← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 161

Sashe 132

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta riƙo hannun Zaytoonah su ka fito.
Ghazala na ganin suna sakkowa ta yi saurin danna waƙar da ta yi downloading yanzu-yanzun nan wanda ake cewa *Allah raka taki gona* tana bibiyar waƙan da ƙarfi-ƙarfi.

Humairah ranta ya ɓaci ta ce " amma Allah wadai na ka ya lalace. Galadima dai bai yi sa'a ba gaskiya, dan'yar tasha ya ajiye a gida"

" 'yar tashar dai ita ce da gida yanzu yarinya, aje chan ayi jinya kafin mahaukaciya ta bi Bola"

"Ke ce mahaukaciya wallahi"

"Humairah ya isa haka, mu tafi"

"Amma Mommy"

"Mu je na ce"
Mommy ta faɗa da ƙarfi. Maganar Ghazala ya taɓata sosai amma kuma idan ta biye ma ta tamkar sun zama ɗaya ne. Gaskiyar Hajiya Ni'ima da ta ke ce ma ta Ghazala dama tun asali fitsararriya ce da ba ta gaji mutunci ba tun ƙuruciya kuma har yanzu.

Har su ka fita Ghazala ba ta bar maimaita Allah raka taki gona ba.

Atika munafuka sai da ta ga sun fice daga gidan ta leƙo daga kitchen tana ayyiririri

"Takawar ki lafiya Zinariyan Galadima. Ki sha sha'anin ki gida ya zama mallakin ki"

"Ki faɗa ki sake faɗa Atika" ta faɗa tana zama tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya...

Da ke Galadima bai ba ta fuska ba ba ta iya tambayarsa abinda ke cinta ba lokacin da ya dawo gida wato ko dai da gaske ne ya saki Zaytoonah kamar yadda ta ke hasashe.

Har washegari bai sako maganar ba dan haka ta samu Raziya akan idan suna cin abinci ta tambayeshi ina Zaytoonah ta je Atika ta ce mu su ta tafi da kayanta. Da ke faÉ—an da Galadima yai ma ta har yanzu yana ranta sai ba ta iya faÉ—a mi shi ba. Cikin sa'a kuwa Suhailah ta tambayeshi ina Anty Zaytoonaha lokacin suna karyawa. Shafa kan ta yai ya ce "Anty ta yi tafiya"

"Yaushe za ta dawo?"

Raziya da Ghazala su ka zuba ma sa ido suna so su ji mi zai ce.

Kusan sakan biyar kafin ya ce "idan ta gama abinda ta je yi za ta dawo, ki ma ta addu'a kin ji"

"Daddy wai da gaske Anty ta haukace?"

"Kar ki sake faÉ—an irin maganan nan kin ji. Anty ba ta da lafiya ne kuma za ta warke"

Ghazala dai ta ji jikinta ya yi sanyi. Kamar dai ya saketa kamar kuma bai saketa ba.

"Kai yadda Mamanta ta shigo É—azu fiska a tsumen nan inaga ya saki Zaytoonah ne fa" ta faÉ—a a ran ta.

Da wuya Galadima ya saki Zaytoonah amma tana tunanin ƙila Hajia Abu ce ta saka shi dan ranta ya matuƙar ɓaci da ta ji labarin abinda Zaytoonah ta yiwa Raziya...

A chan Zaria kuwa kwana ɗaya da dawowan su zazzaɓi ya rufe Zaytoonah. Dama tana fama dashi, rashin nitsuwa ne ya sa ta watsar da duk wani ciwo da ta ke ji. Mommy da kanta ta ɗauketa su ka je Asibiti dan ita sai da su ka zo Zarian ma ta fara zargin Zaytoonah na da ciki. Bayan 'yan tambayoyi da Likita ya mata da kuma gwaji aka tabbatar mu su da Zaytoonah na da ciki. A yadda ma Likitan yai bayani kamar ma cikin ya shiga wata uku.

Maganin zazzaɓi ya rubuta ma ta da multivitamin tareda ba ta shawaran akan ta dena yawan tunani domin jinin ta ya hau.

Mommy ta yi murna da wannan labari sai dai ba ta bayyana shi ba, sai ma cewa da ta yi wa Zaytoonah akan ta yi shiru da maganar cikin ko Galadima kar ta gaya ma sa.

Zaytoonah ta gyaÉ—a ma ta kai.

Maimakon bayan Azumi da suka saka tafiyar su, Mommy chanja ra'ayi ta yi akan gara su tafi yanzu tun kafin Zaytoonah ta fara nauyi.
Cikin sati biyu aka kammala komai na tafiya su ka wuce ƙasar America.
Ko sallama ba su yiwa Galadima ba. Wayar Zaytoonah dama tuni Mommy ta karɓe shi.

Cikin Azumi da Galadima ya zo gida ne ya je gidan su Zaytoonah dan ya duba ta amma ga mamakin sa ba sa nan, Salman ya sanar ma sa ai sun tafi. Abin ya ma sa ciwo amma da ya tuna yadda su ka ƙare da Mommy sai ya gane tabbas har yanzu tana fushi da shi. Shi kan sa har yanzu yana jin haushin abinda Ghazalar ta yi.

*"idan wannan ce Raziya aka dinga yawo da hotonta a manyan social media platforms za ka ji daÉ—i? Ka duba yadda aka haÉ—a hoton nan da kyau da abinda aka rubuta: Matar da ta yanka 'yar mijinta saboda ciwon hauka. Tsakani da Allah za ka ji daÉ—i idan wannan hoton Raziya ce"*

Mommy ta faÉ—a tana nuna ma sa hoton Zaytoonah da ake ta yawo da shi.

Kasa magana yai dan bai san ta ina zai fara ba. Abu ne ya riga ya faru duk hukuncin da zai É—auka akan Ghazala ba zai dawo da hannun agogo baya ba.

*"Dan Allah ka sawwaƙe wa Zaytoonah. Idan har ciwon hauka gareta kuma ita ɗin threat ce ga 'ya'yan ka ni zan zauna da ita kuma na san za ta samu lafiya ta warke gaba ɗaya"*

Maganganun Mommy kenan ranan da ta je office ɗin sa, wanda da ƙyar ya shawo kanta ta yadda ta janye maganar saki da ta yi.
Fatan sa Allah ya sa a dace a tafiyar da su ka yi...

***

Yau ne za su fara therapy na farko saboda tun zuwan su gwaje-gwajen ƙwaƙwalwa aka ma ta kuma sakamako ya nuna cewa babu abinda ya sameta a ƙwaƙwalwa dan haka har yanzu dai treatment na PTSD za a ma ta. Sabon Likita su ka samu mai suna Dr Solomon wanda tsohon Likitan Zaytoonan ne ya haɗa su da shi domin shi baya ƙasar ya tafi ƙasar Austria.

Bayan ya ma ta wasu tambayoyi wanda ta amsa su dai dai kafin nan ya danna remote É—in hannun sa sai ga hoton Zuhayr ya bayyana a jikin projecter.

"Waye wannan?" Likitan ya tambaya yana kallon ta.

Maimakon ta bashi amsa sai ta bige da kallon hoton.

"Mrs Zaytoonah waye wannan ?" Likitan ya sake maimaita tambayar...

***

A chan gidan Justice kuwa liyafa ce ta cigaba wa Ghazala, ganin gida ya zama na ta ita ɗaya sai ta fara sauya tsarin zaman gidan. Har yanzu dai Galadima bai ba ta fuska ba saboda abinda ta aikata amma ta san zuwa lokaci kaɗan zai haƙura ya dawo da hankalinsa wajenta ita ɗaya.
Matsalar Zaytoonah yanzu ya ƙare. Su je chan su ƙarata da jinyar mahaukaciya.

Tabbas ita mai sa'a ce, ba dan ta riga ta jawo Raziya cikin lamarinta ba da abin bai zo ma ta a yadda ta ke so ba, ƙila ma da asirinta ya tonu.

Shikenan ba boka ba magani ta fitar da Zaytoonah.

Tun Zaytoonah ba ta cika sati da barin gidan ba ta riga ta karaɗe ƙawayenta da cewa gida ya zama na ta ita ɗaya. Galadima ya saki Zaytoonah.

A lokacin sallar Azumi ne da ta samu Galadima ta roƙoshi a karo na ba adadi ya ce ya yafe amma dole ta nemi yafiyar Zaytoonah da Mommyn ta.
Ta tabbatar ma sa da lallai za ta kira su ta basu haƙuri.
Suna shirin komawa Abuja ta ma sa maganar ko za a buÉ—e É—akin Zaytoonah a kwashe ma ta sauran kayan a kai ma ta su gida amma amsar da ya ba ta sai ya sa ta cikin ruÉ—ani.

"A wani dalilin za a kwashe kayan?"

Da ƙyar ta iya cewa "naga wai tunda ba ta nan kuma..."

"Ki bar ma ta kayanta a inda su ke"

Ya faÉ—a sannan ya sa kai ya fita ya bar Ghazala da shiga duniyar tunanin wanne ne ba wanne ne ba...

Duk abinda ake ba dan Allah ba to baya taɓa ɗaurewa. Duk wani tattali, soyayya da kwantar da kai da Ghazala ke yiwa yaran Galadima tuni ya fara gushewa domin an tafi wata ɗaya ba ta ga alamar Zaytoonah za ta dawo ba aka cika wata biyu shima shiru kuma ko a waya ba ta taɓa kama Galadima na magana da ita ba sai kawai ta tabbatarwa kan ta kawai fa ya sake ta ne.

Abu na farko da yaran su ka fara fiskanta gameda ita shine rashin sake fiska da ta ke mu su kamar da. Abu kaÉ—an za su yi ta hau faÉ—a. Wani É—an shiga É—akin Galadima da su ke anyhow ta hana shi.

"Iya kacin ku falo Raziya. Ke Babba ce ya kamata ki gayawa ƙannen ki ba koyaushe ne za ku dinga shiga mana ɗaki ba musamman idan muna tare. Indai kunga baya falon sa kam ai kun san yana buƙatar kaɗaici a ɗaki ne. Amma bini-bini kun shiga ɗaki kuna neman sa zai ɓace a ɗakin ne ko me ne"

Raziya ta yi shiru tana kallon Ghazala cike da mamaki..
2/11/21, 10:04 PM - ****: 65

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Shehu*

"Welldone Fatima"
Malamin Maths ɗin su Raziya ya faɗa lokacin da ya miƙa ma ta script na test ɗin da su ka rubuta shekaranjiya.

Takardar da aka miƙa ma ta ta kalla cike da mamaki. Seat mate ɗinta Aysha ta kalli takardar ta ce "10/10, gaskiya kin yi wuta, ni fa 4/10 na ci"

Wannan ne karo na farko da ta samu sakamako mai kyau a test É—in Maths.

Bayan Malamin na su ya fita aka fara hiran test ɗin wanda a duka ajin na su ita kaɗai ce ta cinye, yaron da ya fi kowa ƙwazo a math a ajin 8/10 ya samu.

Tunda Zaytoonah ta fara koya ma ta Maths ta fara cin homeworks ɗin ta and classwork ma ba laifi marks ɗinta ya ƙaru and remarkably first test na su ta fi kowa ci a ajin.

A mafiya yawancin lokuta da Zaytoonah ke koya ma ta karatu haka za ta zaƙe da dinga ma ta iyashege, wasu lokutan sai su yi sati biyu suna kan topic ɗaya tayita cewa ita ba ta ganewa. Jikinta yai sanyi da ta tuna abinda ta yiwa Zaytoonah.
Chapter 132 · 0% Book details