Sashe 158
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Pillow guda biyu Suhailah ta jerawa Zaytoonah a ƙasa kafin ta zauna akan kujera ta ɗaura ƙafafun ta a kai. Wani irin kumburi ƙafafun su ka yi ma ta, dama tun cikin na wata shida ta fara cika ta ko'ina to da ya shiga wata takwas kuwa sai kumburin ƙafa da ciwon baya amma ciwon bayan ba sosai ba. Yanzu kam wahala sosai ta ke yi da cikin. Har lokacin ba ta faɗawa kowa cewa 'yan biyu ba ne, ko last time da ta je gidan Mommy sai da ta tambayeta ko 'yan biyu za ta haifa da wannan ƙaton cikin Zaytoonah ta ce Allah ne masani, ba ta son dubawa ta fi so a ranan da ta haihu kowa ya ga kyautar da Allah ya ba ta.
"Yawwa na ga Assignment É—in" Zaytoonah ta faÉ—a a wahalce.
Ta karɓi littafin Suhailah ta fara dubawa. Tana cikin koya ma ta aikin wayarta ya shiga ringing.
Galadima ne ke kira. Sai da ta yi murmushi kafin ta É—auka.
"Mijin Zayt"
"Na'am Matar Yunus"
"Ya aka yi"
"Yanzu na isa masauki na shine na ce barin kira matar ta yiwa mijin hira"
"Ya hanya"
"Alhamdulillah sai kewan ku da na ke ta yi. Barin ga fiskar matar dan Allah"
"balloon face É—in za ka gani"
"Ko pumpkin face ne ai nawa ne ko"
"To bari na gama koyawa Suhailah karatu"
"Ban yarda ba. Ko rabin minti ne ki bari na ga fiskar princess É—ina"
"Sayyadi please" ta faÉ—a a marairaice
"Ok ok, nan da 10 minutes zan sake kira"
Kaman haÉ—in baki tana ajiye wayar sai ga kiran Farha ya shigo. Bayan sun gaisa ne Farhan ta ma ta albishir akan za ta auri Manager É—in gidan gonan ta wato Muhammad Chu.
"Kin san dai ba iya zuwa zan yi ba yadda na yi nauyin nan"
"Haba Besty. To zan fasa auren har sai kin haihu"
"Kamar da gaske"
Farha ta sa dariya. Sun kai minti uku suna waya kafin ta kashe bayan ta ma ta fatan Allah ya ba su zaman lafiya...
Kwanan Galadima uku a Lagos ya dawo inda ya attending wani conference.
Kaman yadda kullum ya ke ɗaukan Zaytoonah duk dare su ke fita strolling saboda ƙafarta yau ma ɗin dogon hijabi ta zunbula sannan ta saka nose mask saboda sanyi, ta fito falo inda Galadima ke jiran ta.
Yana zaune tareda yaran ɗauke da Alinah suna kallo . Lokacin da ya miƙa Alinah wajen Raziya kuka ta challa kamar wadda ta ga dodo.
"Ai sai ki yi ai. Ba wanda zai fita dake a wannan sanyin" Zaytoonah ta faÉ—a tana wucewa gaba dan ba ta ma son Galadima ya ce su tafi da ita.
Haka su ka fice daga gidan su ka bar Raziya na faman lallashin ta.
A hankali su ke tafiya suna yi suna taÉ—i.
"Sayyadi idan na sauke gaskiya zan huta, is not easy gaskiya"
"Allah ya sauke ki lafiya" ya faÉ—a ahankali. Ba wai ya ji daÉ—in maganar ba ne amma kuma lafiyar Zaytoonah tafi ma sa komai. ÆŠaukan ciki da haihuwa ba wasa ba ne gashi ko hutawan kirki ba ta yi ba da haihuwar Alinah ta sake samun wani cikin...
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zaytoonah ta cigaba da renon cikin ta. Ranan da ya cika wata tara da kwana goma shauku ta fara naƙuda, da ke lokacin ya zo ƙarshen shekara dukkan su na Zaria lokacin.
Baba Nafy ne ta kira ma ta Mommy lokacin da su ka isa Asibiti. Zuwa minti ishirin kuwa Mommy ta iso. Ita dai haihuwan ta na faɗawa lokacin dare dan kuwa tun kusan ƙarfe shaɗaya na safe da su ka zo ba ta samu ta haihu ba sai ƙarfe ɗayan dare. Yadda Mommy ke tare da ita tun safe haka shima Galadima ya ka sa komawa gida lokacin da ya dawo ƙarfe tara ya samu har lokacin ba ta haihu ba.
Mommy ce ta fito daga labour room zuwa É—akin da aka kamawa Zaytoonan inda Galadima ke zaune yana jiran tsammani.
"Hajia ta sauka?"
"Alhamdulillah, ta sauka"
"Tana lafiya ko?"
"E da ita da jariran ta suna lafiya"
Galadima ya fara rarraba ido jin Mommy ta ambaci jarirai
" 'yan biyu maza ta haifa" Mommy ta ma sa gwari-gwari.
Alhamdulillah Galadima ya faÉ—a tareda yin sujudush shukri a wajen yana yiwa Allah godiya.
Ba'a jima ba kuwa aka kawo ma sa 'yan biyun sa bayan an gyara su, ya riƙe su a hannun sa idon sa fal da hawaye.
Zaytoonan ma a keke aka turota zuwa É—akin inda Mommy ta taimaka ma ta ta kwanta akan gado. Ko minti goma bai cika ba baccin wahala ya É—auketa.
Zuwa ƙarfe shida da rabi na safe Hajiya Abu ta dira a Asibitin, fiskarta wasai dan tunda Asuba da ta tashi ta ci karo da saƙon Galadima inda ya ke ma ta albishir da haihuwan 'yan biyu maza ta kasa zaune tsaye. Sai ma da idanun ta ya gane ma ta kyawawan yaran ta sake samun wani nitsuwa. Sai washe baki ta ke tana addu'ar Allah yai mu su albarka. Wannan mata yadda ta ke yi ko ita ta haifi Galadima albarka.
Daga gidan ta ma aka kawowa Zaytoonah abinci duk da Mommy ma ta tafi kawo abincin lokacin da su Salman su ka iso Asibitin.
Kafin ƙarfe goma an cika Asibitin da 'yan dubiya. Kowa ya ga yaran tambayar farko shine waye Hassan waye Hussain saboda identical twins ne. Wanda aka sawa blue riga shine Hassan mai green kuma Hussain abinda Hajia Abu ke faɗawa mutane kenan. Ta kasa ta tsare a ɗakin, saboda hayaniya ma dole aka ba su wani ɗakin aka bar Zaytoonah a ɗakin tana bacci.
Tun safe shiga da fice kawai ake yi zuwa kallon yara. Lokacin da Galadima ya nemi sallama Likita cewa yai a bari ta ƙara kwana saboda a tabbatar da lafiyarta.
Wasa-wasa sai da Zaytoonah ta yi kwana huɗu a Asibitin kafin aka sallameta zuwa lokacin jikinta ya ɗan yi ƙwari.
Bayan ta koma gida ne Galadima ya gaya ma ta ba za ayi taron suna ba har sai ta warke gaba É—aya.
Mommy ce ta nemi hakan saboda ta kula Zaytoonan har yanzu ba a hayyacinta ta ke ba. Kaman ma she's depressed ne.
Mommy ce ta zauna da ita a Asibitin da aka sallameta kuma sai ta ke jeka ka dawo, za ta je da safe ta koma gida da dare.
Hajiya Abu ba ta ji daÉ—in É—aga sunan ba amma ko ba komai zai ba su daman shiri da kyau.
Ana gobe za a raÉ—a suna bayan Mommy ta tafi gida Galadima ya shigo É—akin Zaytoonah. Tana zaune tana shan tea yayinda 'yan biyun ta ke kwance a gadon su mai kyau.
Dai da ya bi yaran sa ya tofa mu su addu'a sannan ya manna mu su kiss a goshi kafin ya ƙariso wajen ta.
"Ya ƙarfin jiki?"
"Alhamdulillah"
"Na mu su huÉ—uba da Hassan da Hussain, akwai inkiyar da ki ke so a sa mu su?"
Tun ranan haihuwan ta ji sunan yaran a bakin Mommy. Kuma shima da kan sa ya faÉ—a ma ta.
"Are you Ok? Ko mu koma Asibiti ne?"
Zaytoonah ta girgiza ma sa kai.
"Sannu kin ji. Allah ya mi ki albarka"
Ta amsa da amin a ranta. Sai da ta ƙarisa shan tea ɗin kafin ta kalleshi ta ce "Humairah tana son a kira su da Aahil da Aamir"
"Ke mi ki ke so?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Juyo da ita yai tana fiskantar sa sannan ya ce "Zaytoon miya ke damun ki? Mi ki ke so? Na lura kaman ba ki damu da yaran nan ba"
"Yadda 'yan uwan ka ke tarairayan yaran nan, idan da ace mata na haifa kana ga za su mu su haka?"
"Subhanallah!"
" shekaran jiya. Ina ji Hajia Abu tana faɗin yanzu kam ka samu magada. Ina jin yadda maroƙan da su ka zo daga Fada su ka dinga yiwa yaran nan kirari and i wonder idan da Mata na haifa za a mu su irin wannan, shin za su samu gata irin wannan"
"Zaytoon"
"Miyasa ba a É—auki 'ya'ya mata a bakin komai ba. Why is it always about having a son..."
Yatsun sa biyu ya sa ya rufe ma ta baki.
"Ba na son sake jin maganar nan a bakin ki, kai makamancin wannan maganar ma ba na son jin ta"
Ya riƙo hannunta ɗaya ya ɗaura a dai-dai ƙirjin sa ya ce "ba ni da ikon sarrafa wannan zuciya a lokutan da ta kwaɗaita min samun ɗa namiji. Amma nan" ya kai ɗaya hannun sa dai-dai gefen kan sa.
"Ƙwaƙwalta tana tunatar da ni cewa na karɓi duk kyautan da Allah ya bani a matsayin abinda ya fi dacewa da ni wannan yasa a kullum na ke gode ma sa. Idan da 'yan biyu mata ki ka haifa i will still love them equal saboda ba kowa ne ma Allah ke bawa kyautan 'yan biyu ba. I'm blessed to have them. Kinga 'yar uwata Hajiya Zainab dama kowanene da ya dangance ni ba ruwan ki da su ko abunda za su faɗa. Ruwan su ne su so abunda ki ka haifa ruwan su ne su ƙi su. Abu ɗaya na ke so ki sani, wanda ki ka haifawa yaran nan yana son kayan sa and any other person's opinion shouldn't matter to you. Kar ki sake ɗaga maganar nan dan raina na ɓaci idan kina yin ta"
Kwantar da kan ta tayi a ƙirjin sa tana fidda hawaye...
Washegari a Fada aka raÉ—a wa yara sunan Hassan (Amir) da Hussain (Ahil) duk da an É—aga taron suna zuwa wata sati hakan bai hana an É—an yi shagali ba.
Kafin sati ya zagayo Zaytoonah ta sake murmurewa, damuwa da ta sa a ran ta shima yanzu ta cire saboda yadda Galadima da Mommy ke ƙarfafa ma ta gwiwa.