolate biyu ya bawa kowa É—aÉ—É—aya.

"Ina GrandMa?"

"Tana kitchen"

Barin su yai ya shige kitchen É—in tareda sallama. Mommy ce tsaye gaban gas cooker tana duba abu a waya, da ke hankalinta yayi nisa ba ta ma lura cewa ba ta rufe miyar da ke kan wuta ba, yana ta simmering har ya fara fatsuwa a jikin gini da gefe-gefen wajen.

"Mommy barka da yammaci" maganar da ta dawo da Mommyn kenan daga duniyar yanar gizo.

"A'a son yaushe ka shigo?" Ta yi maganar tana saurin rufe tukunya.

"Yanzun nan na ƙariso, na ɗauka ma ko kin ji mu da 'yan biyu"

"Hankalina baya wajen. Ya aiki?"

" a bit stressful amma Alhamdulillah"

Mommy ta ma sa fatan alkhairi.
Chapter 84 · 0% Book details