Sashe 91
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Mommy ta shigo gidan da Yamma Zaytoonah na kitchen tana kwashe tuwon semo da ta yi. Tuntuni tayi miyar amma ta tsaya duba report da aka aiko ma ta ne daga chan gidan Gona shiyasa ba ta samu ta gama girkin daren da wuri ba.
Gidan yai wa Mommy shiru saboda ma su surutun gidan ba sa nan.
Sai da ta ajiye jaka ta chanja kaya zuwa wata jallabiyar TJ da ta maida shi kayanta na zaman gida sannan ta fito falo.
"Sannu da aiki" Mommy ta faÉ—a tana kallon Zaytoonah da ta fito daga kitchen.
"Idan babu yaran sai gidan yai shiru kamar ba mutane"
"Suna chan ai sun addabi Tsoho"
Mommy ta yi murmushi tana ƙara godewa Allah a ranta.
Film É—in da ake yi a Zee world dukkan su suka maida hankali akai. Da ke Uwa da 'yar duka suna hutun Sallah shiyasa ma babu wanda ya tashi cikin su lokacin da ake kiran sallar Maghrib.
"Na manta ma, gobe za ki je gidan Hajiya Ni'ima akwai aikin da ta ce za ki ma ta"
"Mommy fatan ba za ayi irin na waccar ƙawan kin nan ba, na gama yiwa 'yar ta jeren gida tana turo min dubu goma kamar wanda ta ga alamun tsiya a jiki na. Da ma kyauta ta ce na mata aikin daya fi"
"Ke kika san wannan, ni dai ance ki je dan haka wannan sauran zance tsakanin ku ne"
Hajiya Ni'ima aiki su ke tare da Mommy kuma office É—in su É—aya. Sosai su ke mutunci da Mommy duk da Mommyn ta girmeta sosai. ÆŠiya ce ga Mai Martaba Sarkin Zazzau amma ko kaÉ—an ba ta da girman kai, lokacin da Mommy ta yi rashin lafiya har gida ta zo ta gaishe ta...
Ƙarfe shaɗaya na safe ta ɗan shige da mintuna ta iso gidan Hajiya Ni'ima, sau ɗaya ta taɓa zuwa gidan tareda Mommy lokacin da ta haihu, shekaran da ta gaba ta kenan.
Za ta fito daga mota ta ji wayarta na ringing dan haka sai ta fasa fita. Ganin numban Alhaji Iliyasu ke kira ta san ko dai yaran ta ne ko kuma dai wani abu ya faru Alhajin ke neman ta. Tana É—auka kuwa ta ji muryan Hashir a wayan yana faÉ—in " Mom kinga wannan Baban me farin gemu irin na Baba Tsoho yana ce min Hashiru kuma suna na Hashir ne"
Ba yau ta saba jin irin ƙorafin nan ba dan haka ta ce ma sa "yi haƙuri ka ji Sweetie na, ai na sani sunan ka Hashir ne ba Hashiru ba, kar ka damu ka ji"
"Mom yau mun yi lamuzi tareda Baba Tsoho" Hadid ya karɓi wayan yana faɗa.
"Kai ba Lamuzi ba ne Lamizi ne" Hashir ya gyara ma sa.
"Mom ina na faÉ—a dai-dai?, Lamuzi ne ko?"
"Lazimi" ta gyara ma sa.
Hashir ya fara dariya yana faɗin ai shi ya faɗa dai-dai Lamizi. Tana ƙoƙarin nuna ma sa shima abinda ya faɗa ba dai-dai ba ne ta ji alamun an ajiye wayan ana faɗa. Ta kashe kiran tana dariya dan 'yan biyun na ta sai a hankali.
Da murmushi a fiskarta ta shiga gidan dan ta riga ta kira Hajiya Ni'imar a waya kuma ta ce ma ta ta shigo tana gida.
Mai aiki ce ta ma ta iso bayan ta zauna aka kawo mata lemo da ruwa. Kusan minti biyu da zuwanta sai ga Hajiya ni'imar ta fito.
"Ka ga Barrister 'yar Barrister"
Zaytoonah ta yi murmushi tana gaida ta.
Aiki ne ta ke son ba ta na wani gidan Yayan ta. Gidan an É—an kwana biyu ba a zama a ciki shine ta ke so a sake rearranging na gidan abubuwan da su ka tsufa kuma a chanja su.
"Kin san da Galadima yana aiki a Sokoto ne to yanzu ya koma Abuja, so zai dinga zuwa nan Zaria often haka. Sannan nan ba da jimawa ba zai yi aure"
"Wani irin gida ne?"
"Babban gida ne gaskiya, inaga zai fi ki fara zuwa ki ga gidan saboda ki san mi da mi ya kamata ayi ma sa. Za mu Iya zuwa yanzu idan ba ki da uzuri" Zaytoonah ta ce su je ba matsala.
Kasancewar karatu yana ɗaukewa Zaytoonah yawan tunani shiyasa a duk hutun da ta samu ta ke amfani da shi wajen samun certificate a wani fanni daban da wanda take karantawa. Kamar Yadda Farha ta dinga ba ta ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta samu certificate a ɓangare uku bayan degree da ta ke da shi a Law. Tana da certificate a Interior design, Spa and Beauty da kuma information technology.
Dawowanta Nigeria ta haɗa hannu da Kamfanin ɗan Alhaji Saleh wanda ƙani ya ke wajen Alhaji Iliyasu Mai Auduga. Alhaji Ibrahim Saleh yana shigo da kayan decoration na gida da office tun daga kan kujeru, gado 3D wall decoration, har painting irin na Artist ɗin nan suna kawowa. A duk lokacin da ake da aiki na decorating gida ya kan tuntuɓi Zaytoonah if she's less busy sai ta je ta supervising aikin. Ba wai dan kuɗi ta ke aikin ba dan ta fi ƙarfin kuɗin sa sai dai tana jin daɗin aikin shiyasa duk lokacin da ta ke free idan ya tuntuɓeta take zuwa da sauri. Cikin ƙawayen Mommy da su ka yi bikin 'ya'yan su akwai wanda su ka ba ta aikin jeren ɗakin 'ya'yan su. Aikin farko da ta fara yi ba ta samu matsala da wanda su ka je jeren ba infact sun yaba ma da hazaƙar ta wajen ganin komai ya shiryu cikin sauƙi kuma ya zo yayi kyau duk tsarin da ta bayar ya sa ɗakin yayi kyau sosai.
Wani aiki kuwa da ta je su Mama- Mama, Baaba-Baaba da ta samu a wajen kallon wacce ba ta san komai ba su ka ma ta. Wata a wajen har da cewa tun kafin a haifeta su ke zuwa jere. Zaytoonah ta tafi ta barsu suka yi aikin da kan su. Daga baya kusan sati uku da auren da Maman Amarya ta je gidan sai da ta kira Zaytoonah akan arrangement na ɗakin bai ma ta ba, itama kuma Amaryan ta yi complain akai. Da ke dai matar ta hannun daman Mommy ne sai ta amince ta je gidan. Da ita da Amaryar da ƙannenta biyu ɗaya namiji ɗaya mace su ka sake gyara ɗakin, hatta falon sai da su ka chanja tsarin zaman kujerun...
Yanayin gidan da su ka je ya burge Zaytoonah ta shiga ko'ina a gidan ta gani ban da É—aki É—aya wanda ta ke tunanin na mai gidan ne.
"Kin ga shi baya son tarkace a gida, sannan ya fi son abu fari ko kuma baƙi. Red, Yellow, Pink da Purple duk kala ne da bai faye so ba dan yana danganta kalar da mata. So sashen sa kar a saka ma sa abu mai kala irin haka"
Hajiya Ni'ima kenan ke yiwa Zaytoonah wannan ƙarin bayani.
Kafin su bar gidan sai da ta tambayeta nawa kuɗin aiki amma sai ta ce ta bari a ƙare aikin tukunna.
Gidan baya buƙatan sabbin abubuwa da an kaɗe an goge yawancin kayan za su dawo da kyaun su dan yawancin kayan gidan ma sabbi ne. Labulayen gidan kam mai gidan ya ce kaf ɗin su a chanja inji Hajiya Ni'ima duk da suma ba wai sun wani tsufa ba ne.
Kusan kwanan su biyar suna sintirin zuwa gidan Galadima ana kan furnishing É—in sa.
Da yammacin ranan jumma'a su ka kammala komai, kuma a ranan maigidan zai dawo dan ya assessing aikin su ko akwai abinda ya ke so su ƙara ko a cire.
A hannun kujera Zaytoonah ta zauna tana cin abinci, tun daga gida ta riƙo abunta dan ta san yau ma za su iya kaiwa yammaci a gidan.
"Allah Yaya sun yi aiki mai kyau, ni kaina sai na ji gidan ya kuma shiga raina"
Bai amsa ma ta ba sai ya buɗe ƙofar falon ya shiga gidan da sallama. Ta gaji da riƙe waya ya sa ta bar wayar a wuyanta ta matse shi da kafaɗarta dan kar ya faɗo. Ta cigaba da cin abincinta tana jin complain ɗin 'yan biyu wanda ko alamun ƙarewa bai yi ba. Labarin makaranta su ke ba ta wanda daga nan kuma aka shiga labarin da ya faru kusan sati ɗaya daya wuce a Islamiyya.
Sa kai yai niyyar yi dan ya haura sama ya fara duba sashen sa kafin ya duba sauran ɓangarorin, sai dai yarinyar da ya gani tana waya ne ta ɗauke ma sa hankali. Tabbas ya san fiskar nan amma ya rasa a ina ne. Ya jima yana kallon ta yana ƙoƙarin tuno a ina ya san fiskar amma bai tuna ba dan haka ya sa kai yai gaba sai kuma ya juyo da sauri ya kalleta a karo na biyu a ƙasan ran sa yana furta *Student ce*
Ikon Allah kenan ashe da rabon zai sake ganin yarinyar nan mai chin Plantain chips a cikin jirgi. Tabbas ita ce, sai dai wannan ba 'yar yarinyar daya gani shekarun baya ba ne wacce baya tsammanin a lokacin ta wuce shekara shashida ko shabakwai.
Kenan Home decoration ta karanta ya riya a ran sa ko kuma Interior design. Bayan ya haura sama ne Hajiya Ni'ima da ta bi Yayan na ta kallo ta maida duban ta ga Zaytoonah da ke cin abinci da ba ta ma san sun shigo ba.
Murmushi ta yi a ƙasan ran ta mai tarin ma'anoni dayawa.
A ɓangaren Galadima kuwa yana shiga falon sa wayar sa ta fara ringing. Ya cirota a Aljihu ya ambaci Sallama da sassanyar muryar sa.
Sai da ta yi murmushi wanda na jin daÉ—in sauraron ma'abocin sallamar ne kafin ta ce " Abu Razz Barka da yammaci, fatan ka isa gida lafiya"
"Alhamdulillah" ya faɗa a taƙaice.
"Ranka shi daÉ—e na ce ko za ka yarda su Raziya su zo su yi weekend a wajena?"
"Allah ya taimaka" ta amsa ma sa da Amin, kafin ta kuma wani maganar ya kashe wayan.