Sashe 87
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari 'yan biyu su ka tsitsiye wai dole sai sun bi Mommy zuwa Abuja. Yadda su ka takure su ka yi kalar tausayi ya sa ta amince ta tafi da su akan za su yi kwana É—aya sai su dawo tunda akwai school...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 44
Bismillahir Rahmanir Rahim
*panic attack*
Kusan awa É—aya da rabi sai ga kiran Ahmad ya shigo wayar lokacin suna ma cin abinci a dining.
Bayan ta amsa ne ta ce ma sa tana zuwa.
Yunƙurin tashi ta yi Muhsina ta ce ta tsaya ta ƙarisa cin abincin tunda ta kusa gamawa. Reluctantly dai sai ta zauna ta ƙarisa abincin, da ta gama ta shiga ɗaki ta saka hijab ta fito.
Tana shiga motar Ahmad ya sa dariya.
"Ikon Allah, Ashe wayar Uncle Justice kika É—auka. Wai ya abin ya faru ne?"
"Dole ka yi dariya ai, Mugu"
Sai da ya sake dariya kafin ya miƙo mata wayar ta yana faɗin " ga wayar ki inji Uncle"
Ta harare shi kafin ta amshi wayar wanda ɗan awa uku zuwa huɗu da yai a wajen Justice har ya ɗauki irin ƙanshin turaren sa.
Ta miƙa ma sa wayar Justice tana bashi labarin ƙatoɓarar da ta yi ɗazu.
"Wai ni kam waye ce Hajia Ghazalan nan ne?"
Hajia Ghazala, Ahmad ya maimaita sunan kafin ya ce " Okey! Ƙanwar matar Uncle ce"
"Ko da ita za mu sha biki ne" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya.
"To waya sani ne, kin san Justice É—in ne sai a hankali ba a iya gane mishi"
Sun ɗan taɓa hira kafin ya tafi. Bayan ta shiga gida ne ta duba call log ɗin ta inda ta ga kiran Mommy da na Auwal kuma duka biyu an amsa kiran. Ko mi ya ce mu su oho ta faɗa a zuciyar ta.
Mommy ta fara kira, gaisawa ce dama za su yi ɗazu da kuma 'yan biyu da su ke son gaisawa da Mom ɗin su, a lokacin kuma Justice ya ɗauka ya ce ba ta kusa idan ta dawo za ta kira. Sai da ta yi murmushi kafin ta sanar da Mommy yadda abin ya faru har da irin katoɓarar da ta yi.
'Yan biyu sun bi Salman zuwa masallaci dan haka ta ce za ta kira anjima. Da ta kira Auwal bai É—aga ba sai tayi tunanin ko yana sallah ne shima dan haka itama ta ajiye wayar ta shiga banÉ—aki.
Sai kusan ƙarfe tara na dare sai ga kiran Auwal, lokacin ma karatun wani littafi ta ke yi.
"Ba dai kin yi bacci ba?"
"A'a karatu na ke ma"
A bazata ta ji ya ma ta wani tambaya wanda ta rasa dangantakar tambayar da ita.
"Ashe Justice bai da mata?"
Sai da tayi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "Eh haka na ji nima"
Shima ɗin ya ɗan yi shiru dan wani kishi da ke cin sa tun lokacin da yai waya da Justice. Shi duk bai ma san wani Justice ba ne sai bayan da su ka yi wayan ne daga baya a fakaice da ya je wajen Mommy ya ke tambayarta. Tunda ya ji Justice shine Galadiman Zazzau hankalin sa ya ƙara tashi. Bai yiwa Justice mummunan zargi ba saboda a iya labarin da ya sani gameda Galadima shi mutum ne na gari, mutum ne da kowa ke ma sa shaidar alkhairi. Sai dai aiki da Zaytoonah ke yi a ƙarƙashin sa da kuma amsa wayar ta da yai ɗazu shi ya ƙwaƙwalwar sa ke riya ma sa wani abu nan take kuma zazzafan kishi ya mamaye ilahirin jikin sa. Yana son Zaytoonah tun da daɗewa, yanzu da wani dama ya sake zuwa ma sa ba zai taɓa bari damar nan ta kubce ma sa ba. Ya yi shiru ne da maganar zuwa a gama case ɗin Mommy amma kuma yanzu yana ganin gara ya bayyana sirrin zuciyar sa tun kafin ya ƙara rasata a karo na biyu.
"Da alama dai ba kya kusa ne Justice ya amsa wayar ki É—azu da yamma"
Tunowa da abinda ya faru da ta yi ya sa ta yi dariya, sai dai dariyan da ta yi ya kara rikitar da Auwal tareda É—aure ma sa kai.
Sai da ta bashi labarin abinda ya faru ya É—an ji sanyi kaÉ—an a ran sa amma duk da haka zuciyar sa ba ta dena zargin wani abu ba....
***
A lokacin da Hajia Ghazala ta dinga kiran numban Justice ba a ɗauka ba hauka ne kawai ba ta yi ba saboda yadda ƙwaƙwalwarta ke ayyano ma ta abubuwa mabanbanta lokaci guda. Tayi tunanin ko sace wayar sa aka yi, ko kuma wayar ce ta faɗi aka ɗauke, ko kuma dai yana tareda wata ce ta ɗau wayar.
A lokacin mantawa ta yi da cewa tanada ɗaya numbar Justice ɗin wanda layin a ƙaramar waya ya saka ta. Boutique ɗin ta za ta je amma fasawa ta yi ta karya kwana ta wuce gidan Justice zuciyarta cike da tararradin abubuwa.
Ganin yaran sa ya sa ta É—an saita nitsuwar ta tareda nunawa kaman dan su É—in ta je gidan. Sai da su ka zazzauna kafin ta tambayesu ko Baban su bai dawo ba kuma tana kiran numbar sa baya shiga. Raziya ta ce ta gwada É—aya layin sa ta gani, sai a sannan ta ankara da cewa ashe layikan na sa biyu ne.
Ta É—auko waya ta kira É—aya numbar, kuma bugu É—aya aka É—auka. Jin sallamar Justice ne ya sa kaso tamanin na damuwar ta ya tafi.
"Ranka shi daÉ—e É—aya numbar ka kamar ba ta shiga, hala ka manta a office ne" ta yi maganar bayan sun gaisa.
"Ba ta hanuna" abinda ya faÉ—a kenan wanda hakan ya É—aure ma ta kai.
Ta sani ba zai ma ta dogon bayani ba shiyasa ta tsayar da maganan a haka amma zuciyar ta yana cike da tarin tambayoyi.
Tana gidan har Auwal ya kawo wayan Justice, dan sun rabu da Justice bayan ya bashi wayar Zaytoonah akan zai je Asibiti duba wani marar lafiya.
Ahmad yai wa Hajia Ghazala bayanin yadda aka yi suka yi exchange É—in waya tareda Zaytoonah.
*Zaytoonah* ta maimaita sunan cike da ayar tambaya na son sanin mai wannan suna.
Washegari da Zaytoonah ta je office ƙoƙarin dodging ɗin Justice ta yi wanda tunda ya zo ko minti talatin bai yi ba ya wuce court saboda suna da zama, hakan ya bawa Zaytoonah daman watayawa yadda take so.
Bayan kwana uku ranan Alhamis sai ga Hajia Ghazala a office É—in Justice. Bayan ta samu ganawa da Justice ne ta ma sa maganar Anwar da ke neman 'yar ta Husna.
"Na ce ko zan turo shi wajen ka dan ka assessing na shi, ka san samarin yanzu sai a hankali"
A iya sanin sa dai mahaifin Husna Alhaji Bashir na raye haka nan 'yan uwan sa na nan.
" ki yi haƙuri, amma ban da lokaci gaskiya. Ina ga dai su Alhaji Bashir za su yi binciken daya dace akan sa. Ke dai ki yi istikhara ki kuma sa ta a addu'o'in ki, ina ga Insha Allahu komai zai zo da sauƙi"
Godiya ta ma sa kafin ta fita daga office É—in da niyyar za ta gaisa da Ahmad. Dama musabbabin zuwan ta ba wai dan maganar saurayin Husna ba ne ta zo ne dan ta ga Zaytoonah.
Office ɗin su Ahmad da aka nuna ma ta nan ta shiga tana wani shan ƙamshi.
Su biyu ne a office É—in Ahmad da wani. Bayan ta gaisa da su ne take tambayar sa ina mutumiyar sa ne.
"Yanzu ta fita kuwa ta je office É—in Barr. Noah, barin kira miki ita" ya fita daga office É—in da zumuÉ—i.
Minti biyu da fitar sa sai ga shi ya shigo, kallon yarinyar da ta biyo bayan sa ta ke yi, kallo irin na ƙurilla.
Yarinyar ba wata Babba bace dan ba ta tunanin za ta kai 25yrs ma. Girman jiki kawai gareta. Duk da kasancewar ta mai ƙiba hakan bai ɓoye kyaun ta ba, tsayin da ta ke da shi ya ɗan ɓoye ƙiban na ta, baƙa ce amma irin baƙin da kallo ɗaya za ka kira su da Black Beauty.
"Ina wuni Hajia" Zaytoonah ta katse ma ta tunanin ta.
"Lafiya" Hajia Ghazala ta amsa tana sake fuska.
Ba wata doguwar magana su ka yi ba Hajiar ta tafi. Sai da ta tafi ne Zaytoonah ke cewa Ahmad gaskiya Hajia Ghazala ba ƙaramin dacewa ta yi da Justice ba, har da cewa Hajia Ghazala ta ma ta kyau. Shima dai Ahmad ɗin hakan ya gani sai dai ƙila kasancewar ta ƙanwar matar Justice ya sa ba ya ma ta wannan kallon.
Ranan Jummu'ah ta haɗa report ɗin ta kenan sai ga kiran Mommy. A yadda ta ji muryan Mommy sai ta yi tunanin kamar ba lafiya ba. Tambayarta ta yi ko za ta zo weekend ta ce ma ta za ta zo. Allah ya kawoki lafiya ta furta sannan ta kashe wayar ko sallama babu hakan ya sa ta ji zuciyar ta ya yi rauni. 'Something is wrong' ta furta a fili. Kai tsaye sai ta kira wayan Salman amma ba a ɗauka ba. Ta tura ma sa saƙo akan ya kirata.
Bayan ta yi sallar Isha ne ta buÉ—e whatsapp É—in ta dan tun safe ba ta hau ba. Wajen status da ta duba ne ta ga Salman da Auwal duk sun É—aura hoto iri É—aya kuma kamar hoton Goggo ne. Tana buÉ—e hoton sai ta ga abinda aka rubuta a jikin hoton Goggon wanda ya girgiza ta. Lokaci guda hawaye su ka fara kwaranya a idon ta.
"Goggo ta rasu" ta furta tana tuno kyawawan halayen wannan tsohuwa.
Numbar Mommy ta kira ba a É—aga ba sai a kira na biyu wanda Hashir ya É—auka yana faÉ—a ma ta GrandMa na waje tareda Uncle Auwal, yaran ne su ka ma ta gulmar wai yanzu su Mommyn ke shirin tafiya Ringim, harda cewa É—azu GrandMa ta dinga kuka.
Tabbas dai Goggo ta bar duniya. Salihar Mata wacce har yau ita Zaytoonah ke gani a matsayin Kaka...