← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 161

Sashe 19

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin 'yan kwanakin nan kuwa ba ta ma jin daɗi, duk safiya sai sanyi ya dameta kuma ba lokacin sanyi ake ba. Ga yawan kasala da ta ke ji, ita da ta ke da kazar-kazar ɗin aiki sai gashi sai ta wuni ba ta assasa komai a ɗakin ba harta wanka sai da ta fara ƙiwuyar sa idan ta yi da safe shikenan sai kuma washe gari. Ranan su na fitowa daga class sai hajijiya ya kamata da ƙyar ta dafa bango ta samu guri ta zauna. Yanayin jikin na ta da ta ke jin chanji ya sa ta je Asibiti dan ta tari ciwon tun kafin ya zo ya hanata karatu.

Tun daga amsoshin tambayoyin da ta bawa likita ya ce alkhairi ne amma za a ma ta test dan a tabbatar. Aikuwa gwajin farko result ya nuna ciki gareta.
Kuka sosai ta fara a office É—in Likita lokacin daya bayyana ma ta sakamakon gwajin.

"Doctor seven years, one month, nine days da aure na"

Likitan wanda Musulmine ya ce " ki godewa Allah. Shi ke bayar wa a lokacin da ya so a kuma wanda ya so. Wasu ma su kan samu shekaru fiye da naki kamin Allah ya karɓi addu'an su"

With full excitement ta je gida tana tunanin yadda za ta faÉ—awa T J and how he'll react.
Ta sa a ranta sai ya zo za ta faÉ—a ma sa amma kafin washegari ta chanja shawara. Har gida za ta je ta surprising É—in sa. Daren ranan ba ta iya barcin kirki ba, motsi kaÉ—an ta shafa cikinta zuwa maranta tana murmushi.

Ranan Alhamis tana dawowa daga Class ta wuce park sai Zaria. Da murna ta nufi gidan ta dan ta san war haka T J na gida.

Da sallama ta shiga falonsu fiskarta É—auke da murmushi amma ganin wanda ke falon ya sa murmushin ya kafe. Iya ce zaune a falon tana kallo tana cin tuwo sai suÉ—e hannu ta ke yi.

"An wuni lafiya" ta furta ranta a ɓace

Iya ta ce "An gaji da karuwancin ne aka dawo?"

Ba ta tanka ma ta ba ta wuce É—akin ta. Ganin kayan T J a É—akin ya sa ta tabbatar Iya ta kwana biyu a gidan. Ta zauna bakin gado tana jin zuciyarta na ma ta zafi. Duk wani excitement da ta ke tattare da shi ya washe. Iya a gidan su kuma T J bai gaya ma ta ba.
Ganin zamanta na Iya kawo ɓacin rai ya sa kawai ta ɗau jakarta ta fita. Gara ta koma inda ta fito ko hankalinta zai kwanta dan idan ta ce za ta kwana a gidan baƙin ciki da takaici kawai za ta sha.
Ba ta samu motan Abuja ba ma sai kusan ƙarfe takwas na dare. Ita dai ko ƙarfe shabiyun dare ne ta sa a ranta za ta tafi.

T J kam tunda Iya ta fara zama a gidansa ya fara daɗewa a waje. Wani lokaci ƙarfe goma koma fiye ya ke dawowa, idan ya dawo da wuri to ƙarfe tara ne.
Bai san da zuwan Maryam ba sai washegari da Iya ke masifar wai wuyan Maryam yayi ƙauri ta zo ko zama ba ta yi ba ta kuma tafiya wani yawon.
Ya sha mamakin wai Maryam ta zo daga baya ya ce bari ya je kawai ya dubata ko lafiya ta zo gida...

As usual haƙurin nan dai da ya saba bayarwa shi ya ke ta ba ta akan rashin sanar da ita gameda zuwan Iya. Duk yadda ta ke son yi mishi Albishir haushin da ta ke ji ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Ƙarshe haka ya tafi ba tareda ta gaya ma sa ba. Bayan sati biyu da ya zo lokacin ta ɗan sakko shine ta nuna ma sa result ɗin test ɗin da aka ma ta.

"Dear shi ne ba ki da lafiya ba za ki gaya min ba"
Ya maida duban sa ga takardar yana karantawa.

Ya É—ago ido ya kalleta ya sake kallon takardar sai kuma ya challa ihu yana " Maryam da gaske?"
Ta gyaÉ—a ma sa kai.

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Muah muah muah" ya shiga kissing É—inta ta ko'ina.

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*9-good news*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Karatu Maryam ta ke babu kama hannun yaro. Yanzu kam tunda aka rufe wannan case ɗin nan ta cire rai da samun soyayyar Iya. Matar ta tsaneta to the core dan haka itama ta kama kan ta, ko sun je Ringim ba ta ko shiga ɗakinta. Sau ɗaya da ta yi ƙoƙarin shiga ta gaisheta daga bakin ƙofa Iya ta wurgeta da mafifici hakan ya sa ta fita da sauri. Tun lokacin ko kallo ƙofar ɗakin Iya ba ta yi.
Ita Iya yanzu ba ta da abokiyar gaba a duniya irin Maryam. Tunda Maryam ta zo gidan su komai ya lalace, Baffah har ya rasu fishi ya ke da ita saboda ta ƙi karɓan Maryam hannu bibbiyu. Ga uwa uba Muntari da har yau ba ta ji ɗuriyar sa ba tunda ya ce zai je Lagos. Ga uwa uba irin zagin da sarakanan ta su ka ma ta duk dan akan Maryam ɗin. Wai ace saboda Maryam Inyamura ɗan ta ya bar gida ya ƙi dawowa ba abinda ya fi wannan ci ma ta tuwo a ƙwarya.

Babban damuwarta shine yanda har yanzu shiru ba ta samu ciki ba. Goggo kan ce ma ta haihuwa lokaci ne idan Allah ya nufa lokacinta yai za ta samu.
Itama ba ta haifi Ruma ba sai da ta yi shekara huÉ—u da marigayi mijinta. Ko 'ya'ya ukun da ta haifa da Baffah haka ta haifesu da ratan shekara hurhuÉ—u ba plannning ba komai.

A ɓangaren T J ma yana son ganin Maryam ta samu ciki ko dan hankalinta ya kwanta to amma Allah ke ba da haihuwa.

Sadiq kam yau lafiya gobe ba lafiya ne, ita kan ta Hajjo rashin lafiyar Sadiq É—in ya sa ta É—an yi hankali kaÉ—an.
T j ya zaunar da ita ya ma ta bayanin ciwon Sadiq tareda gaya ma ta matuƙar su ka cigaba da zama za ta iya haihuwan 'ya'ya ma su irin lalurar sa. Ya ce ma ta zai sawwaƙa ma ta idan ya so sai ya karɓi Sadiq ɗin shi da Maryam za su raine shi, idan yana da tsawon rai to idan kuma ba mai zama ba ne duk ƙaddarar da Allah ya rubuta ma sa za su amsa hannu bibbiyu.
Amma fir Hajjo ta ƙi karɓan wannan shawara. Ita ba abinda ta ke gani irin ƙasƙanci ne T J ya saketa ya cigaba da zama da Maryam ƙabila wai har ma Maryam ce za ta reni ɗan da ta sha wahala ta haifa. Ta ce ko za su haifi irin Sadiq goma ne ba za ta rabu da shi ba.

Tsoron fushin Iya ya sa bai sawwaƙa wa Hajjo ba, yana lallaɓata ne ƙila idan ta amince su rabun Iya ba za ta ji haushi ba sai dai da Hajjon da Iyan duk sammakal. Abinda ake nuna mu su daban, abinda su ke dubawa daban.

Shekaran Sadiq biyu da wata biyar ya rasu. Ba T J da Hajjo kaɗai ba hatta Maryam ta ji mutuwar yaron nan dan tana son sa sosai. Shi ya fara kiranta da sunan Uwa a duniya "Ama" haka ya ke kiranta. A da Hajjo ba ta bari ta taɓa ma ta shi amma tun wani rana da ciwon sa ya tashi T J baya gari ta ga Maryam ne ta tsaya ma ta har aka kaishi asibiti aka yi komai sai ta janye takunkumin da ta sa, ta fara barin Maryam na riƙe yaron a hankali har yaron ma ya fi sabawa da Maryam ɗin.
Maryam yadda ta ke son yaron ita ne yi ma sa wanka, wanke kayan sa. Tsabar samun guri ko yana wajen Hajjo yai kashi indai Maryam na nan haka za ta kawo wa Maryam ta ce ga ɗan ta yayi kashi, Maryam ta karɓeshi ta ma sa tsarki ta gyara shi.

Ranan da ta fara gwada goyonsa kasa tashi ta yi ta zauna a bakin gado tana nan jijjiga shi, tana tsoron ƙila idan ta tashi faɗowa zai yi. A haka T J ya dawo ya sameta yai ta mata dariya daga baya daya ga ta yi fishi sai ya ce ma ta ta tashi ba abinda zai samu Sadiq. Sai da ta miƙe ta sa hannu ta baya incase ta ji zai faɗo ta taro shi shi kuma ya kama hannunta yana murmushi.
"See ba zai faÉ—o ba"

Sai kuma ta fashe da dariya. TJ ya kissing goshinta ya ce "Insha Allahu ke ma naki na zuwa"...

Lokacin rasuwan Sadiq saura ma ta sati ɗaya ta fara jarrabawarta na ƙarshe a makaranta. Ta dai yi jarrabawan ne kawai amma har lokacin mutuwar yaron bai saketa ba musamman da Inna Saratu ta zo mu su ta'aziyar ta dinga habaici tana referring mutuwar Sadiq da cewa "cinyeshi aka yi"
Iya kam ba ta zo ba duk da kuwa Alhaji Isa ya ba su damar su je Zaria su yi ta'aziya. Bayan anyi ukun yaron kowa ya watse amma Inna Saratu sai da ta tsaya ta ƙara kusan sati biyu wai tana kula da Hajjo.

Kasancewarta matar aure yasa ta nemi yin Service na ta a Kaduna kuma ta samu. Da farko cikin Kaduna ta ke PPA É—inta T J ya ce bai yarda ba dole ta kuma neman alfarma aka dawo da ita Zaria.
Chapter 19 · 0% Book details